< 耶利米書 17 >

1 猶大的罪是用鐵筆、用金鋼鑽記錄的,銘刻在他們的心版上和壇角上。
“An rubuta zunubin Yahuda da alƙalamin ƙarfe, an rubuta da tsinin dutse, a kan allunan zukatansu da kuma a kan ƙahonin bagadansu.
2 他們的兒女記念他們高岡上、青翠樹旁的壇和木偶。
Har’ya’yansu ma sun tuna bagadansu da ginshiƙan Asheransu kusa da itatuwa masu duhuwa da kuma a kan tuddai masu tsayi.
3 我田野的山哪,我必因你在四境之內所犯的罪,把你的貨物、財寶,並邱壇當掠物交給仇敵;
Dutsena a ƙasar da dukiyarku na ƙasar da dukan arzikinku za a ba da su ganima, tare da masujadanku na kan tuddai, saboda zunubi ko’ina a ƙasarku.
4 並且你因自己的罪必失去我所賜給你的產業。我也必使你在你所不認識的地上服事你的仇敵;因為你使我怒中起火,直燒到永遠。
Saboda laifinku za ku rasa gādon da na ba ku. Zan bautar da ku ga abokan gābanku a ƙasar da ba ku sani ba, domin kun husata ni, zai kuwa ci har abada.”
5 耶和華如此說: 倚靠人血肉的膀臂, 心中離棄耶和華的, 那人有禍了!
Ga abin da Ubangiji yana cewa, “La’ananne ne mutumin da yake dogara ga mutum, wanda ya dogara ga jiki don ƙarfi wanda kuma zuciyarsa ta juya wa Ubangiji baya.
6 因他必像沙漠的杜松, 不見福樂來到, 卻要住曠野乾旱之處, 無人居住的鹼地。
Zai zama kamar ɗan kurmi a ƙasar da take kango; ba za su ga arziki sa’ad da ya zo ba. Za su zauna a busassun wuraren hamada, a cikin ƙasar gishiri inda ba kowa.
7 倚靠耶和華、以耶和華為可靠的, 那人有福了!
“Amma mai albarka ne mutumin da yake dogara ga Ubangiji, wanda ƙarfin halinsa yana daga Ubangiji.
8 他必像樹栽於水旁, 在河邊扎根, 炎熱來到,並不懼怕, 葉子仍必青翠, 在乾旱之年毫無掛慮, 而且結果不止。
Za su zama kamar itacen da aka dasa kusa da ruwa wanda ya miƙa saiwoyinsa zuwa cikin rafi. Ba ya jin tsoro sa’ad da zafi ya zo; ganyayensa kullum kore suke. Ba shi da damuwa a shekarar fări ba ya taɓa fasa ba da’ya’ya.”
9 人心比萬物都詭詐, 壞到極處, 誰能識透呢?
Zuciya ta fi kome ruɗu ta fi ƙarfin warkewa. Wa zai iya gane ta?
10 我-耶和華是鑒察人心、試驗人肺腑的, 要照各人所行的和他做事的結果報應他。
“Ni Ubangiji nakan bincike zuciya in gwada tunani, don in sāka wa kowane mutum bisa ga halinsa, bisa ga ayyukansa.”
11 那不按正道得財的, 好像鷓鴣菢不是自己下的蛋; 到了中年,那財都必離開他, 他終久成為愚頑人。
Kamar makwarwar da ta kwanta a kan ƙwan da ba ita ta zuba ba haka yake da mutumin da ya sami arziki a hanyar da ba daidai ba. A tsakiyar rayuwarsa za su rabu da shi, a ƙarshe kuma zai zama wawa.
12 我們的聖所是榮耀的寶座, 從太初安置在高處。
Kursiyi mai daraja, da aka ɗaukaka tun daga farko, shi ne wuri mai tsarkinmu.
13 耶和華-以色列的盼望啊, 凡離棄你的必致蒙羞。 耶和華說:離開我的, 他們的名字必寫在土裏, 因為他們離棄我這活水的泉源。
Ya Ubangiji, sa zuciyar Isra’ila, duk waɗanda suka rabu da kai za su sha kunya. Waɗanda suka juya maka baya za a rubuta su a ƙura domin sun yashe Ubangiji, maɓulɓular ruwan rai.
14 耶和華啊,求你醫治我,我便痊癒, 拯救我,我便得救; 因你是我所讚美的。
Ka warkar da ni, ya Ubangiji, zan kuwa warke; ka cece ni zan kuwa cetu, gama kai ne nake yabo.
15 他們對我說:耶和華的話在哪裏呢? 叫這話應驗吧!
Sun riƙa ce mini, “Ina maganar Ubangiji take? Bari tă cika yanzu!”
