< 歷代志上 5 >
1 以色列的長子原是呂便;因他污穢了父親的床,他長子的名分就歸了約瑟。只是按家譜他不算長子。
’Ya’yan Ruben maza ɗan farin Isra’ila (shi ne ɗan fari, amma sa’ad da ya ƙazantar da gadon auren mahaifinsa, sai aka ba wa’yancin ɗan farinsa wa’ya’yan Yusuf maza ɗan Isra’ila; don kada a lissafta shi a tarihin zuriya bisa ga matsayin haihuwarsa,
2 猶大勝過一切弟兄,君王也是從他而出;長子的名分卻歸約瑟。
ko da yake Yahuda shi ne mafi ƙarfi cikin’yan’uwansa kuma mai mulki ya fito daga gare shi,’yancin zaman ɗan fari na Yusuf ne),
3 以色列長子呂便的兒子是哈諾、法路、希斯倫、迦米。
’ya’yan Ruben ɗan farin Isra’ila maza su ne, Hanok, Fallu, Hezron da Karmi.
4 約珥的兒子是示瑪雅;示瑪雅的兒子是歌革;歌革的兒子是示每;
Zuriyar Yowel su ne, Shemahiya, Gog, Shimeyi,
5 示每的兒子是米迦;米迦的兒子是利亞雅;利亞雅的兒子是巴力;
Mika, Reyahiya, Ba’al,
6 巴力的兒子是備拉。這備拉作呂便支派的首領,被亞述王提革拉‧毗列色擄去。
da Beyera, wanda Tiglat-Fileser sarkin Assuriya ya ɗauka zuwa zaman bauta. Beyera shi ne shugaban mutanen Ruben.
7 他的弟兄照着宗族,按着家譜作族長的是耶利、撒迦利雅、比拉。
Danginsu bisa ga iyalansu da aka jera bisa ga tarihin zuriyarsu su ne, Yehiyel shi ne sarki, akwai Zakariya,
8 比拉是亞撒的兒子;亞撒是示瑪的兒子;示瑪是約珥的兒子;約珥所住的地方是從亞羅珥直到尼波和巴力‧免,
da Bela ɗan Azaz. Azaz ɗan Shema daga dangin Yowel. Yowel ya yi zama a yankin Arower har zuwa Nebo da Ba’al-Meyon.
9 又向東延到幼發拉底河這邊的曠野,因為他們在基列地牲畜增多。
Ta waje gabas sun zauna a ƙasar har zuwa bakin hamadan da ya nausa zuwa Kogin Yuferites, domin dabbobinsu sun ƙaru a Gileyad.
10 掃羅年間,他們與夏甲人爭戰,夏甲人倒在他們手下,他們就在基列東邊的全地,住在夏甲人的帳棚裏。
A zamanin Shawulu zuriyar Ruben sun yi yaƙi da Hagirawa, suka ci su da yaƙi, suka zauna a wuraren zaman Hagirawan ko’ina a dukan yankin gabashin Gileyad.
11 迦得的子孫在呂便對面,住在巴珊地,延到撒迦。
Mutanen Gad sun zauna kusa da mutanen Ruben a Bashan, har zuwa Saleka.
12 他們中間有作族長的約珥,有作副族長的沙番,還有雅乃和住在巴珊的沙法。
Yowel shi ne babba, sai Shafan na biyu, sa’an nan Yanai da Shafat, su ne tushen Bashan.
13 他們族弟兄是米迦勒、米書蘭、示巴、約賴、雅干、細亞、希伯,共七人。
Danginsu, bisa ga iyalai su ne, Mika’ilu, Meshullam, Sheba, Yorai, Yakan, Ziya da Eber, su bakwai ne duka.
14 這都是亞比孩的兒子。亞比孩是戶利的兒子;戶利是耶羅亞的兒子;耶羅亞是基列的兒子;基列是米迦勒的兒子;米迦勒是耶示篩的兒子;耶示篩是耶哈多的兒子;耶哈多是布斯的兒子。
Waɗannan su ne’ya’yan Abihayil ɗan Huri, ɗan Yarowa, ɗan Gileyad, ɗan Mika’ilu, ɗan Yeshishai, ɗan Yado, ɗan Buz.
