< 民數記 29 >

1 七月初一日,你們應召開聖會,一切勞工都不許做:這是你們應歡呼吹號的日子。
“‘A rana ta farko ga wata na bakwai, a yi tsattsarkan taro, kada kuma a yi aikin da aka saba na kullum. Rana ce don busa ƙahoni.
2 應獻給上主馨香的全燔祭,即公牛犢一頭,公綿羊一隻,一歲無瑕疵的公羔羊七隻。
Za a miƙa hadaya ta ƙonawa da bijimi guda, rago guda,’yan raguna bakwai, bana ɗaya-ɗaya don daɗin ƙanshi ga Ubangiji, duka su kasance marasa lahani.
3 至於同獻的素祭,應是油調的細麵:為每隻公牛犢獻大分之三「厄法」,為每隻公綿羊獻十分之二「厄法」;
Tare da bijimin za a kuma miƙa hadaya ta gari na kashi ɗaya bisa goma na efa na lallausan gari, kwaɓaɓɓe da mai; da rago guda, kashi biyu bisa goma na efa na lallausan gari, kwaɓaɓɓe da mai;
4 至於七隻公羔羊, 每獻十分之一「厄法」。
kowane’yan raguna bakwai, kashi ɗaya bisa goma.
5 此外,還應獻一隻公山羊作贖罪祭,為你們贖罪。
A haɗa da bunsuru guda a matsayin hadaya don zunubi, don yin muku kafara.
6 除月朔的全燔祭及同獻的素祭,日常全燔祭及同獻的素祭和依禮規應同獻的奠祭外,還應作為中悅上主的馨香火祭。
Waɗannan ƙari ne ga hadayun ƙonawa na wata-wata da na kullayaumi, tare da hadayun garinsu da hadayun sha yadda aka tsara. Hadayu ne da aka miƙa wa Ubangiji ta wuta don daɗin ƙanshi.
7 七月初十,你們也應召開聖會,苦身克己,一切勞工都不許做。
“‘A rana ta goma ga wannan watan bakwai, za a yi tsattsarkan taro. Ba za ku ci abinci ba, ba kuma za ku yi aiki ba.
8 應給上主獻馨香的全燔祭:即公牛犢一頭,公綿羊一隻,一歲無瑕疵的公羔羊七隻。
Za a miƙa hadaya ta ƙonawa da bijimi guda, rago guda, da kuma’yan raguna bakwai,’yan bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani don daɗin ƙanshi ga Ubangiji.
9 至於同獻的素祭,應是油調的細麵:為每隻公牛犢獻十分之三「厄法」,為每隻公綿羊獻十分之二「厄法」;
Tare da bijimin a miƙa hadaya ta gari na kashi ɗaya bisa goma na efa, na lallausan gari kwaɓaɓɓe, da mai; da rago guda, kashi biyu bisa goma na efa, na lallausan gari kwaɓaɓɓe, da mai;
10 至於那七隻公羔羊,為每隻獻十分之一「厄法」。
kowane’yan raguna bakwai, kashi ɗaya bisa goma.
11 除贖罪節日的贖罪祭,日常全燔祭及同獻 的素祭和應獻的奠外,還應獻一隻公山羊作贖罪祭。
A haɗa da bunsuru guda a matsayin hadaya don zunubi, don yin muku kafara da kuma hadaya ta ƙonawa ta kullum; tare da hadaya ta garinta, da kuma hadayu na shansu.
12 七月十五日,你們也應召開聖會,w勞工都不許做,為上主舉行七天慶節。
“‘A rana ta goma sha biyar ga wata na bakwai, za a yi tsattsarkan taro, ba kuwa za a yi aikin da aka saba yi ba. Ku yi biki ga Ubangiji har kwana bakwai.
13 你們應祭全燔祭,作為中悅上主的火祭:即公牛犢十三頭,公綿羊二隻,一歲的公羔羊十四隻。
A miƙa hadayar da aka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji, hadaya ta ƙonawa ta bijimai guda sha uku, raguna biyu, da’yan raguna goma sha huɗu, bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani.
14 至於同獻的素祭,是油調的細麵:十三頭公牛犢,為每頭獻十分之三「厄法」,二隻公綿羊,為每隻獻十分之二「厄法」。
Da kowane bijimai goma sha uku nan, a miƙa hadaya ta gari, kashi uku bisa goma na efa, kwaɓaɓɓe da mai; da ragunan biyu ɗin, a miƙa hadaya ta gari kashi biyu bisa goma na efa, kwaɓaɓɓe da mai;
15 十四隻公羔羊,為每隻獻十分之一「厄法」。
tare kuma da kowane’yan raguna goma sha huɗu, kashi ɗaya bisa goma.
