< 歷代志上 12 >
1 大衛因怕基士的兒子掃羅,躲在洗革拉的時候,有勇士到他那裏幫助他打仗。
Waɗannan su ne mutanen da suka zo wurin Dawuda a Ziklag, yayinda aka kore shi daga gaban Shawulu ɗan Kish (suna cikin jarumawan da suka taimake shi a yaƙi;
2 他們善於拉弓,能用左右兩手甩石射箭,都是便雅憫人掃羅的族弟兄。
suna da baka suna kuma iya harba kibiya, ko majajjawa da hannun dama ko na hagu; su’yan’uwan Shawulu ne daga kabilar Benyamin):
3 為首的是亞希以謝,其次是約阿施,都是基比亞人示瑪的兒子。還有亞斯瑪威的兒子耶薛和毗力,又有比拉迦,並亞拿突人耶戶,
Ahiyezer babbansu da Yowash’ya’yan Shema’a maza daga Gibeya; Yeziyel da Felet’ya’yan Azmawet; Beraka, Yehu daga Anatot,
4 基遍人以實買雅(他在三十人中是勇士,管理他們),且有耶利米、雅哈悉、約哈難,和基得拉人約撒拔、
da Ishmahiya daga Gibeyon, wani jarumi a cikin Talatin nan, wanda shi ne shugaban Talatin; Irmiya, Yahaziyel, Yohanan, Yozabad daga Gedera,
5 伊利烏賽、耶利摩、比亞利雅、示瑪利雅,哈律弗人示法提雅,
Eluzai, Yerimot, Beyaliya, Shemariya da Shefatiya daga Haruf;
6 可拉人以利加拿、耶西亞、亞薩列、約以謝、雅朔班,
Elkana, Isshiya, Azarel, Yoyezer da Yashobeyam daga Kora;
da Yoyela da Zebadiya’ya’yan Yeroham maza daga Gedor.
8 迦得支派中有人到曠野的山寨投奔大衛,都是大能的勇士,能拿盾牌和槍的戰士。他們的面貌好像獅子,快跑如同山上的鹿。
Sai waɗansu mutanen Gad suka koma suna goyon bayan Dawuda suka kuma haɗa kai da shi a kagararsa a hamada. Su ƙwararrun mayaƙa ne, a shirye don yaƙi, kuma suna iya riƙe garkuwa da māshi. Fuskokinsu kamar fuskoki zakoki, kuma suna da sauri kamar bareyi a kan duwatsu.
Ezer shi ne babba, Obadiya shi ne mai binsa a shugabanci, Eliyab na uku,
Mismanna na huɗu, Irmiya na biyar,
Attai na shida, Eliyel na bakwai,
Yohanan na takwas, Elzabad na tara,
Irmiya na goma da kuma Makbannai na goma sha ɗaya.
14 這都是迦得人中的軍長,至小的能抵一百人,至大的能抵一千人。
Waɗannan mutanen Gad shugabannin mayaƙa ne; ƙarami a cikinsu zai iya ƙara da mutum ɗari, kuma babba a cikin zai iya ƙara da dubu.
15 正月,約旦河水漲過兩岸的時候,他們過河,使一切住平原的人東奔西逃。
Su ne suka haye Urdun a wata na farko sa’ad da kogin ya yi ambaliya, suka kuma kori duk mai rai a kwarin, na wajen gabas da na wajen yamma.
Sauran mutanen Benyamin da waɗansu mutanen Yahuda su ma suka zo wurin Dawuda a kagararsa.
17 大衛出去迎接他們,對他們說:「你們若是和和平平地來幫助我,我心就與你們相契;你們若是將我這無罪的人賣在敵人手裏,願我們列祖的上帝察看責罰。」
Sai Dawuda ya fita don yă tarye su, ya kuma ce musu, “In kun zo wurina da salama, don ku taimake ni, to, ina a shirye in bar ku ku haɗa kai tare da ni. Amma in kun zo don ku bashe ni ga abokan gābana sa’ad da hannuwana ba su da laifi a rikici, bari Allah na kakanninmu yă duba yă kuma shari’anta ku.”
18 那時上帝的靈感動那三十個勇士的首領亞瑪撒,他就說: 大衛啊,我們是歸於你的! 耶西的兒子啊,我們是幫助你的! 願你平平安安, 願幫助你的也都平安! 因為你的上帝幫助你。 大衛就收留他們,立他們作軍長。
Sai Ruhu ya sauko a kan Amasai, shugaban Talatin nan, sai ya ce, “Mu naka ne, ya Dawuda! Muna tare da kai, ya ɗan Yesse! Nasara, nasara gare ka, nasara kuma ga waɗanda suke taimakonka. Gama Allahnka zai taimake ka.” Saboda haka Dawuda ya karɓe su ya kuma mai da su shugabannin ƙungiyoyin maharansa.
19 大衛從前與非利士人同去,要與掃羅爭戰,有些瑪拿西人來投奔大衛,他們卻沒有幫助非利士人;因為非利士人的首領商議,打發他們回去,說:「恐怕大衛拿我們的首級,歸降他的主人掃羅。」
Waɗansu mutanen Manasse suka haɗa kai da Dawuda sa’ad da ya tafi tare da Filistiyawa don yă yaƙi Shawulu (Shi da mutanensa ba su taimaki Filistiyawa ba domin bayan shawarwari, shugabanninsu suka salame shi. Sun ce, “Za mu biya da kawunanmu in ya koma ga maigidansa Shawulu.”)