15 還有古尼的孫子、押比疊的兒子亞希。這都是作族長的。
Ahi ɗan Abiyel, ɗan Guni, shi ne kan iyalinsu.
16 他們住在基列與巴珊和巴珊的鄉村,並沙崙的郊野,直到四圍的交界。
Mutanen Gad sun zauna a Bashan da ƙauyukan da suke kurkusa da shi, da kuma a dukan makiyayan Sharon har zuwa iyaka inda suka kai.
17 這些人在猶大王約坦並在以色列王耶羅波安年間,都載入家譜。
Dukan waɗannan sun shiga tarihin zuriya a lokacin mulkin Yotam sarkin Yahuda da Yerobowam sarkin Isra’ila.
18 呂便人、迦得人,和瑪拿西半支派的人,能拿盾牌和刀劍、拉弓射箭、出征善戰的勇士共有四萬四千七百六十名。
Mutanen Ruben, mutanen Gad da rabin kabilar Manasse sun kasance da mutane 44,760 shiryayyu don aikin soja, jarumawan da za su iya riƙe garkuwa da takobi, waɗanda suke iya yin amfani da baka, waɗanda kuma aka horar don yaƙi.
19 他們與夏甲人、伊突人、拿非施人、挪答人爭戰。
Suka yi yaƙi da Hagirawa, Yetur, Nafish da Nodab.
20 他們得了上帝的幫助,夏甲人和跟隨夏甲的人都交在他們手中;因為他們在陣上呼求上帝,倚賴上帝,上帝就應允他們。
Aka taimake su a yaƙin, Allah kuma ya ba da Hagirawa da dukan abokansu gare su, domin sun yi kuka gare shi a lokacin yaƙin. Ya amsa addu’o’insu, domin sun dogara gare shi.
21 他們擄掠了夏甲人的牲畜,有駱駝五萬,羊二十五萬,驢二千;又有人十萬。
Suka ƙwace dabbobin Hagirawa, raƙuma dubu hamsin, tumaki dubu ɗari biyu da hamsin da kuma jakuna dubu biyu. Suka kuma kame mutane dubu ɗari ɗaya,
22 敵人被殺仆倒的甚多,因為這爭戰是出乎上帝。他們就住在敵人的地上,直到被擄的時候。
waɗansu suka mutu, domin yaƙin na Allah ne. Suka zauna a ƙasar har lokacin da aka kai su zaman bauta.
23 瑪拿西半支派的人住在那地。從巴珊延到巴力‧黑們、示尼珥與黑門山。
Mutanen rabin kabilar Manasse sun yi yawa; suka zauna a ƙasar daga Bashan har zuwa Ba’al-Hermon, wato, zuwa Senir (Dutsen Hermon).
24 他們的族長是以弗、以示、以列、亞斯列、耶利米、何達威雅、雅疊,都是大能的勇士,是有名的人,也是作族長的。
Waɗannan su ne kawunan iyalansu. Efer, Ishi, Eliyel, Azriyel, Irmiya, Hodawiya da Yadiyel. Su jarumawa ne, sanannu, su ne kuma kawunan iyalansu.
25 他們得罪了他們列祖的上帝,隨從那地之民的神行邪淫;這民就是上帝在他們面前所除滅的。
Amma ba su yi aminci da Allahn kakanninsu ba, suka kuma yi karuwanci ga waɗansu allolin mutanen ƙasar, waɗanda Allah ya hallaka a gabansu.
26 故此,以色列的上帝激動亞述王普勒和亞述王提革拉‧毗列色的心,他們就把呂便人、迦得人、瑪拿西半支派的人擄到哈臘、哈博、哈拉與歌散河邊,直到今日還在那裏。
Saboda haka Allah na Isra’ila ya zuga ruhun Ful sarkin Assuriya (wato, Tiglat-Fileser sarkin Assuriya), wanda ya kwashe mutanen Ruben, mutanen Gad da rabin kabilar Manasse zuwa zaman bauta. Ya kwashe su zuwa Hala, Habor, Hara da kuma kogin Gozan, inda suke har wa yau.