< 约书亚记 15 >
1 犹大支派按着宗族拈阄所得之地是在尽南边,到以东的交界,向南直到寻的旷野。
An raba wa kabilar Yahuda gādonsu ta wurin yin ƙuri’a, bisa ga iyalansu, rabon ya kai har zuwa sashen Edom, zuwa Jejin Zin can kurewar kudu.
2 他们的南界是从盐海的尽边,就是从朝南的海汊起,
Iyakarsu a kudanci ta tashi tun daga kurewar kudu na Tekun Gishiri,
3 通到亚克拉滨坡的南边,接连到寻,上到加低斯·巴尼亚的南边,又过希斯 ,上到亚达珥,绕到甲加,
zuwa kudancin Hanyar Kunama, ta ci gaba har zuwa Zin, zuwa kudancin Kadesh Barneya. Sa’an nan ta kurɗa zuwa Hezron har zuwa Addar, ta kuma karkata zuwa Karka.
4 接连到押们,通到埃及小河,直通到海为止。这就是他们的南界。
Sai ta wuce zuwa Azmon ta haɗu da Rafin Masar, ta ƙarasa a Bahar Rum. Wannan shi ne iyakarsu ta kudu.
5 东界是从盐海南边到约旦河口。北界是从约旦河口的海汊起,
Iyakarsu ta gabas kuwa ita ce Tekun Gishiri wadda ta zarce har zuwa gaɓar Urdun. Iyakarsu ta arewa ta fara ne daga Tekun Gishiri a bakin Urdun,
6 上到伯·曷拉,过伯·亚拉巴的北边,上到吕便之子波罕的磐石;
wajen Bet-Hogla ta wuce har zuwa arewancin Bet-Araba, zuwa Dutsen Bohan ɗan Ruben.
7 从亚割谷往北,上到底璧,直向河南亚都冥坡对面的吉甲;又接连到隐·示麦泉,直通到隐·罗结,
Sai iyakar ta haura zuwa Debir daga Kwarin Akor ta juya arewa da Gilgal, wadda take fuskantar hawan Adummim a kudancin kwari, ta ci gaba zuwa ruwan En Shemesh, ta ɓullo ta En Rogel.
8 上到欣嫩子谷,贴近耶布斯的南界(耶布斯就是耶路撒冷);又上到欣嫩谷西边的山顶,就是在利乏音谷极北的边界;
Sai kuma ta gangara zuwa Kwarin Ben Hinnom a gangaren kudancin birnin Yebusiyawa (wato, Urushalima). Daga can ta haura zuwa kan tudun a yammancin Kwarin Hinnom, a arewancin ƙarshen Kwarin Refayim.
9 又从山顶延到尼弗多亚的水源,通到以弗 山的城邑,又延到巴拉(巴拉就是基列·耶琳);
Daga kan tudun, iyakar ta nufi maɓulɓular ruwa na Neftowa, ta ɓullo a garuruwan da suke a Dutsen Efron, ta gangara zuwa Ba’ala (wato, Kiriyat Yeyarim).
10 又从巴拉往西绕到西珥山,接连到耶琳山的北边(耶琳就是基撒 );又下到伯·示麦过亭纳,
Sa’an nan ta karkata yamma daga Ba’ala zuwa Dutsen Seyir, ta wuce ta gangaren Dutsen Yeyarim (wato, Kesalon), ta ci gaba zuwa Bet-Shemesh, ta bi zuwa Timna.
11 通到以革伦北边,延到施基 ,接连到巴拉山;又通到雅比聂,直通到海为止。
Ta wuce zuwa gangaren arewancin Ekron, ta juya zuwa Shikkeron, ta wuce zuwa Dutsen Ba’ala, ta kai Yabneyel, iyakarta ta ƙare a teku.
12 西界就是大海和靠近大海之地。这是犹大人按着宗族所得之地四围的交界。
Bakin Bahar Rum nan ne iyakar yammanci. Wannan ita ce iyakar da ta kewaye jama’ar Yahuda bisa ga iyalansu.
13 约书亚照耶和华所吩咐的,将犹大人中的一段地,就是基列·亚巴,分给耶孚尼的儿子迦勒。亚巴是亚衲族的始祖(基列·亚巴就是希伯 )。
Yoshuwa ya ba Kaleb ɗan Yefunne wuri a Yahuda, Kiriyat Arba, wato, Hebron, bisa ga umarnin Ubangiji. (Arba shi ne mahaifin Anak.)
14 迦勒就从那里赶出亚衲族的三个族长,就是示筛、亚希幔、挞买;
Daga can sai Kaleb ya kori’ya’yan Anak, maza su uku daga Hebron, wato, Sheshai, Ahiman da Talmai.
15 又从那里上去,攻击底璧的居民。(这底璧从前名叫基列·西弗。)
Daga can ya nufi Debir ya yi yaƙi da mutanen da suke zama a can (Dā sunan Debir, Kiriyat Sefer ne).
16 迦勒说:“谁能攻打基列·西弗将城夺取,我就把我女儿押撒给他为妻。”
Kaleb ya ce, “Zan ba da’yata Aksa aure ga wanda zai ci Kiriyat Sefer da yaƙi.”
17 迦勒兄弟基纳斯的儿子俄陀聂夺取了那城,迦勒就把女儿押撒给他为妻。
Otniyel ɗan Kenaz, ɗan’uwan Kaleb, ya ci Kiriyat Sefer da yaƙi; saboda haka Kaleb ya ba wa Aksa’yarsa, ya kuwa aure ta.
