< 撒母耳記下 6 >

1 大衛又聚集以色列中所有挑選的人三萬。
Dawuda ya sāke tattara zaɓaɓɓun mutanen Isra’ila, dubu talatin.
2 大衛起身,率領跟隨他的眾人前往,要從巴拉‧猶大將上帝的約櫃運來;這約櫃就是坐在二基路伯上萬軍之耶和華留名的約櫃。
Shi, da dukan mutanensa suka tashi daga Ba’ala-Yahuda don su hauro da akwatin alkawarin Allah, wanda ake kira da SunanUbangiji Maɗaukaki, wanda yake zama a tsakanin kerubobin da suke a kan akwatin alkawarin.
3 他們將上帝的約櫃從岡上亞比拿達的家裏抬出來,放在新車上;亞比拿達的兩個兒子烏撒和亞希約趕這新車。
Suka ɗauko akwatin alkawarin Allah a sabuwar keken yaƙi, suka kawo shi daga gidan Abinadab, wanda yake bisa tudu. Uzza da Ahiyo,’ya’yan Abinadab maza, suka bi da keken yaƙin da akwatin alkawarin Allah yake ciki suka bi da keken yaƙin
4 他們將上帝的約櫃從岡上亞比拿達家裏抬出來的時候,亞希約在櫃前行走。
da akwatin alkawarin Allah yake ciki. Ahiyo kuwa yana tafiya a gaban Abinadab.
5 大衛和以色列的全家在耶和華面前,用松木製造的各樣樂器和琴、瑟、鼓、鈸、鑼,作樂跳舞。
Dawuda da dukan gidan Isra’ila suka yi biki sosai da dukan ƙarfinsu a gaban Ubangiji, da waƙoƙi, da molaye, da garayu, da ganguna, da kacau-kacau da kuma kuge.
6 到了拿艮的禾場,因為牛失前蹄,烏撒就伸手扶住上帝的約櫃。
Da suka kai masussukar Nakon, sai Uzza ya miƙa hannu don yă riƙe akwatin alkawarin Allah, gama shanun sun yi tuntuɓe.
7 上帝耶和華向烏撒發怒,因這錯誤擊殺他,他就死在上帝的約櫃旁。
Fushin Ubangiji kuwa ya ƙuna a kan Uzza domin aikin rashin bangirma, saboda haka Allah ya buge shi ya kuma mutu a can kusa da akwatin alkawarin Allah.
8 大衛因耶和華擊殺 烏撒,心裏愁煩,就稱那地方為毗列斯‧烏撒,直到今日。
Ran Dawuda ya ɓace gama fushin Ubangiji ya ɓarke a kan Uzza. Shi ya sa har wa yau ana kira wurin Ferez Uzza.
9 那日,大衛懼怕耶和華,說:「耶和華的約櫃怎可運到我這裏來?」
Dawuda ya ji tsoron Ubangiji a ranar, sai ya ce, “Yaya akwatin alkawarin Ubangiji zai iya zuwa wurina?”
10 於是大衛不肯將耶和華的約櫃運進大衛的城,卻運到迦特人俄別‧以東的家中。
Bai so yă ɗauki akwatin alkawarin Ubangiji yă kasance tare da shi a Birnin Dawuda ba. A maimakon haka sai ya kai shi gidan Obed-Edom mutumin Gat.
11 耶和華的約櫃在迦特人俄別‧以東家中三個月;耶和華賜福給俄別‧以東和他的全家。
Akwatin Alkawarin Ubangiji ya kasance a gidan Obed-Edom mutumin Gat har tsawon wata uku, Ubangiji kuwa ya albarkace shi da dukan iyalinsa.
12 有人告訴大衛王說:「耶和華因為約櫃賜福給俄別‧以東的家和一切屬他的。」大衛就去,歡歡喜喜地將上帝的約櫃從俄別‧以東家中抬到大衛的城裏。
To, sai aka faɗa wa Sarki Dawuda cewa, “Ubangiji ya sa wa gidan Obed-Edom albarka da dukan abin da yake da shi, saboda akwatin alkawarin Allah.” Saboda haka sai Dawuda ya gangara ya hauro da akwatin alkawarin Allah daga gidan Obed-Edom zuwa Birnin Dawuda da farin ciki.
