< 出埃及記 39 >
1 比撒列用藍色、紫色、朱紅色線做精緻的衣服,在聖所用以供職,又為亞倫做聖衣,是照耶和華所吩咐摩西的。
Daga zare mai ruwan shuɗi, da shuɗayya da kuma jan zare suka yi tsarkaken rigunan domin hidima a wuri mai tsarki. Suka kuma yi tsarkaken riguna don Haruna, yadda Ubangiji ya umarci Musa.
2 他用金線和藍色、紫色、朱紅色線,並撚的細麻做以弗得;
Suka yi efod na zinariya, da shuɗi, da shunayya, da jan zare, da kuma lallausan lilin.
3 把金子錘成薄片,剪出線來,與藍色、紫色、朱紅色線,用巧匠的手工一同繡上。
Suka bubbuga zinariya ta zama falle, suka yayyanka ta zare-zare don su yi saƙa da ita, tare da zane na shuɗi, da na shunayya, da na jan zare, da na lallausan lilin, aikin gwani mai fasaha.
4 又為以弗得做兩條相連的肩帶,接連在以弗得的兩頭。
Suka yi wa efod kafaɗu, sa’an nan suka haɗa su a gefenta biyu na sama, don a iya ɗaurawa.
5 其上巧工織的帶子和以弗得一樣的做法,用以束上,與以弗得接連一塊,是用金線和藍色、紫色、朱紅色線,並撚的細麻做的,是照耶和華所吩咐摩西的。
Gwanin mai saƙa ya saƙa abin ɗamarar efod. Da irin kayan da aka saƙa efod ne aka saƙa abin ɗamarar, wato, da zinariya, da shuɗi, da shunayya, da jan zare, da zaren lallausan lilin, yadda Ubangiji ya umarci Musa.
6 又琢出兩塊紅瑪瑙,鑲在金槽上,彷彿刻圖書,按着以色列兒子的名字雕刻;
Suka shimfiɗa duwatsun onis, suka jera su cikin tsaiko na zinariya, suka kuma zāna sunayen’ya’yan Isra’ila a kan duwatsun kamar yadda akan yi hatimi.
7 將這兩塊寶石安在以弗得的兩條肩帶上,為以色列人做紀念石,是照耶和華所吩咐摩西的。
Sa’an nan suka ɗaura su a ƙyallen kafaɗun efod a matsayin duwatsun tuni wa’ya’yan Isra’ila, yadda Ubangiji ya umarci Musa.
8 他用巧匠的手工做胸牌,和以弗得一樣的做法,用金線與藍色、紫色、朱紅色線,並撚的細麻做的。
Suka yi ƙyallen maƙalawa a ƙirji, aikin gwani. Suka yi shi kamar efod, na zinariya, da na shuɗi, da na shunayya, da na jan zare, da kuma na lallausan lilin.
9 胸牌是四方的,疊為兩層;這兩層長一虎口,寬一虎口,
Ƙyallen maƙalawa a ƙirjin murabba’i ne, aka ninka shi biyu, tsawonsa da fāɗinsa kamu ɗaya-ɗaya ne.
10 上面鑲着寶石四行:第一行是紅寶石、紅璧璽、紅玉;
Sa’an nan suka sa jeri huɗu na duwatsu masu daraja a bisansa. A jeri na farko akwai yakutu, da tofaz, da zumurrudu;
a jeri na biyu akwai turkuwoyis, da saffaya, da daimon;
a jeri na uku akwai yakinta, da idon mage, da ametis;
13 第四行是水蒼玉、紅瑪瑙、碧玉。這都鑲在金槽中。
a jeri na huɗu akwai beril, da onis, da yasfa. Aka sa su cikin tsaiko na zinariya.
14 這些寶石都是按着以色列十二個兒子的名字,彷彿刻圖書,刻十二個支派的名字。
Aka zāna duwatsu goma sha biyu, ɗaya don kowane sunan’ya’yan Isra’ila goma sha biyu, kamar yadda akan yi hatimi.
Sai suka yi tuƙaƙƙun sarƙoƙi na zinariya zalla a kan ƙyallen maƙalawa a ƙirji.
Suka yi tsaiko biyu na zinariya da zoban zinariya biyu, suka kuma ɗaura zoban a kusurwoyi biyu na ƙyallen maƙalawa a ƙirji.
Suka ɗaura sarƙoƙi biyu na zinariya da kusurwoyi na ƙyallen maƙalawa a ƙirji.
18 又把鍊子的那兩頭接在兩槽上,安在以弗得前面肩帶上。
Suka maƙala waɗancan bakin sarƙoƙin zinariya a tsaikon nan biyu, sa’an nan suka rataya su a kafaɗun efod daga gaba.
19 做兩個金環,安在胸牌的兩頭,在以弗得裏面的邊上,
Suka yi zobai biyu na zinariya suka haɗa, suka sa su a gefe biyu na ƙyallen maƙalawa a ƙirji daga ciki kusa da efod.
20 又做兩個金環,安在以弗得前面兩條肩帶的下邊,挨近相接之處,在以弗得巧工織的帶子以上。
Sa’an nan suka yi waɗansu ƙarin zobai biyu na zinariya, suka maƙale su daga ƙasa a gaban kafaɗu biyu na efod kusa da mahaɗin a bisa abin ɗamarar efod.
