< 民數記 7 >

1 梅瑟豎立起會幕那天,就傅油祝聖了帳幕和其中的一切器具、祭壇和附屬的用具。他傅油祝聖以後,
Sa’ad da Musa ya gama kafa tabanakul, sai ya shafe shi da mai, ya tsarkake shi tare da dukan kayayyakinsa, ya kuma shafe bagaden da mai, ya tsarkake shi da dukan kayayyakinsa.
2 以色列的領袖,各家族首領,即協助登記的各支派的領袖,前來奉獻,
Sa’an nan shugabannin Isra’ila, wato, shugabannin iyalai waɗanda suke shugabancin kabilan da aka ƙidaya, suka miƙa hadayu.
3 將他們的供物獻於上主面前:篷車六輛,公牛十二頭:每兩位領袖一輛車,每位領袖一頭牛。他們把這些送到會幕前時,
Suka kawo kyautansu a gaban Ubangiji. Kyautayin kuwa su ne, kekunan yaƙi shida da aka rufe, da shanu goma sha biyu, saniya guda daga kowane shugaba, da kuma keken yaƙi guda daga shugabanni biyu. Suka miƙa waɗannan a gaban tabanakul.
4 上主訓示梅瑟說:「
Ubangiji ya ce wa Musa,
5 你把這些收下,為會幕的事務使用,按照肋未人的職務,分給他們。」
“Ka karɓi abubuwan nan daga gare su, domin a yi amfani da su a aikin Tentin Sujada. Ka ba da su ga Lawiyawa, a ba kowane mutum bisa ga aikinsa.”
6 梅瑟就收下車輛和牛,交給了肋未人。
Haka fa Musa ya ɗauki kekunan yaƙi da shanun ya ba wa Lawiyawa.
7 按革爾雄子孫的職務,分給了他們兩輛車及四頭牛;
Ya ba wa Gershonawa, kekunan yaƙi biyu da shanu huɗu bisa ga aikinsu,
8 按默辣黎子孫的職務,分給了他們四輛車及八頭牛,他們都在司祭亞郎的兒子依塔瑪爾指揮下服務。
ya kuma ya ba wa kabilar Merari kekunan yaƙi huɗu da shanu takwas bisa ga aikinsu. Aka ba da su duka a ƙarƙashin ikon Itamar ɗan Haruna, firist.
9 但沒有分給刻哈特子孫,因為他們應用肩抬所照管的聖物。
Amma Musa bai ba wa Kohatawa kome ba, gama aikinsu shi ne lura da kayayyaki masu tsarki waɗanda ake ɗauka a kafaɗa.
10 在傅油祝聖祭壇時,眾領袖也為祝聖祭壇奉獻了供物。當眾領袖把他們的供物送到祭壇面前時,
Sa’ad da aka shafe bagaden da mai, sai shugabannin suka kawo hadayunsu saboda keɓewarsa, suka miƙa su a bagaden.
11 上主對梅瑟說:「每天應有一位領袖,奉獻自己的供物,為祝聖祭壇。」
Gama Ubangiji ya riga ya gaya wa Musa cewa, “Kowace rana, shugaba guda zai kawo hadayarsa saboda keɓewar bagade.”
12 第一日奉獻自己供物的,是猶大支派阿米納達布的兒子納赫雄。
Wanda ya kawo hadayarsa a rana ta farko shi ne Nashon ɗan Amminadab, shugaban mutanen Yahuda.
