< 撒母耳记下 14 >

1 洗鲁雅的儿子约押,知道王心里想念押沙龙,
Yowab, ɗan Zeruhiya ya gane cewa zuriyar sarki ta koma ga Absalom.
2 就打发人往提哥亚去,从那里叫了一个聪明的妇人来,对她说:“请你假装居丧的,穿上孝衣,不要用膏抹身,要装作为死者许久悲哀的妇人;
Saboda haka Yowab ya aiki wani zuwa Tekowa, ya sa a zo da wata mace mai hikima. Ya ce mata, “Ki yi kamar kina makoki. Ki sa rigar makoki, kada kuwa ki shafa mai. Ki yi kamar macen da ta yi kwanaki da yawa, tana makokin matattu.
3 进去见王,对王如此如此说。”于是约押将当说的话教导了妇人。
Sa’an nan ki je wurin sarki, ki ce masa haka.” Sai Yowab ya faɗa mata duk abin da za tă faɗa.
4 提哥亚妇人到王面前,伏地叩拜,说:“王啊,求你拯救!”
Da macen da ta fito daga Tekowa ta je wajen sarki, sai ta rusuna har ƙasa don bangirma, sai ta ce, “Ka taimake ni, ya sarki!”
5 王问她说:“你有什么事呢?”回答说:“婢女实在是寡妇,我丈夫死了。
Sarki ya ce mata, “Mece ce matsalarki?” Sai ta ce, “Tabbatacce, ni gwauruwa ce; mijina ya mutu.
6 我有两个儿子,一日在田间争斗,没有人解劝,这个就打死那个。
Baiwarka tana da’ya’ya maza biyu. Suka yi faɗa da juna a fili, kuma ba wanda yake can don yă raba su. Ɗayan ya bugi ɗayan, ya kashe shi.
7 现在全家的人都起来攻击婢女,说:‘你将那打死兄弟的交出来,我们好治死他,偿他打死兄弟的命,灭绝那承受家业的。’这样,他们要将我剩下的炭火灭尽,不与我丈夫留名留后在世上。”
To, ga duk iyali sun hau kan baiwarka, suna cewa, ‘Ki ba mu ɗayan da ya kashe ɗan’uwansa mu kashe don ran ɗan’uwansa da ya kashe; sa’an nan za mu hallaka magājin shi ma.’ Za su kashe garwashin wuta mai ci da nake da shi kaɗai, su bar mijina ba suna, ba jika, a duniya.”
8 王对妇人说:“你回家去吧!我必为你下令。”
Sarki ya ce wa macen, “Koma gida, zan ba da umarni a madadinki.”
9 提哥亚妇人又对王说:“我主我王,愿这罪归我和我父家,与王和王的位无干。”
Amma macen da ta fito daga Tekowa ta ce, “Ranka yă daɗe, sarki! Bari alhakin shari’arka yă kasance a kaina da gidan mahaifina, kai sarki da gidan mulkinka, ba ku da laifi a ciki.”
10 王说:“凡难为你的,你就带他到我这里来,他必不再搅扰你。”
Sai sarki ya ce, “In wani ya yi miki magana, ki kawo shi wurina, ba zai kuwa ƙara damunki ba.”
11 妇人说:“愿王记念耶和华—你的 神,不许报血仇的人施行灭绝,恐怕他们灭绝我的儿子。”王说:“我指着永生的耶和华起誓:你的儿子连一根头发也不致落在地上。”
Sai ta ce, “To, bari sarki yă rantse da Ubangiji Allahnsa don yă hana mai ramako yin ƙarin hallakawar da aka yi, domin kada a hallaka ɗana.” Sai ya ce, “Muddin Ubangiji yana a raye, babu gashi guda na ɗanki da zai fāɗi ƙasa.”
12 妇人说:“求我主我王容婢女再说一句话。”王说:“你说吧!”
Sai matar ta ce, “Bari baiwarka ta ƙara yin magana sau ɗayan nan wa ranka yă daɗe.” Ya ce, “Ki faɗa.”
13 妇人说:“王为何也起意要害 神的民呢?王不使那逃亡的人回来,王的这话就是自证己错了!
Matar ta ce, “To, don me ka yi wa mutanen Allah irin wannan abu? Sa’ad da sarki ya ce haka, ashe, ba ka hukunta kanka ke nan ba, tun da yake sarki bai yarda ɗansa yă komo gida ba?
14 我们都是必死的,如同水泼在地上,不能收回。 神并不夺取人的性命,乃设法使逃亡的人不致成为赶出、回不来的。
Kamar ruwan da ya zuba a ƙasa, wanda ba a iya kwasa, haka dole mu mutu. Amma Allah ba ya ɗaukan rai; a maimako, yakan ƙirƙiro hanyoyi domin mutumin da aka kora kada yă kasance yasasshe daga gare shi.
15 我来将这话告诉我主我王,是因百姓使我惧怕。婢女想,不如将这话告诉王,或者王成就婢女所求的。
“Yanzu ga shi na zo don in faɗa wannan wa ranka yă daɗe sarki, don mutane sun tsorata ni. Baiwarka ta yi tunani ta ce, ‘Zan yi magana wa sarki; wataƙila yă yi abin da baiwarsa ta roƙa.
16 人要将我和我儿子从 神的地业上一同除灭,王必应允救我脱离他的手。
Wataƙila sarki zai yarda yă ceci baiwarsa daga hannun mutumin nan da yake ƙoƙari yă hallaka ni da ɗana daga gādon da Allah ya ba mu.’
17 婢女又想,我主我王的话必安慰我;因为我主我王能辨别是非,如同 神的使者一样。惟愿耶和华—你的 神与你同在!”
