< 羅馬書 6 >

1 那麼,我們可說什麼呢?我們要常留在罪惡中,好叫恩寵洋溢嗎?
Me kuwa zamu ce yanzu? Sai mu ci gaba da yin zunubi domin Alheri ya yawaita?
2 斷乎不可! 我們這些死於罪惡的人,如何還能在罪惡中生活呢?
Ba zai taba faruwa ba. 'Yaya za'ace mu da muka mutu cikin zunubi mu ci gaba da rayuwa cikin sa?
3 難道你們不知道:我們受過洗歸於基督耶穌的人,就是受洗歸於他的死亡嗎?
Ba ku san cewa duk wadanda aka yi masu baftisma cikin Almasihu Yesu an yi masu baftisma har ya zuwa mutuwarsa ne ba?
4 我們藉著洗禮已歸於死亡與祂同葬了,為的是基督怎樣藉著父的光榮,從死者中復活了,我們也怎樣在新生活中度生。
An kuwa binne mu tare da shi, ta wurin baftisma cikin mutuwarsa. Haka kuma ya kasance ne domin kamar yadda Almasihu ya tashi daga matattu cikin daukakar Uba. Sakamakon haka muma zamu yi tafiya cikin sabuwar rayuwa.
5 如果我們藉著同祂相似的死亡,已與祂結合,也要藉著同祂相似的復活與祂結合,
Domin kuwa idan muna tare dashi cikin kamannin mutuwarsa zamu kuwa zauna tare dashi har ga kamannin tashinsa.
6 因為我們知道,我們的舊人已與祂同釘在十字架上了,使那屬罪惡的自我消逝,好叫我們不再作罪惡的奴隸,
Mun kuma san cewa, an giciye wannan tsohon mutunmin nan namu tare dashi, domin a hallaka jikin zunubi. wanna kuwa ya kasance ne domin kada mu ci gaba da bautar zunubi.
7 因為已死的人,便脫離了罪惡。
Duk kuma wanda ya mutu an ambace shi a matayin adali akan zunubi.
8 所以,如果我們與基督同,我們相信也要祂同生,
Amma idan muka mutu tare da Almasihu, mun bada gaskiya zamu yi rayuwa tare dashi.
9 因為我們知道:基督既從死者中復活,就不再死亡;死亡不再統治祂了,
Muna da sanen cewa an tada Almasihu daga matattu, don haka kuwa ba matacce yake ba. Mutuwa kuma bata da iko a kansa.
10 因為祂死,是死於罪惡,僅僅一次;祂活,是活於天主。
Game da mutuwar da yayi ga zunubi yayi sau daya kuma domin dukka. Rayuwar da yake yi kuma yana yi wa Allah ne.
11 你們也要這樣看自己是死於罪惡,在基督耶穌內活於天主的人。
Don haka ku ma sai ku dauki kanku a matsayin matattu ga zunubi amma rayayyu ga Allah cikin Almasihu Yesu.
12 所以不要讓k你們必死的身體上為王,致令你們從祂的情慾,
Sabili da haka kada ku bar zunubi yayi mulki a cikin jikinku, har ku yi biyayya ga sha'awarsa.
13 也不要把你們的肢體交與罪惡,作不義的武器;但該將你們自己獻於天主,有如從死者中復活的人,將你們的肢體獻於天主,當作正義的武器:
Kada ku mika gabobin jikinku ga zunubi a matsayin kayan aikin rashin adalci. Amma ku mika kanku ga Allah rayayyu daga mutuwa. Ku kuma mika gabobin jikinku ga Allah a matsayin kayan aiki na adalci.
14 罪惡不應再統治你們,因為你們已不再法律權下,而是在恩寵權下。
kada ku ba zunubi dama yayi mulki a kanku, domin ba karkashin doka kuke ba, amma karkashin alheri kuke.
15 那麼,我們因為不在法律權下,而在恩寵權下,就可以犯罪嗎?絕對不可!
To sai me? Sai mu yi zunubi wai don ba a karkashin doka muke ba amma alheri. ba zai taba faruwa ba.
16 難道你們不知道:你們將自己獻給誰當奴隸,而服從他,就成了你們所服從者的奴隸,或作罪惡的奴隸,以致死亡;或作順命的奴隸,以得正義嗎?
Ba ku san cewa duk ga wanda kuka mika kanku a matsayin bayi, a gareshi ku bayi ne ba? Wannan fa gaskiya ne, ko dai ku bayi ne ga zunubi wanda kaiwa ga mutuwa ko kuma bayi ga biyayya wanda ke kaiwa ga adalci.
17 感謝天主,雖然你們曾作過罪惡的奴隸,現在你們卻從心裏聽從那傳給你們的教理規範,
Amma godiya ta tabbata ga Allah! domin da ku bayin zunubi ne, amma kun yi biyayya daga zuciyarku irin salon koyarwar da aka baku.
18 脫離罪惡,獲得了自由,作了正義的奴隸。
An 'yantar daku daga bautar zunubi, an kuma maishe ku bayin adalci.
19 為了你們本性的軟弱,我且按常情來說:你們在從前怎樣將你們的肢體當作奴隸,獻於不潔和不法,行不法的事;如今也要怎樣將你們的肢體當作奴隸,獻於正義,行聖善的事。
Ina magana da ku kamar mutum, domin kasawarku ta nama da jini. Kamar yadda kuka mika gabobin jikinku ga kazamta da miyagun ayyuka, haka ma yanzu ku mika gabobin jikinku a matsayin bayi na adalci.
20 當你們作罪惡的奴隸時,不受正義的束縛;
Domin a lokacin da kuke bayin zunubi, ku yantattu ne ga adalci.
21 但那時你們得了什麼效果?只是叫你們現在以些事為可恥,因為其結局就是死亡;
A wannan lokacin wanne amfani kuka samu na ayyukan da yanzu kuke jin kunyarsu? Domin kuwa sakamakon wadannan ayyuka shine mutuwa.
22 可是現在,你們脫離了罪惡,獲得了自由,作了天主的奴隸,你們所得的效果是使你們成聖,結局就是永生。 (aiōnios g166)
Amma yanzu da da aka yantar daku daga zunubi aka mai da ku bayin Allah, amfaninsa ku kuwa shine tsarkakewarku. Sakamakon kuwa shine rai na har abada. (aiōnios g166)
23 因為罪惡的薪俸是死亡,但是天主的恩賜是在我們的主基督耶穌內的永生。 (aiōnios g166)
Don kuwa sakamakon zunubi mutuwa ne. Amma kyautar Allah itace rai madauwami cikin Almasihu Yesu Ubangijinmu. (aiōnios g166)

< 羅馬書 6 >