< 历代志上 9 >

1 以色列人都按家谱计算,写在以色列诸王记上。犹大人因犯罪就被掳到巴比伦。
Haka aka lissafta dukan Isra’ila a tarihin zuriyoyi a littafin sarakunan Isra’ila. Aka kwasa mutanen Yahuda zuwa zaman bauta a Babilon domin rashin aminci.
2 先从巴比伦回来,住在自己地业城邑中的有以色列人、祭司、利未人、尼提宁的首领。
To, na farkon da aka sāke zaunar da su a mallakarsu a garuruwansu, su ne waɗansu Isra’ilawa, firistoci, Lawiyawa da kuma masu hidimar haikali.
3 住在耶路撒冷的有犹大人、便雅悯人、以法莲人、玛拿西人。
Waɗanda suke daga Yahuda, daga Benyamin, da kuma daga Efraim da Manasse waɗanda suka zauna a Urushalima su ne,
4 犹大儿子法勒斯的子孙中有乌太。乌太是亚米忽的儿子;亚米忽是暗利的儿子;暗利是音利的儿子;音利是巴尼的儿子。
Uttai ɗan Ammihud, ɗan Omri, ɗan Imri, ɗan Bani, zuriyar Ferez ɗan Yahuda.
5 示罗的子孙中有长子亚帅雅和他的众子。
Na mutanen Shilo kuwa su ne, Asahiya ɗan fari da’ya’yansa maza.
6 谢拉的子孙中有耶乌利和他的弟兄,共六百九十人。
Na mutanen Zera su ne, Yewuyel. Mutane daga Yahuda sun kai 690.
7 便雅悯人中有哈西努的曾孙、何达威雅的孙子、米书兰的儿子撒路,
Na Benyamin su ne, Sallu ɗan Meshullam, ɗan Hodawiya, ɗan Hassenuwa;
8 又有耶罗罕的儿子伊比尼雅,米基立的孙子、乌西的儿子以拉,伊比尼雅的曾孙、流珥的孙子、示法提雅的儿子米书兰,
Ibnehiya ɗan Yeroham; Ela ɗan Uzzi, ɗan Mikri; da Meshullam ɗan Shefatiya, ɗan Reyuwel, ɗan Ibniya.
9 和他们的族弟兄,按着家谱计算共有九百五十六名。这些人都是他们的族长。
Mutane daga Benyamin, kamar yadda aka lissafta zuriyarsu, sun kai 956. Dukan waɗannan mutane kawunan iyalansu ne.
10 祭司中有耶大雅、耶何雅立、雅斤,
Na firistoci su ne, Yedahiya; Yehoyarib; Yakin;
11 还有管理 神殿希勒家的儿子亚萨利雅。希勒家是米书兰的儿子;米书兰是撒督的儿子;撒督是米拉约的儿子;米拉约是亚希突的儿子。
Azariya ɗan Hilkiya, ɗan Meshullam, ɗan Zadok, ɗan Merahiyot, ɗan Ahitub, shugaban da yake lura da gidan Allah;
12 有玛基雅的曾孙、巴施户珥的孙子、耶罗罕的儿子亚大雅,又有亚第业的儿子玛赛;亚第业是雅希细拉的儿子;雅希细拉是米书兰的儿子;米书兰是米实利密的儿子;米实利密是音麦的儿子。
Adahiya ɗan Yeroham, ɗan Fashhur, ɗan Malkiya; da Ma’asai ɗan Adiyel, ɗan Yazera, ɗan Meshullam, ɗan Meshillemit, ɗan Immer.
13 他们和众弟兄都是族长,共有一千七百六十人,是善于做 神殿使用之工的。
Firistocin da suke kawunan iyalai, sun kai 1,760. Dukansu ƙwararru ne, masu hakkin hidima a cikin gidan Allah.