13 他的供物是一個重一百三十「協刻耳」的銀盤,一個依聖所的衡量重七十「協刻耳」的銀盆,兩件內都盛滿油調的細麵,為作素祭;
Hadayar da ya kawo ita ce, faranti guda ɗaya na azurfa, nauyinsa shekel ɗari ɗaya da talatin, da kuma daro na yayyafawa na azurfa, nauyinsa shekel saba’in, dukan biyu, an auna su bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri ne, kowannensu cike da lallausan gari, haɗe da mai kamar hadaya ta gari;
14 一個重十「協刻耳」盛滿香料的金盂;
ya kawo kwanon zinariya ɗaya, mai nauyin shekel goma, cike da turaren hayaƙi;
15 公牛犢一頭,公綿羊一隻,一歲的公羔羊一隻,為作全燔祭;
da ƙaramin bijimi guda ɗaya, tunkiya ɗaya, da rago, dukansu bana ɗaya-ɗaya domin hadaya ta ƙonawa;
16 公山羊一隻,為作贖罪祭;
ya kuma kawo bunsuru ɗaya domin hadaya don zunubi;
17 又公牛二頭,公綿羊五隻,公山羊五隻,一歲的公羔羊五隻,為作和平祭:以上是阿米納達布的兒子納赫雄的供物。
da shanu biyu, raguna biyar, bunsurai biyar da kuma’yan raguna biyar dukansu bana ɗaya-ɗaya, a miƙa su hadaya ta salama. Wannan ita ce hadayar Nashon ɗan Amminadab.
18 第二日奉獻供物的,是依撒加爾的領袖,族阿爾的兒子乃塔乃耳。
A rana ta biyu, Netanel ɗan Zuwar, shugaban mutanen Issakar, ya kawo hadayarsa.
19 他奉獻的供物,是一個重一百三十「協刻耳」的銀盤,一個依聖所的衡量,重七十「協刻耳」的銀盆,兩件內都盛滿油調的細麵,為作素祭;
Hadayar da ya kawo ita ce, faranti guda ɗaya na azurfa, nauyinsa shekel ɗari ɗaya da talatin, da kuma daro na yayyafawa na azurfa, nauyinsa shekel saba’in, dukan biyu, an auna su bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, kowannensu cike da lallausan gari, haɗe da mai kamar hadaya ta gari;
20 一個重十「協刻耳」盛滿香料的金盂;
ya kuma kawo kwanon zinariya ɗaya mai nauyin shekel, goma cike da turaren hayaƙi;
21 公牛犢一頭,公綿羊一隻,一歲的公羔羊一隻,為作全燔祭;
da ƙaramin bijimi guda ɗaya, tunkiya ɗaya da rago, dukansu bana ɗaya-ɗaya domin hadaya ta ƙonawa;
22 公山羊一隻,為作贖罪祭:
ya kuma kawo bunsuru ɗaya domin hadaya don zunubi;
23 又公牛二頭,公綿羊五隻,公山羊五隻,一歲的公羔羊五隻,為作和平祭:以上是族阿爾的兒子乃塔乃耳的供物。
da shanu biyu, raguna biyar, bunsurai biyar da kuma’yan raguna biyar dukansu bana ɗaya-ɗaya, a miƙa su hadaya ta salama. Wannan ita ce hadayar Netanel ɗan Zuwar.
24 第三日是則步隆子孫的領袖,赫隆的兒子厄里雅布。
A rana ta uku, Eliyab ɗan Helon, shugaban mutanen Zebulun, ya kawo hadayarsa.
25 他的供物,是一個重一百三十「協刻耳」的銀盤,一個依聖所的衡量,重七十「協刻耳」的銀盆,兩件內都盛滿油調的細麵,為作素祭;
Hadayar da ya kawo ita ce, faranti guda ɗaya na azurfa, nauyinsa shekel ɗari ɗaya da talatin, da kuma daro na yayyafawa na azurfa, nauyinsa shekel saba’in, dukan biyu, an auna su bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, kowannensu cike da lallausan gari, haɗe da mai kamar hadaya ta gari;
26 一個重十「協刻耳」盛滿香料的金盂;
ya kuma kawo kwanon zinariya ɗaya, mai nauyin shekel goma, cike da turaren hayaƙi;
27 公牛犢一頭,公綿羊一隻,一歲的公羔羊一隻,為作全燔祭;
da ƙaramin bijimi guda ɗaya, tunkiya ɗaya, da rago, dukansu bana ɗaya-ɗaya domin hadaya ta ƙonawa;
28 公山羊一隻,為作贖罪祭;
ya kuma kawo bunsuru ɗaya domin hadaya don zunubi;
29 又公牛二頭,公綿羊五隻,公山羊五隻,一歲的公羔羊五隻,為作和平祭:以上是赫隆的兒子厄里雅布的供物。
da shanu biyu, raguna biyar, bunsurai biyar da kuma’yan raguna biyar, dukansu bana ɗaya-ɗaya, a miƙa su hadaya ta salama. Wannan ita ce hadayar Eliyab ɗan Helon.