16 至於我,那跟從你作牧人的職分, 我並沒有急忙離棄, 也沒有想那災殃的日子; 這是你知道的。 我口中所出的言語都在你面前。
Ban gudu zaman mai yin maka kiwo ba; ka sani ban marmarin ranan nan ta masifa ba. Abin da ya fito daga leɓunana kuwa, a bayyane suke gare ka.
17 不要使我因你驚恐; 當災禍的日子,你是我的避難所。
Kada ka zama mini abin razana; kai ne mafakata a ranar masifa.
18 願那些逼迫我的蒙羞, 卻不要使我蒙羞; 使他們驚惶, 卻不要使我驚惶; 使災禍的日子臨到他們, 以加倍的毀壞毀壞他們。
Bari masu tsananta mini su sha kunya, amma ka kiyaye ni daga shan kunya; bari su tsorata, amma ka kiyaye ni da razana. Ka kawo musu ranar masifa; ka hallaka su da hallaka riɓi biyu.
19 耶和華對我如此說:「你去站在平民的門口,就是猶大君王出入的門,又站在耶路撒冷的各門口,
Ga abin da Ubangiji ya ce mini, “Ka je ka tsaya a ƙofar mutane, inda sarakunan Yahuda sukan shiga su fita; ka tsaya kuma a dukan sauran ƙofofin Urushalima.
20 對他們說:『你們這猶大君王和猶大眾人,並耶路撒冷的一切居民,凡從這些門進入的都當聽耶和華的話。
Ka ce musu, ‘Ku ji maganar Ubangiji, ku sarakunan Yahuda, da dukan mutanen Yahuda da dukan mazaunan Urushalima waɗanda suke bi ta waɗannan ƙofofi.
21 耶和華如此說:你們要謹慎,不要在安息日擔甚麼擔子進入耶路撒冷的各門;
Ga abin da Ubangiji yana cewa, ku yi hankali kada ku ɗauki kaya a ranar Asabbaci ko ku shigar da shi ta ƙofofin Urushalima.
22 也不要在安息日從家中擔出擔子去。無論何工都不可做,只要以安息日為聖日,正如我所吩咐你們列祖的。』
Kada ku fitar da kayan gidajenku ko ku yi wani aiki a ranar Asabbaci mai tsarki, yadda na umarci kakanni-kakanninku.
23 他們卻不聽從,不側耳而聽,竟硬着頸項不聽,不受教訓。」
Duk da haka ba su saurara ba, ba su kuwa mai da hankali ba; suka taurare ba su kuwa saurara ko su karɓi horo ba.
24 耶和華說:「你們若留意聽從我,在安息日不擔甚麼擔子進入這城的各門,只以安息日為聖日,在那日無論何工都不做;
Amma in kuka yi hankali kuka yi mini biyayya, in ji Ubangiji, ba ku kuwa shigar da kaya ta ƙofofi a ranar Asabbaci ba, amma kuka kiyaye ranar Asabbaci da tsarki ba tare da yin wani aiki a cikinta ba,
25 那時就有坐大衛寶座的君王和首領,他們與猶大人,並耶路撒冷的居民,或坐車,或騎馬,進入這城的各門,而且這城必存到永遠。
sa’an nan sarakuna da suke zama a kursiyin Dawuda za su shiga ta ƙofofin wannan birni tare da fadawansu. Su da fadawansu za su shiga a kan kekunan yaƙi da kuma a kan dawakai, mutanen Yahuda suna musu rakiya tare da waɗanda suke zaune a Urushalima, wannan birni kuwa za tă kasance da mazauna har abada.
26 也必有人從猶大城邑和耶路撒冷四圍的各處,從便雅憫地、高原、山地,並南地而來,都帶燔祭、平安祭、素祭,和乳香,並感謝祭,到耶和華的殿去。
Mutane za su zo daga garuruwan Yahuda da ƙauyukan kewaye da Urushalima, daga iyakar Benyamin da gindin tuddan yamma, daga ƙasar tudu da kuma Negeb, suna kawo hadayun ƙonawa da hadayun gari, sadakokin turare da na godiya zuwa gidan Ubangiji.
27 你們若不聽從我,不以安息日為聖日,仍在安息日擔擔子,進入耶路撒冷的各門,我必在各門中點火;這火也必燒毀耶路撒冷的宮殿,不能熄滅。」
Amma in ba ku yi mini biyayya ba, ba ku kiyaye ranar Asabbaci da tsarki ba, kuka ɗauki wani kaya yayinda kuke shiga ƙofofin Urushalima a ranar Asabbaci, to, sai in cinna wa ƙofofin Urushalima wutar da ba a iya kashewa, tă cinye kagaranta.’”

< 耶利米書 17 >