“Yanzu kuwa baiwarka tana cewa, ‘Bari magana ranka yă daɗe sarki yă ba ni hutu, gama ranka yă daɗe sarki yana kama da mala’ikan Allah cikin rarrabe nagarta da mugunta. Bari Ubangiji Allahnka yă kasance tare da kai.’”
18 王对妇人说:“我要问你一句话,你一点不要瞒我。”妇人说:“愿我主我王说。”
Sai sarki ya ce wa matar, “Kada ki ɓoye mini kome daga abin da zan tambaye ki.” Matar ta ce, “Bari ranka yă daɗe sarki yă yi tambaya.”
19 王说:“你这些话莫非是约押的主意吗?”妇人说:“我敢在我主我王面前起誓:王的话正对,不偏左右,是王的仆人约押吩咐我的,这些话是他教导我的。
Sarki ya ce, “Anya, babu hannun Yowab a cikin dukan wannan?” Matar ta ce, “Muddin kana a raye, ranka yă daɗe sarki, ba wanda zai juya dama ko hagu daga wani abin da ranka yă daɗe sarki ya faɗa. I, bawanka Yowab ne ya umarce ni in yi wannan, shi ne kuma ya sa kalmomin nan a bakin baiwarka.
20 王的仆人约押如此行,为要挽回这事。我主的智慧却如 神使者的智慧,能知世上一切事。”
Bawanka Yowab ne ya yi haka don yă daidaita al’amura. Ranka yă daɗe yana da hikima iri ta mala’ikan Allah, ya san dukan kome da yake faruwa a ƙasar.”
21 王对约押说:“我应允你这事。你可以去,把那少年人押沙龙带回来。”
Sarki ya ce wa Yowab, “To, da kyau, zan yi haka. Je ka, ka dawo da saurayin nan Absalom.”
22 约押就面伏于地叩拜,祝谢于王,又说:“王既应允仆人所求的,仆人今日知道在我主我王眼前蒙恩了。”
Yowab ya rusuna har ƙasa don bangirma, ya kuma yi wa sarki kyakkyawar fata. Yowab ya ce, “Yau, bawanka ya sani ya sami tagomashi a gare ka, ranka yă daɗe sarki, gama sarki ya ji roƙon bawansa.”
23 于是约押起身往基述去,将押沙龙带回耶路撒冷。
Sa’an nan Yowab ya tafi Geshur ya dawo da Absalom Urushalima.
24 王说:“使他回自己家里去,不要见我的面。”押沙龙就回自己家里去,没有见王的面。
Amma sarki ya ce, “Yă tafi gidansa; kada yă zo yă gan ni.” Saboda haka Absalom ya tafi gidansa, bai kuwa je ganin sarki ba.
25 以色列全地之中,无人像押沙龙那样俊美,得人的称赞,从脚底到头顶毫无瑕疵。
A cikin dukan Isra’ila babu wanda ake yabon kyansa kamar Absalom. Tun daga kansa har zuwa tafin ƙafansa babu tabo a jikinsa.
26 他的头发甚重,每到年底剪发一次;所剪下来的,按王的平称一称,重二百舍客勒。
A duk sa’ad da ya aske gashin kansa (yakan aske kansa lokaci-lokaci sa’ad da ya yi masa nauyi) yakan auna shi, nauyin gashin kuwa yakan kai wajen shekel ɗari biyu a ma’aunin da ake awo.
27 押沙龙生了三个儿子,一个女儿。女儿名叫她玛,是个容貌俊美的女子。
Aka haifa wa Absalom’ya’ya uku maza da’ya mace guda. Sunanta Tamar, ta kuwa zama kyakkyawan mace ƙwarai.
28 押沙龙住在耶路撒冷足有二年,没有见王的面。
Absalom ya zauna a Urushalima shekara biyu amma ba tare da ganin fuskar sarki ba.
29 押沙龙打发人去叫约押来,要托他去见王,约押却不肯来。第二次打发人去叫他,他仍不肯来。
Sai Absalom ya aika a kira masa Yowab don yă aike shi wurin sarki, amma Yowab ya ƙi zuwa. Saboda haka ya sāke aika sau na biyu, amma ya ƙi yă zo.
30 所以押沙龙对仆人说:“你们看,约押有一块田,与我的田相近,其中有大麦,你们去放火烧了。”押沙龙的仆人就去放火烧了那田。
Sai ya ce wa bayinsa, “Duba, gonar Yowab tana gab da tawa, kuma yana da sha’ir a can. Ku je ku sa mata wuta.” Sai bayin Absalom suka sa wa gonar wuta.
31 于是约押起来,到了押沙龙家里,问他说:“你的仆人为何放火烧了我的田呢?”
Sa’an nan Yowab ya tafi gidan Absalom ya ce masa, “Me ya sa bayinka suka sa wa gonata wuta?”
32 押沙龙回答约押说:“我打发人去请你来,好托你去见王,替我说:‘我为何从基述回来呢?不如仍在那里。’现在要许我见王的面;我若有罪,任凭王杀我就是了。”
Absalom ya ce wa Yowab, “Kai, na aika, ‘Ka zo nan don in aike ka wurin sarki ka tambaya, “Me ya sa na dawo daga Geshur? Ai, ya fi mini a ce ina can har yanzu!”’ Yanzu kuwa, ina so in ga sarki, kuma idan na yi wani laifi, to, yă kashe ni.”
33 于是约押去见王,将这话奏告王,王便叫押沙龙来。押沙龙来见王,在王面前俯伏于地,王就与押沙龙亲嘴。
Saboda haka Yowab ya tafi wurin sarki ya gaya masa wannan. Sai sarki ya aika aka zo da Absalom, ya kuma rusuna da fuskarsa har ƙasa a gaban sarki. Sarki kuwa ya sumbaci Absalom.

< 撒母耳记下 14 >