30 第四日是勒烏本子孫的領袖,舍德烏爾的兒子厄里族爾。
A ranan ta huɗu, Elizur ɗan Shedeyur, shugaban mutanen Ruben, ya kawo hadayarsa.
31 他的供物,是一個重一百三十「協刻耳」的銀盤,一個依聖所的衡量,重七十「協刻耳」的銀盆,兩件內都盛滿油調的細麵,為作素祭;
Hadayar da ya kawo ita ce, faranti guda ɗaya na azurfa, nauyinsa shekel ɗari ɗaya da talatin, da kuma daro na yayyafawa na azurfa, nauyinsa shekel saba’in, dukan biyu, an auna su bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, kowannensu cike da lallausan gari, haɗe da mai kamar hadaya ta gari;
32 一個重十「協刻耳」盛滿香料的金盂;
ya kuma kawo kwanon zinariya ɗaya mai nauyin shekel goma, cike da turaren hayaƙi;
33 公牛犢一頭,公綿羊一隻,一歲的公羔羊一隻,為作全燔祭;
da ƙaramin bijimi guda ɗaya, tunkiya ɗaya, da rago, dukansu bana ɗaya-ɗaya domin hadaya ta ƙonawa;
34 公山羊一隻,為作贖罪祭;
ya kuma kawo bunsuru ɗaya domin hadaya don zunubi;
35 又公牛二頭,公綿羊五隻,公山羊五隻,一歲的公羔羊五隻,為作和平祭:以上是舍德烏爾的兒子厄里族爾的供物。
da shanu biyu, raguna biyar, bunsurai biyar da kuma’yan raguna biyar, dukansu bana ɗaya-ɗaya, a miƙa su hadaya ta salama. Wannan ita ce hadayar Elizur ɗan Shedeyur.
36 第五日是西默盎子孫的領袖,族黎沙待的兒子舍路米耳。
A rana ta biyar, Shelumiyel ɗan Zurishaddai, shugaban mutanen Simeyon, ya kawo hadayarsa.
37 他的供物,是一個重一百三十「協刻耳」的銀盤,一個依聖所的衡量,重七十「協刻耳」的銀盆,兩件內都盛滿油調的細麵,為作素祭;
Hadayar da ya kawo ita ce, faranti guda ɗaya na azurfa, nauyinsa shekel ɗari ɗaya da talatin, da kuma daro na yayyafawa na azurfa, nauyinsa shekel saba’in, dukan biyu, an auna su bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, kowannensu cike da lallausan gari, haɗe da mai kamar hadaya ta gari;
38 一個重十「協刻耳」盛滿香料的金盂;
ya kuma kawo kwanon zinariya ɗaya mai nauyin shekel goma, cike da turaren hayaƙi;
39 公牛犢一頭,公綿羊一隻,一歲的公羔羊一隻,為作全燔祭;
da ƙaramin bijimi guda ɗaya, tunkiya ɗaya, da rago, dukansu bana ɗaya-ɗaya domin hadaya ta ƙonawa;
40 公山羊一隻,為作贖罪祭;
ya kuma kawo bunsuru ɗaya domin hadaya don zunubi;
41 又公牛二頭,公綿羊五隻,公山羊五隻,一歲的公羔羊五隻,為作和平祭:以上是族黎沙待的兒子協路米耳的供物。
da shanu biyu, raguna biyar, bunsurai biyar da kuma’yan raguna biyar, dukansu bana ɗaya-ɗaya, a miƙa su hadaya ta salama. Wannan ita ce hadayar Shelumiyel ɗan Zurishaddai.