20 大衛往洗革拉去的時候,有瑪拿西人的千夫長押拿、約撒拔、耶疊、米迦勒、約撒拔、以利戶、洗勒太都來投奔他。
Da Dawuda ya tafi Ziklag, waɗannan mutanen Manasse ne suka haɗa kai da shi. Adna, Yozabad, Yediyayel, Mika’ilu, Yozabad, Elihu da Zilletai, shugabannin ƙungiyoyi na dubu a cikin Manasse.
21 這些人幫助大衛攻擊群賊;他們都是大能的勇士,且作軍長。
Suka taimaki Dawuda a kan ƙungiyoyin hari, gama dukansu jarumawa ne sosai, kuma su shugabanni ne a cikin mayaƙansa.
22 那時天天有人來幫助大衛,以致成了大軍,如上帝的軍一樣。
Kowace rana mutane suka riƙa zuwa don su taimaki Dawuda, sai da ya kasance da runduna mai girma, kamar mayaƙan Allah.
23 預備打仗的兵來到希伯崙見大衛,要照着耶和華的話將掃羅的國位歸與大衛。他們的數目如下:
Ga yawan mutanen shiryayyu don yaƙi waɗanda suka zo wurin Dawuda a Hebron don su mai da mulkin Shawulu gare shi, yadda Ubangiji ya faɗa.
24 猶大支派,拿盾牌和槍預備打仗的有六千八百人。
Mutanen Yahuda, masu riƙe garkuwa da māshi, su 6,800 shiryayyu don yaƙi;
mutanen Simeyon, jarumawa shiryayyu don yaƙi, su 7,100;
27 耶何耶大是亞倫家的首領,跟從他的有三千七百人。
haɗe da Yehohiyada, shugaban iyalin Haruna tare da mutane 3,700,
28 還有少年大能的勇士撒督,同着他的有族長二十二人。
da Zadok, matashi jarumi sosai, tare da shugabanni su 22 daga iyalinsa;
29 便雅憫支派,掃羅的族弟兄也有三千人,他們向來大半歸順掃羅家。
mutanen Benyamin,’yan’uwan Shawulu, su 3,000, yawanci waɗanda suke biyayya ga gidan Shawulu sai lokacin;
30 以法蓮支派大能的勇士,在本族著名的有二萬零八百人。
mutanen Efraim, jarumawa, sanannu cikin gidajensu, su 20 800;
31 瑪拿西半支派,冊上有名的共一萬八千人,都來立大衛作王。
mutanen rabin kabilar Manasse, sanannu da sunaye suka zo suka mai da Dawuda sarki, su 18,000;
32 以薩迦支派,有二百族長都通達時務,知道以色列人所當行的;他們族弟兄都聽從他們的命令。
mutanen Issakar, masu fahimtar lokuta suka kuma san abin da ya kamata Isra’ila ya yi, manya 200, tare da danginsu a ƙarƙashin shugabancinsu;
33 西布倫支派,能上陣用各樣兵器打仗、行伍整齊、不生二心的有五萬人。
mutanen Zebulun, ƙwararru sojoji shiryayyu don yaƙi da kowane irin makami, suka zo don su taimaki Dawuda da zuciya ɗaya, su 50,000;
34 拿弗他利支派,有一千軍長;跟從他們、拿盾牌和槍的有三萬七千人。
mutanen Naftali su 1,000 shugabanni, tare da mutane 37,000 masu riƙe garkuwa da masu;
mutanen Dan, shiryayyu don yaƙi, su 28,600;
mutanen Asher, ƙwararrun sojoji shiryayyu don yaƙi, su 40,000;
37 約旦河東的呂便支派、迦得支派、瑪拿西半支派,拿着各樣兵器打仗的有十二萬人。
kuma daga gabashin Urdun, mutanen Ruben, Gad da kuma rabin kabilar Manasse, masu kayan yaƙi iri-iri, su 120,000.
38 以上都是能守行伍的戰士,他們都誠心來到希伯崙,要立大衛作以色列的王。以色列其餘的人也都一心要立大衛作王。
Dukan waɗannan mayaƙa ne waɗanda suka ba da kansu da yardar rai su yi hidima. Suka zo Hebron da cikakken niyya don su naɗa Dawuda sarki a bisa dukan Isra’ila. Duka sauran Isra’ilawa su ma suka goyi baya a naɗa Dawuda sarki.
39 他們在那裏三日,與大衛一同吃喝,因為他們的族弟兄給他們預備了。
Mutanen suka yi kwana uku a can tare da Dawuda, suna ci suna sha, gama iyalansu sun yi musu tanadi.
40 靠近他們的人以及以薩迦、西布倫、拿弗他利人將許多麵餅、無花果餅、乾葡萄、酒、油,用驢、駱駝、騾子、牛馱來,又帶了許多的牛和羊來,因為以色列人甚是歡樂。
Haka ma, maƙwabtansu daga nesa har Issakar, Zebulun da Naftali suka zo suka kawo abinci a kan jakuna, raƙuma, alfadarai da shanu. Akwai tanadin mai yawa na gari, kauɗar ɓaure, nonnan busassun’ya’yan inabi, ruwan inabi, mai, shanu da tumaki. Duk an yi haka don a nuna farin ciki ƙwarai a cikin dukan ƙasar Isra’ila.