13 抬耶和華約櫃的人走了六步,大衛就獻牛與肥羊為祭。
Sa’ad da waɗanda suke ɗaukan akwatin alkawarin Ubangiji suka yi tafiya taki shida, sai yă yi hadayar bijimi da saniya mai ƙiba.
14 大衛穿着細麻布的以弗得,在耶和華面前極力跳舞。
Dawuda, sanye da efod lilin, ya yi ta rawa a gaban Ubangiji da dukan ƙarfinsa,
15 這樣,大衛和以色列的全家歡呼吹角,將耶和華的約櫃抬上來。
yayinda shi da dukan gidan Isra’ila suka hauro da akwatin alkawarin Ubangiji da sowa da kuma busar ƙahoni.
16 耶和華的約櫃進了大衛城的時候,掃羅的女兒米甲從窗戶裏觀看,見大衛王在耶和華面前踴躍跳舞,心裏就輕視他。
Sa’ad da akwatin alkawarin Ubangiji ya shiga Birnin Dawuda, sai Mikal’yar Shawulu ta leƙa ta taga ta ga Dawuda sarki yana tsalle, yana rawa a gaban Ubangiji, sai ta rena shi a zuciyarta.
17 眾人將耶和華的約櫃請進去,安放在所預備的地方,就是在大衛所搭的帳幕裏。大衛在耶和華面前獻燔祭和平安祭。
Suka kawo akwatin alkawarin Ubangiji, aka ajiye shi a inda aka shirya masa a cikin tentin da Dawuda ya shirya dominsa. Dawuda kuma ya miƙa hadaya ta ƙonawa da hadaya ta salama a gaban Ubangiji.
18 大衛獻完了燔祭和平安祭,就奉萬軍之耶和華的名給民祝福,
Bayan ya gama yin hadaya ta ƙonawa da hadaya ta salama, sai ya albarkaci mutane a cikin sunan Ubangiji Maɗaukaki.
19 並且分給以色列眾人,無論男女,每人一個餅,一塊肉,一個葡萄餅;眾人就各回各家去了。
Sa’an nan ya rarraba abinci, da ƙosai, dabino, da waina ga kowane mutum a cikin dukan jama’ar Isra’ila, maza da mata. Dukan mutane kuwa suka watse zuwa gidajensu.
20 大衛回家要給眷屬祝福;掃羅的女兒米甲出來迎接他,說:「以色列王今日在臣僕的婢女眼前露體,如同一個輕賤人無恥露體一樣,有好大的榮耀啊!」
Da Dawuda ya koma gida don yă sa wa gidansa albarka, sai Mikal’yar Shawulu ta fito don tă tarye shi, sai ta ce, “Tabbas sarkin Isra’ila ya fiffita kansa yau, ya tuɓe a gaban bayinsa’yan mata, kamar yadda duk marar kunya yakan yi!”
21 大衛對米甲說:「這是在耶和華面前;耶和華已揀選我,廢了你父和你父的全家,立我作耶和華民以色列的君,所以我必在耶和華面前跳舞。
Dawuda ya ce wa Mikal, “Na yi rawana domin in girmama Ubangiji ne, wanda ya zaɓe ni a maimakon mahaifinki ko wani daga cikin dukan gidansa, shi ne kuma ya sa ni sarki a kan Isra’ila, mutanen Ubangiji, zan yi biki a gaban Ubangiji.
22 我也必更加卑微,自己看為輕賤。你所說的那些婢女,她們倒要尊敬我。」
Zan ma mai da kaina abin reni fiye da haka, za a kuma zama abin reni a gare ki. Amma waɗannan bayi’yan matan da kika yi magana a kai, za su gan ni da martaba.”
23 掃羅的女兒米甲,直到死日,沒有生養兒女。
Mikal’yar Shawulu kuwa ba tă haifi ɗa ba har mutuwarta.

< 撒母耳記下 6 >