< 以西結書 3 >
1 他對我說:「人子啊,要吃你所得的,要吃這書卷,好去對以色列家講說。」
Ya kuma ce mini, “Ɗan mutum, ka ci abin da yake a gabanka, ka ci wannan littafi; sa’an nan ka tafi ka yi magana wa gidan Isra’ila.”
Saboda haka na buɗe bakina, ya kuma ba ni littafin in ci.
3 又對我說:「人子啊,要吃我所賜給你的這書卷,充滿你的肚腹。」我就吃了,口中覺得其甜如蜜。
Sai ya ce mini, “Ɗan mutum, ka ci wannan littafin da nake ba ka, ka kuma cika cikinka da shi.” Sai na ci shi, ya kuma yi zaki kamar zuma a bakina.
4 他對我說:「人子啊,你往以色列家那裏去,將我的話對他們講說。
Sa’an nan ya ce mini, “Ɗan mutum, yanzu ka tafi gidan Isra’ila ka faɗa kalmomina gare su.
5 你奉差遣不是往那說話深奧、言語難懂的民那裏去,乃是往以色列家去;
Ba ina aikan ka wurin mutanen da suke da baƙon harshe da kuma yare mai wuya ba ne, amma zuwa ga gidan Isra’ila ne,
6 不是往那說話深奧、言語難懂的多國去,他們的話語是你不懂得的。我若差你往他們那裏去,他們必聽從你。
ba ga mutane da yawa na baƙon harshe da yare mai wuya, waɗanda ba ka san kalmominsu ba. Tabbatacce da na aike ka wurin irinsu, da sun saurare ka.
7 以色列家卻不肯聽從你,因為他們不肯聽從我;原來以色列全家是額堅心硬的人。
Amma gidan Isra’ila ba sa niyya su saurare ka domin ba sa niyya su saurare ni, gama dukan gidan Isra’ila sun taurare suna kuma kin ji.
8 看哪,我使你的臉硬過他們的臉,使你的額硬過他們的額。
Amma zan sa ka zama mai taurinkai da taurin zuciya kamar su.
9 我使你的額像金鋼鑽,比火石更硬。他們雖是悖逆之家,你不要怕他們,也不要因他們的臉色驚惶。」
Zan sa goshinka ya zama da tauri kamar dutse, da tauri fiye da dutsen ƙanƙara ƙarfi. Kada ka ji tsoronsu ko ka firgita ta wurinsu, ko da yake su gidan’yan tawaye ne.”
10 他又對我說:「人子啊,我對你所說的一切話,要心裏領會,耳中聽聞。
Ya kuma ce mini, “Ɗan mutum, ka ji da kyau ka kuma lura da dukan kalmomin da nake maka magana.
11 你往你本國被擄的子民那裏去,他們或聽,或不聽,你要對他們講說,告訴他們這是主耶和華說的。」
Ka tafi yanzu zuwa ga’yan’uwanka waɗanda suke zaman bauta ka yi musu magana. Ka ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa,’ ko ku ji, ko kada ku ji.”
12 那時,靈將我舉起,我就聽見在我身後有震動轟轟的聲音,說:「從耶和華的所在顯出來的榮耀是該稱頌的!」
Sa’an nan Ruhu ya ɗaga ni sama, a bayana na ji wata karar babban motsi na cewa, Bari a yabi ɗaukakar Ubangiji a wurin zamansa!
13 我又聽見那活物翅膀相碰,與活物旁邊輪子旋轉震動轟轟的響聲。
Karar fikafikan rayayyun halittun nan ne suke goge junansu da kuma karar da’irorin nan da suke kusa da su, ƙarar babban motsi.
14 於是靈將我舉起,帶我而去。我心中甚苦,靈性忿激,並且耶和華的靈在我身上大有能力。
Sa’an nan Ruhu ya ɗaga ni sama ya kuma tafi da ni, na kuwa tafi da ɓacin rai da kuma fushin ruhuna, tare da hannu mai ƙarfi na Ubangiji a bisa na.
15 我就來到提勒‧亞畢,住在迦巴魯河邊被擄的人那裏,到他們所住的地方,在他們中間憂憂悶悶地坐了七日。
Na zo wurin masu zaman bautan da suke zama a Tel Abib kusa da Kogin Kebar, A can kuwa, inda suke zama, na zauna a cikinsu kwana bakwai, ina mamaki.
