< 羅馬書 5 >
1 我們既因信德成義,便是藉我們的主耶穌基督,與天主和好了。
Tun da shike mun sami barata, sabili da bangaskiya, mun sami salama tare da Allah ta wurin Yesu Almasihu.
2 藉著耶穌我們得因信德進入了現今所站立的這恩寵中,並因希望分天主的光榮而歡躍。
. Ta wurin sa kuma mun sami iso zuwa ga alheri inda muke tsayawa albarkacin bangaskiyarmu. Muna murna da gabagadin da Allah ya ba mu game da abin da zai faru, gabagadin da zamu dandana nan gaba cikin daukakar Allah.
3 不但如此,我們連在磨難中也歡躍,因為我們知道:磨難生忍耐,
Ba kuwa haka kadai ba, amma muna murna da shan wahalolinmu. Mun san cewa shan wuya na haifar da
Jimiri, Jimiri kuma na kawo amincewa, amincewa na kawo gabagadi game da abin da zai zo nan gaba.
5 望德不叫人蒙羞,因為天主的愛,藉著所賜與我們的聖神,已傾注在我們心中了。
Wannan gabagadi wato begen da muke da shi baya kunyatarwa, domin kuwa an kwarara mana kaunar Allah a cikin zuciyarmu ta wurin Ruhu Mai Tsarki, da aka ba mu.
6 當我們還在軟弱的時候,基督就在指定的時期為不虔敬的人死了。
Domin kuwa ko yayin da muke raunana, Almasihu ya mutu a lokacin da ke dai dai domin marasa ibada.
To ai kuwa yana da wuya kwarai wani mutum ya yarda ya mutu don mutumin kirki ma. Watakila, wani na iyayin kasada ya yarda ya mutu don nagarin mutum.
8 但是,基督在我們還是罪人的時候,就為我們死了,這證明了天主怎樣愛我們。
Amma Allah ya tabbatar mana da kaunarsa a gare mu, don kuwa tun muna masu zunubi, Almasihu ya mutu domin mu.
9 現在,我們既因祂的血而成義,我們更要藉著祂脫免天主的義怒,
Balle ma yanzu, da muka barata ta wurin jininsa, za mu sami tsira daga fushin Allah.
10 因為,假如我們還在為仇敵的時候,因著祂聖子的死得與天主和好了;那麼,在和好之後,我們一定更要因著祂的生命得救了。
Domin kuwa, in tun muna makiya, aka sulhunta mu da Allah ta wurin mutuwar Dansa, balle ma, yanzu da muka sami sulhu, zamu sami tsira ta wurin ransa.
11 不但如此,我們現今既藉著我們的主耶穌基督獲得了和好,也必藉著祂而歡躍於天主。
Bama haka kadai ba, amma muna murna a cikin Allah ta wurin Ubangijinmu Yesu Almasihu, wanda ta wurinsa ne muka sami wannan sulhu.
12 故此,就如罪惡藉著一人進入了世界,死亡藉著罪惡也進入了世界;這樣死亡就殃及了眾人,因為眾人都犯了罪,成義也是如此──
Saboda haka, kamar yadda ta wurin mutum daya zunubi ya shigo cikin duniya, ta haka mutuwa ta shigo ta dalilin zunubi.
13 沒有法律之前,罪惡已經在世界上;但因沒有法律,罪惡本不應算為罪惡。
Domin kuwa tun kafin a bada shari'a, zunubi na nan a duniya, amma ba' a lissafin zunubi in da ba shari'a.
14 但從亞當起,直到梅瑟,死亡卻作了王,連那些沒有像亞當一樣違法犯罪的人,也屬它權下:這亞當原是那未來亞當的預像。
Duk da haka, mutuwa ta mallake tun daga Adamu har Musa, har ma wadanda basu yi zunubin keta umarni irin na Adamu ba, wanda yake misalin mai zuwan nan a gaba.
15 但恩寵決不是過犯所能比的,因為如果因一人的過犯大眾都死了;那麼,天主的恩寵和那因耶穌基督一人的恩寵所施與的恩惠,更要豐富地洋溢到大眾身上。
Amma kyautar ba kamar keta umarnin take ba. Domin in sabo da laifin mutum dayan nan ne, da yawa suke mutuwa, haka ma alherin sa da baiwarsa ta wurin mutum dayan nan, Yesu Almasihu, sai baiwar ta wadata zuwa ga masu yawa.
16 這恩惠的效果也不是那因人犯罪的結果所能比的,因為審判固然由於一人的過犯而來,被定罪;但恩賜卻使人在犯了許多過犯之後,獲得成義。
Domin kyautar ba kamar sakamakon wannan da yayi zunubin bace. Ta haka din nan ne, hukuncin nan mai tsanani ya zo sabo da zunubin mutum dayan. Har yanzu dai, wannan baiwa ta yanci ta zo ne bayan laifuffuka masu yawa.
17 如果因一人的過犯,死亡就因那一人作了王;那麼,那些豐富地蒙受了恩寵和正義恩惠的人,更要藉著耶穌基督一人在生命中為王了。
Domin, idan sabo da laifin mutum dayan nan ne, mutuwa ta mallake, saboda dayan, haka ma wadanda suka karbi alheri mai yawa da kuma baiwar adalci ta wurin ran, Yesu Almasihu.
18 這樣看來:就如因一人的過犯,眾人都被定了罪;同樣也一人的正義行為,眾人也都獲得了正義和生命。
Don haka, kamar yadda zunubin dayan ya sa hukunci ya zo kan dukka, haka ma aikin adalci na dayan zai kawo barata da rai ga mutane masu yawa.
19 正如因一人的悖逆,大家都成了罪人;同樣,因一人的服從,大眾都成了義人。
Kuma kamar yadda rashin biyayyar dayan ta sa mutane masu yawan gaske su zama masu zunubi, haka ma ta biyayyar dayan mutane da yawan gaske za su sami adalci.
20 法律本是後加的,是為增多過犯;但是罪惡在那裡越多,恩寵在那裡也越格外豐富,
Amma shari'a ta zo, inda ta sa zunubi ya habaka. Amma inda zunubi ya habaka, alheri ma ya habaka ribin ribi.
21 以致罪惡怎樣藉死亡為王,恩寵也怎樣藉正義而為王,使人藉著我們的主耶穌基督獲得永生。 (aiōnios )
Wannan ya faru ne, don kamar yadda zunubi yai mallaka zuwa mutuwa, haka kuma alheri ya mallaka zuwa adalci da rai na har abada ta wurin Yesu Almasihu Ubangijin mu. (aiōnios )