42 第六日是加得子孫的領袖勒烏耳的兒子厄里雅撒夫。
A rana ta shida, Eliyasaf ɗan Deyuwel, shugaban mutanen Gad, ya kawo hadayarsa.
43 他的供物,是一個重一百三十「協刻耳」的銀盤,一個依聖所的衡量,重七十「協刻耳」的銀盆,兩件內都盛滿油調的細麵,為作素祭;
Hadayar da ya kawo ita ce, faranti guda ɗaya na azurfa, nauyinsa shekel ɗari ɗaya da talatin, da kuma daro na yayyafawa na azurfa, nauyinsa shekel saba’in, dukan biyu, an auna su bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, kowannensu cike da lallausan gari, haɗe da mai kamar hadaya ta gari;
44 一個重十「協刻耳」盛滿香料的金盂;
ya kuma kawo kwanon zinariya ɗaya mai nauyin shekel goma, cike da turaren hayaƙi;
45 公牛犢一頭,公綿羊一隻,一歲的公羔羊一隻,為作全燔祭;
da ƙaramin bijimi guda ɗaya, tunkiya ɗaya, da rago, dukansu bana ɗaya-ɗaya domin hadaya ta ƙonawa;
46 公山羊一隻,為作贖罪祭;
ya kuma kawo bunsuru ɗaya domin hadaya don zunubi;
47 又公牛二頭,公綿羊五隻,公山羊五隻,一歲的公羔羊五隻,作和平祭:以上是勒烏耳兒子厄里雅撒夫的供物。
da shanu biyu, raguna biyar, bunsurai biyar da kuma’yan raguna biyar, dukansu bana ɗaya-ɗaya, a miƙa su hadaya ta salama. Wannan ita ce hadayar Eliyasaf ɗan Deyuwel.
48 第七日是厄弗辣因子孫的領袖阿米胡得的兒子厄里沙瑪。
A rana ta bakwai, Elishama ɗan Ammihud, shugaban mutanen Efraim, ya kawo hadayarsa.
49 他的供物,是一個重一百三十「協刻耳」的銀盤,一個依聖所的衡量,重七十「協刻耳」的銀盆,兩件內都盛滿油調的細麵,為作素祭;
Hadayar da ya kawo ita ce, faranti guda ɗaya na azurfa, nauyinsa shekel ɗari ɗaya da talatin, da kuma daro na yayyafawa na azurfa, nauyinsa shekel saba’in, dukan biyu, an auna su bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, kowannensu cike da lallausan gari, haɗe da mai kamar hadaya ta gari;
50 一個重十「協刻耳」盛滿香料的金盂;
kwanon zinariya ɗaya mai nauyin shekel goma, cike da turaren hayaƙi;
51 公牛犢一頭,公綿羊一隻,一歲的公羔羊一隻,為作全燔祭;
da ƙaramin bijimi guda ɗaya, tunkiya ɗaya, da rago, dukansu bana ɗaya-ɗaya domin hadaya ta ƙonawa;
52 公山羊一隻,為作贖罪祭;
ya kuma kawo bunsuru ɗaya domin hadaya don zunubi;
53 又公牛二頭,公綿羊五隻,公山羊五隻,一歲的公羔羊五隻,為作和平祭:以上是阿米胡得的兒子厄里沙瑪的供物。
da shanu biyu, raguna biyar, bunsurai biyar da kuma’yan raguna biyar, dukansu bana ɗaya-ɗaya, a miƙa su hadaya ta salama. Wannan ita ce hadayar Elishama ɗan Ammihud.
