< 希伯来书 1 >
A zamanin da, Allah ya yi wa kakanin kakanninmu magana ta hanyoyi ma su yawa iri iri, ta bakin annabawa.
2 就在这末世借着他儿子晓谕我们;又早已立他为承受万有的,也曾借着他创造诸世界。 (aiōn )
Amma a zamanin nan na karshe, ya yi mana magana ta wurin Dansa, wanda ya sa magajin kome, wanda ta wurinsa ya halicci duniya. (aiōn )
3 他是 神荣耀所发的光辉,是 神本体的真像,常用他权能的命令托住万有。他洗净了人的罪,就坐在高天至大者的右边。
Shi ne hasken daukakar Allah, ainihin kamanin zatinsa. Ya na rike da dukkan abubuwa ta ikon kalmarsa. Bayan da ya tsarkake zunubanmu, sai ya zauna a hannun dama na madaukaki a can sama.
4 他所承受的名,既比天使的名更尊贵,就远超过天使。
Ta haka ya ke da fifiko a kan mala'iku, kamar yadda sunansa da ya gada yake da fifiko nesa a kan nasu.
5 所有的天使, 神从来对哪一个说: 你是我的儿子, 我今日生你? 又指着哪一个说: 我要作他的父, 他要作我的子?
Domin kuwa wanene a cikin mala'iku Allah ya taba cewa, “Kai Da na ne, yau na zama Uba a gare ka?'' kuma, “Zan kasance Uba a gareshi, shi kuma, zai kasance Da a gare ni?''
6 再者, 神使长子到世上来的时候,就说: 神的使者都要拜他。
Kuma, da Allah ya kawo magaji a duniya, sai ya ce, “Dukan mala'ikun Allah su yi masa sujada.”
7 论到使者,又说: 神以风为使者, 以火焰为仆役;
A game da mala'iku kuma sai ya ce, “yakan mai da mala'ikunsa ruhohi, masu hidimarsa kuma harsunan wuta.
8 论到子却说: 神啊,你的宝座是永永远远的; 你的国权是正直的。 (aiōn )
A game da Dan, ya ce “kursiyinka, ya Allah, na har abada abadin ne. Sandar sarautarka sanda ce ta tsantsar gaskiya. (aiōn )
9 你喜爱公义,恨恶罪恶; 所以 神,就是你的 神,用喜乐油膏你, 胜过膏你的同伴;
Ka kaunaci aikin adalci, ka ki aikin sabo. Saboda haka Allah, wato Allahnka, ya shafe ka da man farin ciki fiye da tsararrakinka.”
10 又说:主啊,你起初立了地的根基; 天也是你手所造的。
“Tun farko, Ubangiji, kai ne ka hallici duniya. Sammai kuma aikin hannayenka ne.
11 天地都要灭没,你却要长存。 天地都要像衣服渐渐旧了;
Za su hallaka, amma kai madawwami ne. Duk za su tsufa kamar tufafi.
12 你要将天地卷起来,像一件外衣, 天地就都改变了。 惟有你永不改变; 你的年数没有穷尽。
Za ka nade su kamar mayafi, za su kuma sauya, amma kai kana nan ba sakewa, Har abada shekarunka ba za su kare ba.”
13 所有的天使, 神从来对哪一个说: 你坐在我的右边, 等我使你仇敌作你的脚凳?
Amma wanene a cikin mala'ikun Allah ya taba cewa, “Zauna a hannun dama na, sai na sa makiyanka a karkashin kafafunka?''
14 天使岂不都是服役的灵、奉差遣为那将要承受救恩的人效力吗?
Ashe, ba dukkan mala'iku bane ruhohi, wadanda Allah yakan aika, don su yi wa wadanda za su gaji ceto hidima?