21 用一條藍細帶子把胸牌的環子和以弗得的環子繫住,使胸牌貼在以弗得巧工織的帶子上,不可與以弗得離縫,是照耶和華所吩咐摩西的。
Suka ɗaura zoban ƙyallen maƙalawa a ƙirjin a zoban efod da shuɗiyar igiya don ƙyallen maƙalawa a ƙirji, ya kwanta lif a bisa kan abin ɗamarar efod don kada yă kunce daga efod, sun yi yadda Ubangiji ya umarci Musa.
Suka kuma saƙa taguwa ta efod da shuɗi duka, aikin gwani mai saƙa,
23 袍上留一領口,口的周圍織出領邊來,彷彿鎧甲的領口,免得破裂。
an yi wa taguwar wuyan wundi a tsakiya kamar sulke, aka daje wuyan don kada yă kece.
24 在袍子底邊上,用藍色、紫色、朱紅色線,並撚的細麻做石榴,
Suka yi fasalin’ya’yan rumman da shuɗi, da shunayya, da jan zare, da lallausan lilin kewaye da gefe-gefen taguwar.
25 又用精金做鈴鐺,把鈴鐺釘在袍子周圍底邊上的石榴中間:
Suka yi ƙararrawa da zinariya zalla, suka sa su a tsakanin fasalin’ya’yan rumman kewaye da gefe-gefen taguwa.
26 一個鈴鐺一個石榴,一個鈴鐺一個石榴,在袍子周圍底邊上用以供職,是照耶和華所吩咐摩西的。
Aka jera ƙararrawan da’ya’yan rumman bi da bi. Haka aka jera su kewaye da gefe-gefen taguwar aiki, yadda Ubangiji ya umarci Musa.
Suka saƙa doguwar riga da lallausan lilin don Haruna da’ya’yansa, aikin gwani mai saƙa,
28 並用細麻布做冠冕和華美的裹頭巾,用撚的細麻布做褲子,
suka yi rawanin da lallausan lilin, da hulan lilin da rigunan ciki na lallausan lilin.
29 又用藍色、紫色、朱紅色線,並撚的細麻,以繡花的手工做腰帶,是照耶和華所吩咐摩西的。
Suka yi abin ɗamara da lallausan lilin da shuɗi, shunayya da jan zare, aikin gwanin mai ɗinki, yadda Ubangiji ya umarci Musa.
30 他用精金做聖冠上的牌,在上面按刻圖書之法,刻着「歸耶和華為聖」。
Suka yi allo tsattsarka da zinariya tsantsa, suka zāna rubutu irin na hatimi a kansa haka, Mai tsarki ga Ubangiji.
31 又用一條藍細帶子將牌繫在冠冕上,是照耶和華所吩咐摩西的。
Sa’an nan suka ɗaura shi da shuɗiyar igiya a gaban rawanin, yadda Ubangiji ya umarci Musa.
32 帳幕,就是會幕,一切的工就這樣做完了。凡耶和華所吩咐摩西的,以色列人都照樣做了。
Ta haka aka gama dukan aikin tabanakul da Tentin Sujada. Isra’ilawa suka yi kome yadda Ubangiji ya umarci Musa.
33 他們送到摩西那裏。帳幕和帳幕的一切器具,就是鉤子、板、閂、柱子、帶卯的座,
Sa’an nan suka kawo wa Musa tabanakul, tentin da dukan kayayyakinsa, ƙugiyoyinsa, katakansa, da sandunansa, da dogayen sandunansa da rammukansa;
34 染紅公羊皮的蓋、海狗皮的頂蓋,和遮掩櫃的幔子,
murfi na fatun rago wanda aka rina ja, da murfi na fatun shanun teku; da kuma laɓulen
akwatin Alkawari da sandunansa da murfin kafara;
tebur da dukan kayayyakinsa, da burodin Kasancewa;
37 精金的燈臺和擺列的燈盞,與燈臺的一切器具,並點燈的油,
wurin ajiye fitilu na zinariya zalla, da jerin fitilunsa da dukan kayayyakinsa, da man fitila,
bagade na zinariya, da man shafewa, da turare mai ƙanshi, da labulen ƙofar shiga tenti,
39 銅壇和壇上的銅網,壇的槓並壇的一切器具,洗濯盆和盆座,
bagade na tagulla na raga, da sandunansa da kayan aikinsa; da daro da wurin ajiyarsa,
40 院子的帷子和柱子,並帶卯的座,院子的門簾、繩子、橛子,並帳幕和會幕中一切使用的器具,
labulen filin, sandunansa da rammukansa, labulen ƙofar shiga filin; igiyoyi da ƙarafan kafa filin; dukan kayan aikin tabanakul da Tentin Sujada;
41 精工做的禮服,和祭司亞倫並他兒子在聖所用以供祭司職分的聖衣。
da kuma saƙaƙƙun rigunan da ake sawa don hidima a wuri mai tsarki, duk da tsarkakan riguna na Haruna firist da rigunan’ya’yansa maza, sa’ad da suke hidima a matsayin firistoci.
42 這一切工作都是以色列人照耶和華所吩咐摩西做的。
Isra’ilawa suka yi dukan aikin nan yadda Ubangiji ya umarci Musa.
43 耶和華怎樣吩咐的,他們就怎樣做了。摩西看見一切的工都做成了,就給他們祝福。
Musa ya duba aikin, sai ya ga cewa sun yi shi daidai yadda Ubangiji ya umarta. Sai Musa ya sa musu albarka.