14 利未人米拉利的子孙中,有哈沙比雅的曾孙、押利甘的孙子、哈述的儿子示玛雅。
Na Lawiyawa su ne, Shemahiya ɗan Hasshub, ɗan Azrikam, ɗan Hashabiya, mutumin Merari;
15 有拔巴甲、黑勒施、迦拉,并亚萨的曾孙、细基利的孙子、米迦的儿子玛探雅,
Bakbakkar, Heresh, Galal da Mattaniya ɗan Mika, ɗan Zikri, ɗan Asaf;
16 又有耶杜顿的曾孙、迦拉的孙子、示玛雅的儿子俄巴底,还有以利加拿的孙子、亚撒的儿子比利家。他们都住在尼陀法人的村庄。
Obadiya ɗan Shemahiya, ɗan Galal, ɗan Yedutun; da Berekiya ɗan Asa, ɗan Elkana, wanda ya zauna a ƙauyukan Netofawa.
17 守门的是沙龙、亚谷、达们、亚希幔,和他们的弟兄;沙龙为长。
Matsaran ƙofofi su ne, Shallum, Akkub, Talmon, Ahiman da’yan’uwansu. Shallum ne babbansu
18 从前这些人看守朝东的王门,如今是利未营中守门的。
da aka ajiye a Ƙofar Sarki a gabas, har zuwa wannan lokaci. Waɗannan su ne matsaran ƙofofi na sansanin Lawiyawa.
19 可拉的曾孙、以比雅撒的孙子、可利的儿子沙龙,和他的族弟兄可拉人都管理使用之工,并守会幕的门。他们的祖宗曾管理耶和华的营盘,又把守营门。
Shallum ɗan Kore, ɗan Ebiyasaf, ɗan Kora, da’yan’uwansa matsaran ƙofofi daga iyalin (mutanen Kohat) su suke da hakkin tsaron madogaran ƙofar Tenti kamar dai yadda kakanninsu suka kasance da hakkin tsaron mashigin mazaunin Ubangiji.
20 从前以利亚撒的儿子非尼哈管理他们,耶和华也与他同在。
A dā Finehas ɗan Eleyazar ne yake lura da matsaran, kuma Ubangiji ya kasance tare da shi.
21 米施利米雅的儿子撒迦利雅是看守会幕之门的。
Zakariya ɗan Meshelemiya shi ne mai tsaro a mashigin Tentin Sujada.
22 被选守门的人共有二百一十二名。他们在自己的村庄,按着家谱计算,是大卫和先见撒母耳所派当这紧要职任的。
Duka-duka, waɗanda aka zaɓa don su zama matsaran madogaran ƙofa sun kai 212. Aka rubuta su zuriya-zuriya a ƙauyukansu. Dawuda da Sama’ila mai duba ne suka sa matsaran a wurarensu na aminci.
23 他们和他们的子孙按着班次看守耶和华殿的门,就是会幕的门。
Su da zuriyarsu, su suke lura da tsaron ƙofofin gidan Ubangiji, gidan da ake kira Tenti.
24 在东西南北,四方都有守门的。
Matsaran suna a kusurwoyi huɗu, gabas, yamma, arewa da kudu.
25 他们的族弟兄住在村庄,每七日来与他们换班。
’Yan’uwansu a ƙauyukansu sukan zo lokaci, lokaci su yi ayyukansu kwana bakwai, bakwai.
26 这四个门领都是利未人,各有紧要的职任,看守 神殿的仓库。
Amma manyan matsara huɗu, waɗanda suke Lawiyawa, an danƙa musu hakkin lura da ɗakuna da kuma wuraren ajiya a gidan Allah.
27 他们住在 神殿的四围,是因委托他们守殿,要每日早晨开门。
Sukan kwana a kewayen gidan Allah, domin dole su tsare shi; kuma su suke lura da mabuɗi don buɗewa a kowace safiya.
28 利未人中有管理使用器皿的,按着数目拿出拿入;
Waɗansunsu su ne suke lura da kayayyakin da ake amfani da su a hidimar haikali; sukan ƙirga su sa’ad da ake shigar da su da sa’ad da ake fitar da su.
