< 歷代志上 13 >
Sai Dawuda ya tattauna da kowane ɗaya daga cikin shugabanninsa, shugabannin sojoji na dubu-dubu da na ɗari-ɗari.
2 大衛對以色列全會眾說:「你們若以為美,見這事是出於耶和華-我們的上帝,我們就差遣人走遍以色列地,見我們未來的弟兄,又見住在有郊野之城的祭司利未人,使他們都到這裏來聚集。
Sa’an nan ya ce wa dukan taron Isra’ila, “In ya yi muku kyau kuma in nufin Ubangiji Allahnmu ne, bari mu aika da saƙo nesa da kuma ko’ina zuwa ga sauran’yan’uwanmu a duk iyakokin Isra’ila, da kuma zuwa ga firistoci da Lawiyawa waɗanda suke tare da su a garuruwansu da makiyayansu, su zo wurinmu.
3 我們要把上帝的約櫃運到我們這裏來;因為在掃羅年間,我們沒有在約櫃前求問上帝。」
Bari mu ɗauko akwatin alkawarin Allahnmu mu kawo wurinmu, gama ba mu neme shi a lokacin mulkin Shawulu ba.”
4 全會眾都說可以如此行;這事在眾民眼中都看為好。
Dukan taron jama’a suka yarda su yi haka, domin ya yi daidai ga dukan mutane.
5 於是,大衛將以色列人從埃及的西曷河直到哈馬口都招聚了來,要從基列‧耶琳將上帝的約櫃運來。
Saboda haka Dawuda ya tattara dukan Isra’ilawa, daga Kogin Shihor a Masar zuwa Lebo Hamat, don su kawo akwatin alkawarin Allah daga Kiriyat Yeyarim.
6 大衛率領以色列眾人上到巴拉,就是屬猶大的基列‧耶琳,要從那裏將約櫃運來。這約櫃就是坐在二基路伯上耶和華上帝留名的約櫃。
Dawuda da dukan Isra’ilawa tare da shi suka tafi Ba’ala na Yahuda (Kiriyat Yeyarim) don su haura daga can su kawo akwatin alkawarin Allah Ubangiji, wanda yake zama tsakanin kerubobi, akwatin alkawarin da ake kira da Sunan.
7 他們將上帝的約櫃從亞比拿達的家裏抬出來,放在新車上。烏撒和亞希約趕車。
Suka ɗauki akwatin alkawarin Allah daga gidan Abinadab a kan sabon keken shanu, Uzza da Ahiyo ne suke lura da shi.
8 大衛和以色列眾人在上帝前用琴、瑟、鑼、鼓、號作樂,極力跳舞歌唱。
Dawuda da dukan Isra’ilawa suka yi shagali da dukan ƙarfinsu a gaban Allah, tare da waƙoƙi da garayu, molaye, ganguna, kuge da ƙahoni.
9 到了基頓的禾場;因為牛失前蹄,烏撒就伸手扶住約櫃。
Sa’ad da suka kai masussukar Kidon, Uzza ya miƙa hannunsa don yă gyara akwatin alkawarin, gama shanun sun yi tuntuɓe.
10 耶和華向他發怒,因他伸手扶住約櫃擊殺他,他就死在上帝面前。
Sai fushin Ubangiji ya ƙuna a kan Uzza, ya kuma buge shi domin ya sa hannunsa a kan akwatin alkawarin. Sai ya mutu a can a gaban Allah.
11 大衛因耶和華擊殺烏撒,心裏愁煩,就稱那地方為毗列斯‧烏撒,直到今日。
Ran Dawuda ya ɓace domin Ubangiji ya husata a kan Uzza, kuma har wa yau ana ce da wannan wuri Ferez Uzza.
12 那日,大衛懼怕上帝,說:「上帝的約櫃怎可運到我這裏來?」
Dawuda ya ji tsoron Allah a wannan rana ya kuma yi tambaya, “Yaya zan taɓa kawo akwatin alkawarin Allah gare ni?”
13 於是大衛不將約櫃運進大衛的城,卻運到迦特人俄別‧以東的家中。
Don haka bai ɗauki akwatin alkawarin ya kasance tare da shi a Birnin Dawuda ba. A maimakon haka, ya kai shi gidan Obed-Edom mutumin Gat.
14 上帝的約櫃在俄別‧以東家中三個月,耶和華賜福給俄別‧以東的家和他一切所有的。
Akwatin Alkawarin Allah ya zauna tare da iyalin Obed-Edom a gidansa wata uku, Ubangiji kuwa ya albarkaci gidan Obed-Edom da kome da yake da shi.