54 第八日是默納協子孫的領袖,培達族爾的兒子加默里耳。
A rana ta takwas, Gamaliyel ɗan Fedazur, shugaban mutanen Manasse, ya kawo hadayarsa.
55 他的供物,是一個重一百三十「協刻耳」的銀盤,一個依聖所的衡量,重七十「協刻耳」的銀盆,兩件內都盛滿油調的細麵,為作素祭;
Hadayar da ya kawo ita ce, faranti guda ɗaya na azurfa, nauyinsa shekel ɗari ɗaya da talatin, da kuma daro na yayyafawa na azurfa, nauyinsa shekel saba’in, dukan biyu, an auna su bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, kowannensu cike da lallausan gari, haɗe da mai kamar hadaya ta gari;
56 一個重十「協刻耳」盛滿香料的金盂;
kwanon zinariya ɗaya mai nauyin shekel goma, cike da turaren hayaƙi;
57 公牛犢一頭,公綿羊一隻,一歲的公羔羊一隻,為作全燔祭;
da ƙaramin bijimi guda ɗaya, tunkiya ɗaya, da rago, dukansu bana ɗaya-ɗaya domin hadaya ta ƙonawa;
58 公山羊一隻,為作贖罪祭;
ya kuma kawo bunsuru ɗaya domin hadaya don zunubi;
59 又公牛二頭,公綿羊五隻,公山羊五隻,一歲的公羔羊五隻,為作和平祭:以上是培達族爾的兒子加默里耳的供物。
da shanu biyu, raguna biyar, bunsurai biyar da kuma’yan raguna biyar, dukansu bana ɗaya-ɗaya, a miƙa su hadaya ta salama. Wannan ita ce hadayar Gamaliyel ɗan Fedazur.
60 第九日是本雅明子孫的領袖,基德敖尼的兒子阿彼丹。
A rana ta tara, Abidan ɗan Gideyoni, shugaban mutanen Benyamin, ya kawo hadayarsa.
61 他的供物,是一個重一百三十「協刻耳」的銀盤,一個依聖所的衡量,重七十「協刻耳」的銀盆,兩件內都盛滿油調的細麵,為作素祭;
Hadayar da ya kawo ita ce, faranti guda ɗaya na azurfa, nauyinsa shekel ɗari ɗaya da talatin, da kuma daro na yayyafawa na azurfa, nauyinsa shekel saba’in, dukan biyu, an auna su bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, kowannensu cike da lallausan gari, haɗe da mai kamar hadaya ta gari;
62 一個重十「協刻耳」盛滿香料的金盂;
kwanon zinariya ɗaya mai nauyin shekel goma, cike da turaren hayaƙi;
63 公牛犢一頭,公綿羊一隻,一歲的公羔羊一隻,為作全燔祭;
da ƙaramin bijimi guda ɗaya, tunkiya ɗaya, da rago, dukansu bana ɗaya-ɗaya domin hadaya ta ƙonawa;
64 公山羊一隻,為作贖罪祭;
ya kuma kawo bunsuru ɗaya domin hadaya don zunubi;
65 又公牛二頭,公綿羊五隻,公山羊五隻,一歲的公羔羊五隻,為作和平祭:以上是基德敖尼的兒子阿彼丹的供物。
da shanu biyu, raguna biyar, bunsurai biyar da kuma’yan raguna biyar, dukansu bana ɗaya-ɗaya, a miƙa su hadaya ta salama. Wannan ita ce hadayar Abidan ɗan Gideyoni.
66 第十日是丹子孫的領袖,阿米沙待的兒子阿希厄則爾。
A rana ta goma, Ahiyezer ɗan Ammishaddai, shugaban mutanen Dan, ya kawo hadayarsa.