A ƙarshen kwana bakwai ɗin maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
17 「人子啊,我立你作以色列家守望的人,所以你要聽我口中的話,替我警戒他們。
“Ɗan mutum, na mai da kai mai tsaro don gidan Isra’ila; saboda haka ka ji maganar da zan yi ka kuma yi musu kashedin nan da ya fito daga gare ni.
18 我何時指着惡人說:他必要死;你若不警戒他,也不勸戒他,使他離開惡行,拯救他的性命,這惡人必死在罪孽之中;我卻要向你討他喪命的罪。
In na ce wa mugu, ‘Lalle za ka mutu,’ ba ka kuwa yi masa kashedi ko ka tsawata masa a kan mugayen hanyoyinsa don yă ceci ransa ba, wannan mugun zai mutu saboda zunubinsa, zan kuwa nemi hakkin jininsa a hannunka.
19 倘若你警戒惡人,他仍不轉離罪惡,也不離開惡行,他必死在罪孽之中,你卻救自己脫離了罪。
Amma in ka yi wa mugun kashedi bai kuwa juya daga mugayen hanyoyinsa ba, zai mutu saboda zunubinsa; amma kai kam za ka kuɓuta.
20 再者,義人何時離義而犯罪,我將絆腳石放在他面前,他就必死;因你沒有警戒他,他必死在罪中,他素來所行的義不被記念;我卻要向你討他喪命的罪。
“Har yanzu, in mai adalci ya juya daga adalcinsa ya aikata mugunta, na kuma sa abin tuntuɓe a gabansa, zai mutu. Da yake ba ka yi masa kashedi ba, zai mutu saboda zunubinsa. Ba za a tuna da abin adalcin da ya yi ba, zan kuwa nemi hakkin jininsa a hannunka.
21 倘若你警戒義人,使他不犯罪,他就不犯罪;他因受警戒就必存活,你也救自己脫離了罪。」
Amma in ka yi wa mai adalcin kashedi kada yă yi zunubi bai kuwa yi zunubi ba, tabbatacce zai rayu saboda ya ji kashedin, kuma kai kam za ka kuɓuta.”
22 耶和華的靈在那裏降在我身上。他對我說:「你起來往平原去,我要在那裏和你說話。」
Hannun Ubangiji ya kasance a kaina a can, ya kuma ce mini, “Tashi ka fita zuwa fili, a can kuwa zan yi maka magana.”
23 於是我起來往平原去,不料,耶和華的榮耀正如我在迦巴魯河邊所見的一樣,停在那裏,我就俯伏於地。
Saboda haka na tashi da tafi fili. Ɗaukakar Ubangiji kuwa ta tsaya a can, kamar ɗaukakar da na gani kusa da Kogin Kebar, sai na fāɗi rubda ciki.
24 靈就進入我裏面,使我站起來。耶和華對我說:「你進房屋去,將門關上。
Sai Ruhu ya sauko a kaina ya kuma ɗaga ni na tsaya a ƙafafuna. Ya yi mini magana ya ce, “Ka fita, ka rufe kanka a cikin gida.
25 人子啊,人必用繩索捆綁你,你就不能出去在他們中間來往。
Kuma kai, ɗan mutum, za su ɗaura ka da igiyoyi; za a daure ka yadda ba za ka iya fita a cikin mutane ba.
26 我必使你的舌頭貼住上膛,以致你啞口,不能作責備他們的人;他們原是悖逆之家。
Zan sa harshenka ya manne wa dasashinka don ka yi shiru ka kuma kāsa tsawata musu, ko da yake su gidan’yan tawaye ne.
27 但我對你說話的時候,必使你開口,你就要對他們說:『主耶和華如此說。』聽的可以聽,不聽的任他不聽,因為他們是悖逆之家。」
Amma sa’ad da na yi maka magana, zan buɗe bakinka za ka kuwa faɗa musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya faɗa.’ Duk mai ji ya ji, kuma duk wanda ya ƙi ji, ya ƙi ji; gama su gida ne na’yan tawaye.