< 帖撒罗尼迦后书 1 >
1 保罗、西拉、提摩太写信给帖撒罗尼迦、在 神—我们的父与主耶稣基督里的教会。
Bulus da Silbanus da Timoti, zuwa ga ikilisiyar Tasolonika cikin Allah Ubanmu da Ubangiji Yesu Almasihu.
Bari alheri ya kasance tare da ku da salama daga Allah Ubanmu da Ubangijinmu Yesu Almasihu.
3 弟兄们,我们该为你们常常感谢 神,这本是合宜的;因你们的信心格外增长,并且你们众人彼此相爱的心也都充足。
Lallai ne mu godewa Allah kulluyaumin domin ku, yan'uwa. Domin hakan dai dai ne, saboda bangaskiyarku ta karu sosai, kuma kaunar junanku tana karuwa.
4 甚至我们在 神的各教会里为你们夸口,都因你们在所受的一切逼迫患难中,仍旧存忍耐和信心。
Mu da kanmu muna fahariya da ku a ikilisiyoyin Allah. Muna maganar hakurinku da bangaskiyarku a cikin dukkan tsananin da kuke fuskanta. Muna maganar kuncin da kuke jimrewa.
5 这正是 神公义判断的明证,叫你们可算配得 神的国;你们就是为这国受苦。
Wannan itace alamar shari'ar Allah ta adalci. Sakamakon haka shine za a dauke ku cancantattu na mulkin Allah wanda kuke wahala dominsa.
6 神既是公义的,就必将患难报应那加患难给你们的人,
Adalci ne ga Allah ya mayar da kunci ga wadanda suke kuntata maku,
7 也必使你们这受患难的人与我们同得平安。那时,主耶稣同他有能力的天使从天上在火焰中显现,
ya kuma baku hutu ku dake shan wuya tare da mu. Zai yi haka ne a bayyanar Ubangiji Yesu daga sama da Mala'ikun ikonsa.
8 要报应那不认识 神和那不听从我主耶稣福音的人。
A cikin wuta mai huruwa zai dau fansa bisa wadanda basu san Allah ba da wadanda basu karbi bisharar Ubangijinmu Yesu almasihu ba.
9 他们要受刑罚,就是永远沉沦,离开主的面和他权能的荣光。 (aiōnios )
Za su sha azaba ta hallaka har abada daga fuskar Ubangiji da kuma daukakar ikonsa. (aiōnios )
10 这正是主降临、要在他圣徒的身上得荣耀、又在一切信的人身上显为希奇的那日子。我们对你们作的见证,你们也信了。
Zai yi wannan lokacin da yazo a wannan rana don jama'arsa su daukaka shi, kuma ya zama abin mamaki ga dukkan wadanda suka bada gaskiya. Domin kun gaskata shaidarmu a gare ku.
11 因此,我们常为你们祷告,愿我们的 神看你们配得过所蒙的召,又用大能成就你们一切所羡慕的良善和一切因信心所做的工夫,
Saboda wannan muke addu'a kullum domin ku. Muna addu'a domin Allahnmu ya sa ku cancanci kiran ku. Muna addu'a ya biya ku muradin ku na yin nagarta da dukkan wani aikin bangaskiya da kuma iko.
12 叫我们主耶稣的名在你们身上得荣耀,你们也在他身上得荣耀,都照着我们的 神并主耶稣基督的恩。
Muna addu'a haka domin sunan Ubangijinmu Yesu ya sami daukaka daga gare ku. Addu'armu itace ya daukaka ku, saboda alherin Allahnmu da Ubangijinmu Yesu Almasihu.