18 押撒过门的时候,劝丈夫向她父亲求一块田,押撒一下驴,迦勒问她说:“你要什么?”
Wata rana da ta zo wurin Otniyel, sai ya zuga ta ta roƙi mahaifinta fili. Da ta sauka daga kan jakinta sai Kaleb ya tambaye ta ya ce, “Me kike so in yi miki?”
19 她说:“求你赐福给我,你既将我安置在南地,求你也给我水泉。”她父亲就把上泉下泉赐给她。
Ta amsa ta ce, “Ka yi mini alheri na musamman, tun da ka ba ni wuri a Negeb, ina roƙonka, ka ba ni maɓulɓulan ruwa.” Kaleb kuwa ya ba ta maɓulɓulan ruwa na tuddai da na kwari.
Wannan shi ne gādon kabilar Yahuda bisa ga iyalansu.
21 犹大支派尽南边的城邑,与以东交界相近的,就是甲薛、以得、雅姑珥、
Garuruwan kabilar Yahuda da suke kudu cikin Negeb zuwa iyakar Edom su ne. Kabzeyel, Eder, Yagur,
25 夏琐·哈大他、加略·希斯 (加略·希斯 就是夏琐)、
Hazor-Hadatta, Keriyot Hezron (wato, Hazor),
Hazar Gadda, Heshmon, Bet-Felet,
Hazar Shuwal, Beyersheba, Biziyotiya,
Ziklag, Madmanna, Sansanna,
32 利巴勿、实忻、亚因、临门,共二十九座城,还有属城的村庄。
Lebayot, Shilhim, Ayin, Rimmon, jimillarsu, garuruwa da ƙauyukansu duka ashirin da tara ne.
Biranen da suke a filayen kwari su ne, Eshtawol, Zora; Ashna,
Zanowa, En Gannim, Taffuwa, Enam,
Yarmut, Adullam, Soko, Azeka,
36 沙拉音、亚底他音、基底拉、基底罗他音,共十四座城,还有属城的村庄。
Sha’arayim, Aditayim, Gedera (Gederotayim ke nan). Garuruwa goma sha huɗu ke nan da ƙauyukansu.
Zenan, Hadasha, Migdal Gad,
Dileyan, Mizfa, Yokteyel,
41 基低罗、伯·大衮、拿玛、玛基大,共十六座城,还有属城的村庄。
Gederot, Bet-Dagon, Na’ama, Makkeda, garuruwa goma sha shida ke nan da ƙauyukansu.
44 基伊拉、亚革悉、玛利沙,共九座城,还有属城的村庄。
Keyila, Akzib, Maresha, garuruwa tara ke nan da ƙauyukansu.
Ekron da ƙauyukan da suke kewaye da ita;
46 从以革伦直到海,一切靠近亚实突之地,并属其地的村庄。
yammancin Ekron da dukan garuruwa da ƙauyukan da suke kusa da Ashdod.
47 亚实突和属亚实突的镇市村庄;迦萨和属迦萨的镇市村庄;直到埃及小河,并大海和靠近大海之地。
Ashdod da garuruwa da kuma ƙauyukan da suke kewaye da ita, Gaza da garuruwanta da ƙauyukanta har zuwa Rafin Masar da kuma Bahar Rum.
Birane na cikin ƙasar tuddai kuwa, su ne, Shamir, Yattir, Soko,
Danna, Kiriyat Sanna (wato, Debir),
51 歌珊、何伦、基罗,共十一座城,还有属城的村庄。
Goshen, Holon, Gilo, garuruwa goma sha ɗaya ke nan da ƙauyukansu.
Yanum, Bet-Taffuwa, Afeka,
54 宏他、基列·亚巴(基列·亚巴就是希伯 )、洗珥,共九座城,还有属城的村庄。
Humta, Kiriyat Arba (wato, Hebron) da Ziyor, garuruwa tara ke nan da ƙauyukansu.
Mawon, Karmel, Zif, Yutta
Yezireyel, Yokdeyam, Zanowa,
57 该隐、基比亚、亭纳,共十座城,还有属城的村庄。
Kayin, Gibeya, Timna, garuruwa goma ke nan da ƙauyukansu.
59 玛腊、伯·亚诺、伊勒提君,共六座城,还有属城的村庄。
Ma’arat, Bet-Anot, Eltekon, garuruwa shida ke nan da ƙauyukansu.
60 又有基列·巴力(基列·巴力就是基列·耶琳)、拉巴,共两座城,还有属城的村庄。
Kiriyat Ba’al (wato, Kiriyat Yeyarim) da Rabba, garuruwa biyu ke nan da ƙauyukansu.
Biranen da suke a jeji kuwa su ne, Bet-Araba, Middin, Sekaka,
62 匿珊、盐城、隐·基底,共六座城,还有属城的村庄。
Nibshan, Birnin gishiri da En Gedi, garuruwa shida ke nan da ƙauyukansu.
63 至于住耶路撒冷的耶布斯人,犹大人不能把他们赶出去,耶布斯人却在耶路撒冷与犹大人同住,直到今日。
Kabilar Yahuda kuwa ba su iya korar Yebusiyawa waɗanda suke zama cikin Urushalima ba; har wa yau Yebusiyawa suna nan zaune tare da mutanen Yahuda.