< 创世记 10 >
1 挪亚的儿子闪、含、雅弗的后代记在下面。洪水以后,他们都生了儿子。
Wannan shi ne labarin Shem, Ham da Yafet,’ya’yan Nuhu maza, waɗanda su ma sun haifi’ya’ya maza bayan ambaliyar.
2 雅弗的儿子是歌篾、玛各、玛代、雅完、土巴、米设、提拉。
’Ya’yan Yafet maza su ne, Gomer, Magog, Madai da Yaban, Tubal, Meshek, da kuma Tiras.
’Ya’yan Gomer maza su ne, Ashkenaz, Rifat, da Togarma.
’Ya’yan maza Yaban su ne, Elisha, Tarshish, Kittim da Rodanim.
5 这些人的后裔将各国的地土、海岛分开居住,各随各的方言、宗族立国。
(Daga waɗannan mutane ne masu zama a bakin teku suka bazu zuwa cikin ƙasashensu da kuma cikin al’ummansu, kowanne da yarensa.)
’Ya’yan Ham maza su ne, Kush, Masar, Fut, da Kan’ana.
7 古实的儿子是西巴、哈腓拉、撒弗他、拉玛、撒弗提迦。拉玛的儿子是示巴、底但。
’Ya’yan Kush maza su ne, Seba, Hawila, Sabta, Ra’ama da Sabteka.’Ya’yan Ra’ama maza kuwa su ne, Sheba da Dedan.
Kush shi ne mahaifin Nimrod wanda ya yi girma ya zama jarumin yaƙi a duniya.
9 他在耶和华面前是个英勇的猎户,所以俗语说:“像宁录在耶和华面前是个英勇的猎户。”
Shi babban maharbi ne a gaban Ubangiji. Shi ya sa akan ce, kamar Nimrod babban maharbi a gaban Ubangiji.
10 他国的起头是巴别、以力、亚甲、甲尼,都在示拿地。
Cibiyoyin mulkinsa na farko su ne Babilon, Erek, Akkad, da Kalne a cikin Shinar.
11 他从那地出来往亚述去,建造尼尼微、利河伯、迦拉,
Daga wannan ƙasa, sai ya tafi Assuriya, inda ya gina Ninebe, Rehobot Ir, Kala
da Resen, wadda take tsakanin Ninebe da Kala; wanda yake babban birni.
13 麦西生路低人、亚拿米人、利哈比人、拿弗土希人、
Mizrayim shi ne mahaifin Ludiyawa, Anamawa, Lehabiyawa, Naftuhiyawa,
14 帕斯鲁细人、迦斯路希人、迦斐托人;从迦斐托出来的有非利士人。
Fetrusiyawa, da Kasluhiyawa (inda Filistiyawa suka fito) da kuma Kaftorawa.
Kan’ana shi ne mahaifin, Sidon ɗan farinsa, da na Hittiyawa,
Yebusiyawa, Amoriyawa, Girgashiyawa,
Hiwiyawa, Arkiyawa, Siniyawa,
18 亚瓦底人、洗玛利人、哈马人,后来迦南的诸族分散了。
Arbadiyawa, Zemarawa, da Hamawa. Daga baya zuriyar Kan’aniyawa suka yaɗu
19 迦南的境界是从西顿向基拉耳的路上,直到迦萨,又向所多玛、蛾摩拉、押玛、洗扁的路上,直到拉沙。
har iyakar Kan’ana ta kai Sidon ta wajen Gerar har zuwa Gaza, sa’an nan ta milla zuwa Sodom, Gomorra, Adma da Zeboyim, har zuwa Lasha.
20 这就是含的后裔,各随他们的宗族、方言,所住的地土、邦国。
Waɗannan su ne’ya’yan Ham maza bisa ga zuriyarsu da yarurrukansu, cikin ƙasashensu da kuma al’ummominsu.
21 雅弗的哥哥闪,是希伯子孙之祖,他也生了儿子。
Aka kuma haifa wa Shem, wan Yafet,’ya’ya maza. Shem shi ne kakan’ya’yan Eber duka.
’Ya’yan Shem maza su ne, Elam, Asshur, Arfakshad, Lud da Aram.
’Ya’yan Aram maza su ne, Uz, Hul, Geter da Mash.
Arfakshad ne mahaifin Shela. Shela kuma shi ne mahaifin Eber.
25 希伯生了两个儿子,一个名叫法勒,因为那时人就分地居住;法勒的兄弟名叫约坍。
Aka haifa wa Eber’ya’ya maza biyu. Aka ba wa ɗaya suna Feleg, gama a zamaninsa ne aka raba duniya; aka kuma sa wa ɗan’uwansa suna Yoktan.
Yoktan shi ne mahaifin, Almodad, Shelef, Hazarmawet, Yera,
Ofir, Hawila da Yobab. Dukan waɗannan’ya’yan Yoktan maza ne.
Yankin da suka zauna ya miƙe daga Mesha zuwa wajen Sefar a gabashin ƙasar tudu.
31 这就是闪的子孙,各随他们的宗族、方言,所住的地土、邦国。
Waɗannan su ne’ya’yan Shem maza bisa ga zuriyarsu da yarurrukansu, cikin ƙasashensu da kuma al’ummominsu.
32 这些都是挪亚三个儿子的宗族,各随他们的支派立国。洪水以后,他们在地上分为邦国。
Waɗannan su ne zuriyar’ya’yan Nuhu maza bisa ga jerin zuriyarsu cikin al’ummominsu. Daga waɗannan ne al’ummomi suka bazu ko’ina a duniya bayan ambaliya.