< 民数记 25 >

1 以色列人住在什亭,百姓与摩押女子行起淫乱。
Lokacin da Isra’ila suke a sansani a Shittim, sai maza suka fara yin lalata da matan Mowabawa,
2 因为这女子叫百姓来,一同给她们的神献祭,百姓就吃她们的祭物,跪拜她们的神。
waɗanda suka gayyace su zuwa wajen hadayu na allolinsu. Mutane suka ci suka kuma yi wa waɗannan alloli sujada.
3 以色列人与巴力·毗珥连合,耶和华的怒气就向以色列人发作。
Ta haka Isra’ila suka sa kai a bautar gumaka Ba’al-Feyor. Ubangiji kuwa ya husata da su.
4 耶和华吩咐摩西说:“将百姓中所有的族长在我面前对着日头悬挂,使我向以色列人所发的怒气可以消了。”
Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka kama dukan shugabannin mutanen nan, ka kashe su, ka kuma bar su a tsakar rana a gaban Ubangiji, don Ubangiji yă huce daga fushin da nake yi da Isra’ila.”
5 于是摩西吩咐以色列的审判官说:“凡属你们的人,有与巴力·毗珥连合的,你们各人要把他们杀了。”
Saboda haka Musa ya ce wa alƙalan Isra’ila, “Dole kowannenku yă kashe mutanen nan da suka haɗa kai cikin bautar Ba’al-Feyor.”
6 摩西和以色列全会众正在会幕门前哭泣的时候,谁知,有以色列中的一个人,当他们眼前,带着一个米甸女人到他弟兄那里去。
Sa’an nan wani mutumin Isra’ila ya kawo wata Bamidiyana a iyalinsa a idon Musa da dukan taron jama’ar Isra’ila, yayinda suke kuka a ƙofar Tentin Sujada.
7 祭司亚伦的孙子,以利亚撒的儿子非尼哈看见了,就从会中起来,手里拿着枪,
Da Finehas ɗan Eleyazar, ɗan Haruna, firist, ya ga haka, sai ya bar taron, ya ɗauki māshi
8 跟随那以色列人进亭子里去,便将以色列人和那女人由腹中刺透。这样,在以色列人中瘟疫就止息了。
ya bi mutumin Isra’ilan nan cikin tenti, ya soke dukansu biyu, māshin ya ratsa jikin mutumin Isra’ilan har zuwa jikin macen. Sa’an nan aka tsai da annoban nan a kan Isra’ilawa.
9 那时遭瘟疫死的,有二万四千人。
Waɗanda suka mutu a wannan annoba, sun kai mutum 24,000.
10 耶和华晓谕摩西说:
Ubangiji ya ce wa Musa,
11 “祭司亚伦的孙子,以利亚撒的儿子非尼哈,使我向以色列人所发的怒消了;因他在他们中间,以我的忌邪为心,使我不在忌邪中把他们除灭。
“Finehas ɗan Eleyazar, ɗan Haruna, firist, ya kawar da fushina daga Isra’ilawa; saboda ya yi kishi irin nawa a gabansu, don haka saboda ɗaukakata ban kawo ƙarshensu ba.
12 因此,你要说:‘我将我平安的约赐给他。
Saboda haka ka faɗa masa cewa zan yi alkawarin salama da shi.
13 这约要给他和他的后裔,作为永远当祭司职任的约;因他为 神有忌邪的心,为以色列人赎罪。’”
Shi da zuriyarsa za su kasance da alkawari na zama firist har abada, saboda kishinsa domin ɗaukakar Allahnsa, ya kuma yi kafara domin Isra’ilawa.”
14 那与米甸女人一同被杀的以色列人,名叫心利,是撒路的儿子,是西缅一个宗族的首领。
Sunan mutumin Isra’ilan da aka kashe tare da macen nan Bamidiyana kuwa Zimri ne, ɗan Salu, shugaban mutanen Simeyon.
15 那被杀的米甸女人,名叫哥斯比,是苏珥的女儿;这苏珥是米甸一个宗族的首领。
Sunan macen nan Bamidiyana da aka kashe kuwa Kozbi ne,’yar Zur, wani basaraken iyalin Midiyawa.
16 耶和华晓谕摩西说:
Ubangiji ya ce wa Musa,
17 “你要扰害米甸人,击杀他们;
“Ka ɗauki Midiyawa a matsayin abokan gāba, ka kuma kashe su,
18 因为他们用诡计扰害你们,在毗珥的事上和他们的姊妹、米甸首领的女儿哥斯比的事上,用这诡计诱惑了你们;这哥斯比,当瘟疫流行的日子,因毗珥的事被杀了。”
gama sun ɗauke ku a matsayin abokan gāba, sa’ad da suka ruɗe ku a kan al’amuran Feyor da’yar’uwarsu Kozbi’yar shugaban Midiyawa, macen da aka kashe a annoba ta dalili Feyor.”

< 民数记 25 >