< 诗篇 125 >

1 上行之诗。 倚靠耶和华的人 好像锡安山,永不动摇。
Waƙar haurawa. Waɗanda suke dogara ga Ubangiji suna kama da Dutsen Sihiyona, wanda ba ya jijjiguwa amma dawwammame ne har abada.
2 众山怎样围绕耶路撒冷, 耶和华也照样围绕他的百姓, 从今时直到永远。
Kamar duwatsun da sun kewaye Urushalima, haka Ubangiji ya kewaye mutanensa yanzu da har abada kuma.
3 恶人的杖不常落在义人的分上, 免得义人伸手作恶。
Sandar mulkin mugaye ba zai ci gaba da kasance a kan ƙasar da take rabon adalai ba, domin kada masu adalci su yi amfani da hannuwansu su aikata mugunta.
4 耶和华啊,求你善待那些为善 和心里正直的人。
Ka yi alheri, ya Ubangiji, ga waɗanda suke nagartattu, ga waɗanda suke masu aikata gaskiya a zuciyarsu.
5 至于那偏行弯曲道路的人, 耶和华必使他和作恶的人一同出去受刑。 愿平安归于以色列!
Amma waɗanda suka juye ga karkatattun hanyoyi Ubangiji zai kore su tare da masu aikata mugunta. Salama tă kasance tare da Isra’ila.

< 诗篇 125 >