< 诗篇 52 >
1 以东人多益来告诉扫罗说:“大卫到了亚希米勒家。”那时,大卫作这训诲诗,交与伶长。 勇士啊,你为何以作恶自夸? 神的慈爱是常存的。
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Wani maskil ta Dawuda. Sa’ad da Doyeg mutumin Edom ya tafi wurin Shawulu ya ce masa, “Dawuda ya tafi gidan Ahimelek.” Me ya sa kake fariya game da mugunta, kai babban mutum? Me ya sa kake fariya dukan yini, kai da kake abin kunya a idanun Allah?
Harshenka kan shirya hallaka; yana nan kamar reza mai ci, kana ta ruɗu.
3 你爱恶胜似爱善, 又爱说谎,不爱说公义。 (细拉)
Kana ƙaunar mugunta fiye da alheri, ƙarya a maimakon faɗin gaskiya. (Sela)
Kana ƙaunar kowace kalmar cutarwa, Ya kai harshe mai ruɗu!
5 神也要毁灭你,直到永远; 他要把你拿去,从你的帐棚中抽出, 从活人之地将你拔出。 (细拉)
Tabbatacce Allah zai kai ka ga madawwamiyar hallaka. Zai fizge ka yă yayyage ka daga tentinka; zai tumɓuke ka daga ƙasar masu rai. (Sela)
Masu adalci za su ga su ji tsoro; za su yi masa dariya, suna cewa,
7 说:看哪,这就是那不以 神为他力量的人, 只倚仗他丰富的财物,在邪恶上坚立自己。
“Yanzu, ga mutumin da bai mai da Allah mafakarsa ba amma ya dogara a yawan arzikinsa ya kuma yi ƙarfi ta wurin hallaka waɗansu!”
8 至于我,就像 神殿中的青橄榄树; 我永永远远倚靠 神的慈爱。
Amma ni kamar itace zaitun ne ina haɓaka a gidan Allah; na dogara ga ƙauna marar ƙarewa ta Allah har abada abadin.
9 我要称谢你,直到永远, 因为你行了这事。 我也要在你圣民面前仰望你的名; 这名本为美好。
Zan yabe ka har abada game da abin da ka yi; a cikin sunanka zan dogara, gama sunanka yana da kyau. Zan yabe ka a gaban tsarkakanka.