67 他的供物,是一個重一百三十「協刻耳」的銀盤,一個依聖所的衡量重七十「協刻耳」的銀盆,兩件內都盛滿油調的細麵,為作素祭;
Hadayar da ya kawo ita ce, faranti guda ɗaya na azurfa, nauyinsa shekel ɗari ɗaya da talatin, da kuma daro na yayyafawa na azurfa, nauyinsa shekel saba’in, dukan biyu, an auna su bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, kowannensu cike da lallausan gari, haɗe da mai kamar hadaya ta gari;
68 一個重十「協刻耳」盛滿香料的金盂:
kwanon zinariya ɗaya mai nauyin shekel goma, cike da turaren hayaƙi;
69 公牛犢一頭,公綿羊一隻,一歲的公羔羊一隻,為作全燔祭;
da ƙaramin bijimi guda ɗaya, tunkiya ɗaya, da rago, dukansu bana ɗaya-ɗaya domin hadaya ta ƙonawa;
70 公山羊一隻,為作贖罪祭;
ya kuma kawo bunsuru ɗaya domin hadaya don zunubi;
71 又公牛二頭,公綿羊五隻,公山羊五隻,一歲的公羔羊五隻,為作和平祭:以上是阿米沙待的兒子阿希厄則爾的供物。
da shanu biyu, raguna biyar, bunsurai biyar da kuma’yan raguna biyar, dukansu bana ɗaya-ɗaya, a miƙa su hadaya ta salama. Wannan ita ce hadayar Ahiyezer ɗan Ammishaddai.
72 第十一日是阿協爾子孫的領袖,敖革蘭的兒子帕革厄耳。
A rana ta goma sha ɗaya, Fagiyel ɗan Okran, shugaban mutanen Asher, ya kawo hadayarsa.
73 他的供物,是一個重一百三十「協刻耳」的銀盤,一個依聖所的衡量,重七十「協刻耳」的銀盆,兩件內都盛滿油調的細麵,為作素祭;
Hadayar da ya kawo ita ce, faranti guda ɗaya na azurfa, nauyinsa shekel ɗari ɗaya da talatin, da kuma daro na yayyafawa na azurfa, nauyinsa shekel saba’in, dukan biyu, an auna su bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, kowannensu cike da lallausan gari, haɗe da mai kamar hadaya ta gari;
74 一個重十「協刻耳」盛滿香料的金盂;
kwanon zinariya ɗaya mai nauyin shekel goma, cike da turaren hayaƙi;
75 公牛犢一頭,公綿羊一隻,一歲的公羔羊一隻,為作全燔祭;
da ƙaramin bijimi guda ɗaya, tunkiya ɗaya, da rago, dukansu bana ɗaya-ɗaya domin hadaya ta ƙonawa;
76 公山羊一隻,為作贖罪祭;
ya kuma kawo bunsuru ɗaya domin hadaya don zunubi;
77 又公牛二頭,公綿羊五隻,公山羊五隻,一歲的公羔羊五隻,為作和平祭:以上是敖革蘭的兒子帕革厄耳的供物。
da shanu biyu, raguna biyar, bunsurai biyar da kuma’yan raguna biyar, dukansu bana ɗaya-ɗaya, a miƙa su hadaya ta salama. Wannan ita ce hadayar Fagiyel ɗan Okran.
78 第十二日是納斐塔里子孫的領袖,厄南的兒子阿希辣。
A rana ta goma sha biyu, Ahira ɗan Enan, shugaban mutanen Naftali, ya kawo hadayarsa.
