< 啟示錄 4 >

1 這些事以後,我看見天上有一個門開了,並且有我初次聽見,那同我說話像似號角的聲音,說:「你上到這裏來,我要指示給你,這些事以後必須要發生的事。」
Bayan wannan sai na duba, a can kuma a gabana ga ƙofa a buɗe a sama. Sai muryar da na ji da fari da take magana da ni mai kama da busar ƙaho ta ce, “Hauro nan, zan kuma nuna maka abin da lalle zai faru bayan wannan.”
2 我立刻神魂超拔了。看,在天上安置了一個寶座,有一位坐在那寶座上的。
Nan da nan sai ga ni cikin Ruhu, a can a gabana kuwa ga kursiyi a cikin sama da wani zaune a kansa.
3 那位坐著的,看來好似水蒼玉和紅瑪瑙;圍繞寶座的虹霓,看來好似翡翠。
Wannan mai zama a can kuwa yana da kamannin dutsen yasfa da karneliya. Bakan gizo, mai kama da zumurrudu, ya kewaye kursiyin.
4 寶座周圍還有二十四個寶座,寶座上坐著二十四位長老:身穿白衣,頭戴金冠。
Kewaye da kursiyin kuwa akwai waɗansu kursiyoyi ashirin da huɗu, zaune a kansu kuwa dattawa ashirin da huɗu ne. Suna saye da fararen tufafi suna kuma da rawanin zinariya a kawunansu.
5 有閃電、響聲和雷霆從那寶座發出來;在寶座前還燃著七個火炬,那就是天主的七神。
Daga kursiyin hasken walƙiya yana ta fitowa, da ƙararraki da kuma tsawa. A gaban kursiyin, fitilu bakwai suna ci. Waɗannan ne ruhohi bakwai na Allah.
6 寶座前面有如玻璃海,彷彿水晶;在寶座每一面當中,在寶座周圍,有四個活物,前後都滿了眼睛:
Haka kuma a gaban kursiyin akwai wani abu mai kama da tekun gilashi, yana ƙyalli kamar madubi. A tsakiya kuwa, kewaye da kursiyin, akwai halittu huɗu masu rai, cike kuma suna da idanu gaba da baya.
7 第一個活物像獅子,第二個活物像牛犢,第三個活物面貌像人,第四個活物像飛鷹。
Halitta ta fari tana kama da zaki, ta biyun kuwa tana kama da bijimi, ta ukun kuma tana da fuska kamar ta mutum, ta huɗun kuma tana kama da gaggafa mai tashi sama.
8 那四個活物,個個都有六個翅膀,周圍內外都滿了眼睛,日夜不停的說:「聖!聖!聖!上主,全能的天主,是昔在、今在、及將來永在者。」
Kowace a cikin halittu huɗu masu rai ɗin nan tana da fikafikai guda shida, tana kuma cike da idanu a ko’ina, har ma ƙarƙashin fikafikanta. Dare da rana ba sa fasa cewa,
9 每逢那些活物將光榮、尊威和頌謝歸於那坐在寶座上的,萬世萬代的永生者時, (aiōn g165)
Duk lokacin da halittu masu ran nan suka rera ɗaukaka, girma da kuma godiya ga wannan wanda yake zaune a kan kursiyin da kuma wanda yake mai rai har abada abadin, (aiōn g165)
10 二十四位長老就俯伏在坐於寶座的那位前,朝拜那萬世萬代的永生者,且把他們的榮冠投在寶座前說:「 (aiōn g165)
sai dattawa ashirin da huɗun nan su fāɗi a ƙasa a gaban wannan wanda yake zaune a kursiyin, su yi sujada wa wannan wanda yake da rai har abada abadin. Sukan ajiye rawaninsu a gaban kursiyin suna cewa, (aiōn g165)
11 上主,我們的天主!你是堪享光榮、尊威和權能的,因為你創造了萬物,萬物都是因了你的旨意而存在,而造成的。」
“Ya Ubangijinmu da Allahnmu, ka cancanci ɗaukaka da girma da iko, domin ka halicci dukan abubuwa, kuma ta wurin nufinka aka halicce su suka kuma kasance.”

< 啟示錄 4 >