< 民数记 36 >

1 约瑟的后裔,玛拿西的孙子,玛吉的儿子基列,他子孙中的诸族长来到摩西和作首领的以色列人族长面前,说:
Sai shugabannin gidajen iyalan Gileyad ɗan Makir, ɗan Manasse, waɗanda suka fito daga kabilar zuriyar Yusuf, suka zo, suka yi magana a gaban Musa da shugabanni, shugabannin iyalan Isra’ilawa.
2 “耶和华曾吩咐我主拈阄分地给以色列人为业,我主也受了耶和华的吩咐将我们兄弟西罗非哈的产业分给他的众女儿。
Suka ce, “Sa’ad da Ubangiji ya umarce ranka yă daɗe, yă raba ƙasar gādo ga Isra’ilawa ta wurin ƙuri’a, ya umarce ka, ka ba wa’ya’ya matan nan na Zelofehad ɗan’uwanmu gādonsa.
3 她们若嫁以色列别支派的人,就必将我们祖宗所遗留的产业加在她们丈夫支派的产业中。这样,我们拈阄所得的产业就要减少了。
To, a ce sun auri mutane daga waɗansu kabilan Isra’ilawa fa; ka ga, za a ɗebe gādonsu daga gādon kakanninmu a ƙara wa gādon kabilan mutanen da suka aura ke nan. Ta haka za a ɗebe sashe daga gādon da aka ba mu ke nan.
4 到了以色列人的禧年,这女儿的产业就必加在她们丈夫支派的产业上。这样,我们祖宗支派的产业就减少了。”
Sa’ad da Shekara ta Murnar Isra’ilawa ta kewayo, za a haɗa gādonsu da na kabilan mutanen da suka aura, a kuma ba su mallakar gādon da aka ɗebe daga kabilar kakanninmu.”
5 摩西照耶和华的话吩咐以色列人说:“约瑟支派的人说得有理。
Ta wurin umarnin Ubangiji, Musa ya ba Isra’ilawa wannan umarni, “Abin da kabilar zuriyar Yusuf suke faɗi, daidai ne.
6 论到西罗非哈的众女儿,耶和华这样吩咐说:她们可以随意嫁人,只是要嫁同宗支派的人。
Ga abin da Ubangiji ya umarta saboda’ya’ya matan nan na Zelofehad. Za su iya auri duk wanda suka ga dama, muddin sun yi aure a cikin kabilar kakanninsu.
7 这样,以色列人的产业就不从这支派归到那支派,因为以色列人要各守各祖宗支派的产业。
Ba gādon Isra’ilan da za a ba wa wata kabila daga wata kabila, gama kowane mutumin Isra’ila zai riƙe gādonsa na kabilar da ya gāda daga kakanninsa.
8 凡在以色列支派中得了产业的女子必作同宗支派人的妻,好叫以色列人各自承受他祖宗的产业。
Kowace’ya wadda ta ci gādon ƙasa, a kowace kabilar Isra’ilawa, dole tă auri wani cikin kabilar kakanninta, saboda kowane mutumin Isra’ila yă mallaki gādon kakanninsa.
9 这样,他们的产业就不从这支派归到那支派,因为以色列支派的人要各守各的产业。”
Ba gādon da za a ba wa wata kabila daga wata kabila, gama kowace kabilar Isra’ilawa za tă riƙe mallaka da ta gāda.”
10 耶和华怎样吩咐摩西,西罗非哈的众女儿就怎样行。
Saboda haka’ya’yan Zelofehad mata suka yi yadda Ubangiji ya umarci Musa.
11 西罗非哈的女儿玛拉、得撒、曷拉、密迦、挪阿都嫁了他们伯叔的儿子。
’Ya’yan Zelofehad mata, Mala, Tirza, Hogla, Milka da Nowa, suka auri’ya’yan’yan’uwa na gefen mahaifinsu.
12 她们嫁入约瑟儿子、玛拿西子孙的族中;她们的产业仍留在同宗支派中。
Suka yi aure cikin kabilar zuriyar Manasse ɗan Yusuf, gādonsu kuwa ya kasance a cikin iyali da kuma kabilar mahaifinsu.
13 这是耶和华在摩押平原—约旦河边、耶利哥对面—借着摩西所吩咐以色列人的命令典章。
Waɗannan su ne umarnai da ƙa’idodin da Ubangiji ya ba wa Isra’ilawa ta wurin Musa, a filayen Mowab kusa da Urdun, ɗaura da Yeriko.

< 民数记 36 >