79 他的供物,是一個重一百三十「協刻耳」的銀盤,一個依聖所的衡量,重七十「協刻耳」的銀盆,兩件內都盛滿油調的細麵,為作素祭;
Hadayar da ya kawo ita ce, faranti guda ɗaya na azurfa, nauyinsa shekel ɗari ɗaya da talatin, da kuma daro na yayyafawa na azurfa, nauyinsa shekel saba’in, dukan biyu, an auna su bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, kowannensu cike da lallausan gari, haɗe da mai kamar hadaya ta gari;
80 一個重十「協刻耳」盛滿香料的金盂,
kwanon zinariya ɗaya mai nauyin shekel goma, cike da turaren hayaƙi;
81 公牛犢一頭,公綿羊一隻,一歲的公羔羊一隻,為作全燔祭;
da ƙaramin bijimi guda ɗaya, tunkiya ɗaya, da rago, dukansu bana ɗaya-ɗaya domin hadaya ta ƙonawa;
82 公山羊一隻,為作贖罪祭;
ya kuma kawo bunsuru ɗaya domin hadaya don zunubi;
83 又公牛二頭,公綿羊五隻,公山羊五隻一歲的公羔羊五隻,為作和平祭:以上是厄南的兒子阿希辣的供物。
da shanu biyu, raguna biyar, bunsurai biyar da kuma’yan raguna biyar, dukansu bana ɗaya-ɗaya, a miƙa su hadaya ta salama. Wannan ita ce hadayar Ahira ɗan Enan.
84 以上是傅油祝聖祭壇時,以色列領袖們為祝聖祭壇所奉獻的供物,計有銀盤十二個,銀盆十二個,金盂十二個;
Waɗannan su ne hadayun shugabannin Isra’ilawa saboda keɓewar bagade sa’ad da aka shafe shi, an kawo faranta goma sha biyu na azurfa, darunan goma sha biyu na azurfa don yayyafawa, da kuma kwanonin zinariya goma sha biyu.
85 銀盤每個重一百三十「協刻耳」,銀盆每個重七十,器皿的銀子依聖所的衡量,共重二千四百「協刻耳」;
Kowane faranti na azurfa yana da nauyin shekel ɗari da talatin, kuma kowane daro na azurfa don yayyafawa yana da nauyin shekel saba’in. Duka-duka dai, nauyin kwanonin azurfa, shekel dubu biyu ne da ɗari huɗu, bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri.
86 盛滿香料的金盂十二個,依聖所衡量,每個盂重十「協刻耳」,這些盂的金子,共重一百二十「協刻耳」;
Kwanonin zinariya goma sha biyu da aka cika da turaren hayaƙi kuwa, nauyinsu shekel goma ne kowanne, bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri. Duka-duka dai, nauyin kwanonin zinariya, shekel ɗari ɗaya ne da ashirin.
87 為作全燔祭的一切牲畜,計有公牛犢十二頭,公綿羊十二隻,一歲的公羔羊十二隻,還有同獻的素祭;此外尚有公山羊十二隻,為作贖罪祭;
Jimillar dabbobi don hadaya ta ƙonawa, ta kai ƙanana bijimai goma sha biyu, raguna goma sha biyu da’yan raguna goma sha biyu, dukansu bana ɗaya-ɗaya, tare da hadayarsu ta hatsi. Aka yi amfani da bunsurai goma sha biyu domin hadaya don zunubi.
88 為作和平祭的一切牲畜,計有公牛犢二十四頭,公綿羊六十隻,公山羊六十隻,一歲的公羔羊六十隻:以上是在傅油祝聖祭壇後,為祝聖祭壇所獻的供物。
Jimillar dabbobi don hadaya ta salama, ta kai shanu ashirin huɗu, raguna sittin, bunsurai sittin da kuma’yan raguna sittin, dukansu bana ɗaya-ɗaya. Waɗannan su ne hadayu saboda keɓewar bagade, bayan an shafe shi.
89 當梅瑟進入會幕為同上主說話時,他聽見從約櫃的贖罪蓋上,兩革魯賓間,有與他說話的聲音:是上主在與他說話。
Sa’ad da Musa ya shiga Tentin Sujada don yă yi magana da Ubangiji, sai ya ji murya tana magana da shi daga tsakanin kerubobi biyu a bisa murfin akwatin Alkawari. A ta haka Ubangiji ya yi masa magana.

< 民數記 7 >