29 又有人管理器具和圣所的器皿,并细面、酒、油、乳香、香料。
An sa waɗansu su lura da kayayyakin da kuma dukan waɗansu kayan wuri mai tsarki, da kuma gari da ruwan inabi, da mai, turare da kuma kayan yaji.
30 祭司中有人用香料做膏油。
Amma waɗansu firistoci ne suke harhaɗa kayan yajin.
31 利未人玛他提雅是可拉族沙龙的长子,他紧要的职任是管理盘中烤的物。
Wani Balawe mai suna Mattitiya, ɗan farin Shallum mutumin Kora ne aka danƙa masa hakkin toya burodin miƙawa.
32 他们族弟兄哥辖子孙中,有管理陈设饼的,每安息日预备摆列。
Waɗansu’yan’uwansu Kohatawa ne suke lura da shiryawa burodin da ake kaiwa a tebur a kowane Asabbaci.
33 歌唱的有利未人的族长,住在属殿的房屋,昼夜供职,不做别样的工。
Waɗanda suke mawaƙa, kawunan iyalan Lawiyawa, sukan zauna a ɗakunan haikali kuma ba sa yin waɗansu ayyuka domin su suke da hakkin aiki dare da rana.
34 以上都是利未人著名的族长,住在耶路撒冷。
Dukan waɗannan su ne kawunan iyalan Lawiyawa, manya kamar yadda aka lissafta su a zuriyarsu, kuma suna zama a Urushalima.
35 在基遍住的有基遍的父亲耶利。他的妻名叫玛迦;
Yehiyel mahaifin Gibeyon ya zauna a Gibeyon. Matarsa ita ce Ma’aka
36 他长子是亚伯顿。他又生苏珥、基士、巴力、尼珥、拿答、
ɗansa na fari kuwa shi ne Abdon, sai Zur, Kish, Ba’al, Ner, Nadab,
37 基多、亚希约、撒迦利雅、米基罗。
Gedor, Ahiyo, Zakariya da Miklot.
38 米基罗生示米暗。这些人和他们的弟兄在耶路撒冷对面居住。
Miklot shi ne mahaifin Shimeyam. Su ma sun zauna kusa da danginsu a Urushalima.
39 尼珥生基士;基士生扫罗;扫罗生约拿单、麦基舒亚、亚比拿达、伊施·巴力。
Ner shi mahaifin Kish, Kish mahaifin Shawulu, kuma Shawulu shi ne mahaifin Yonatan, Malki-Shuwa, Abinadab da Esh-Ba’al.
40 约拿单的儿子是米力·巴力;米力·巴力生米迦。
Ɗan Yonatan shi ne, Merib-Ba’al wanda shi ne mahaifin Mika.
41 米迦的儿子是毗敦、米勒、他利亚、亚哈斯。
’Ya’yan Mika maza su ne, Fiton, Melek, Tareya da Ahaz.
42 亚哈斯生雅拉;雅拉生亚拉篾、亚斯玛威、心利;心利生摩撒;
Ahaz shi ne mahaifin Yada, Yada shi ne mahaifin Alemet, Azmawet da Zimri, Zimri kuwa shi ne mahaifin Moza.
43 摩撒生比尼亚;比尼亚生利法雅;利法雅的儿子是以利亚萨;以利亚萨的儿子是亚悉。
Moza shi ne mahaifin Bineya; Refahiya, Eleyasa da kuma Azel.
44 亚悉有六个儿子,他们的名字是亚斯利干、波基路、以实玛利、示亚利雅、俄巴底雅、哈难。这都是亚悉的儿子。
Azel yana da’ya’ya maza shida, kuma ga sunayensu. Azrikam, Bokeru, Ishmayel, Sheyariya, Obadiya da Hanan. Waɗannan su ne’ya’yan Azel maza.

< 历代志上 9 >