16 除日常全燔祭及同獻的素祭和奠祭外,還應獻一隻公山羊作贖罪祭。
A haɗa da bunsuru guda, a matsayin hadaya don zunubi, ban da hadaya ta ƙonawa na kullum tare da hadayarta, ta gari da kuma hadaya ta sha.
17 第二日,應獻公牛犢十二頭,公綿羊二隻,一歲無瑕疵的公羔羊十四隻。
“‘A rana ta biyu, a miƙa bijimai goma sha biyu, raguna biyu, da’yan raguna goma sha huɗu, bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani.
18 至於公牛犢、公綿羊和公羔羊應同獻的奠祭和素祭,依數照例奉獻。
Tare da bijiman, ragunan da’yan ragunan a miƙa hadayarsu da gari da hadaya ta sha, bisa ga adadin da aka ƙayyade.
19 除日常全燔祭及同獻的素祭和奠祭外,還應獻一隻公山羊作為贖罪祭。
A haɗa da bunsuru guda a matsayin hadaya, don zunubi, ban da hadaya ta ƙonawa ta kullum, tare da hadayarta ta gari da hadayunsu ta sha.
20 第三日,應獻公牛犢十一頭,公綿羊二隻,一歲無瑕疵的公羔羊十四隻。
“‘A rana ta uku za a miƙa bijimai goma sha ɗaya, raguna biyu, da kuma’yan raguna goma sha huɗu, bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani.
21 至於與公牛犢、公綿羊和公羔羊應同獻的素祭和奠祭外,還應獻一隻公山羊作贖罪祭。
Tare da bijiman, ragunan da’yan raguna, a miƙa hadayun gari da hadayun sha, bisa ga adadin da aka ƙayyade.
22 除日常全燔祭及同獻的素祭和奠祭外,還應獻一隻公山羊作贖罪祭。
A haɗa da bunsuru guda a matsayin hadaya don zunubi, ban da hadaya ta ƙonawa ta kullum, tare da hadayarta ta gari da hadaya ta sha.
23 第四日,應獻公牛犢十頭,公綿羊二隻,一歲無瑕疵的十四隻,
“‘A rana ta huɗu a miƙa bijimai goma, raguna biyu, da’yan raguna goma sha huɗu, bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani.
24 至於公牛犢、公綿羊和公羔羊應同獻的素祭和奠祭,依數照例奉獻。
Tare da bijiman, ragunan da kuma’yan raguna, a miƙa hadayunsu na gari da hadayu na sha bisa ga adadin da aka ƙayyade.
25 除日常全燔祭及同獻的素祭和奠祭外,還應獻一隻公山羊作贖罪祭。
A haɗa da bunsuru guda, a matsayin hadaya don zunubi, ban da hadaya ta ƙonawa ta kullum, tare da hadayarta ta gari da hadaya ta sha.
26 第五日,應獻公牛犢九頭,公綿羊二隻,一歲無瑕疵的十四隻。
“‘A rana ta biyar a miƙa bijimai tara, raguna biyu, da’yan raguna goma sha huɗu, bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani.
27 至於與公牛犢、公綿羊和公羔羊應同獻的素祭和奠祭,依數照例奉獻。
Tare da bijiman, ragunan da kuma’yan ragunan, a miƙa hadayu na gari, da hadayu na sha bisa ga adadin da aka ƙayyade.
28 除日常全燔祭及同獻的素祭和奠祭外,還應獻一隻公山羊作贖罪祭。
A haɗa da bunsuru guda a matsayin hadaya don zunubi, ban da hadaya ta ƙonawa ta kullum, tare da hadayarta ta gari da hadaya ta sha.
29 第六日,應獻公牛犢八頭,公綿羊二隻,一歲無瑕疵的十四隻。
“‘A rana ta shida a miƙa bijimai takwas, raguna biyu, da’yan raguna goma sha huɗu, bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani.
30 至於與公牛犢、公綿羊和公羔羊同獻的素祭和奠祭,依數照例奉獻。
Tare da bijiman, ragunan da kuma’yan raguna, a miƙa hadayunsu ta gari da hadayu na sha bisa adadin da a ƙayyade.
31 除日常全燔祭及同獻的素祭外,還應獻一隻公山羊作贖罪祭。
A haɗa da bunsuru guda a matsayin hadaya don zunubi, ban da hadaya ta ƙonawa ta kullum tare da hadayarta ta hatsi da hadaya ta sha.
32 第七日,應獻公牛犢七頭,公綿羊二隻,一歲無瑕疵的十四隻。
“‘A rana ta bakwai a miƙa bijimai bakwai, raguna biyu da’yan raguna goma sha huɗu, bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani.
33 至於與公牛犢、公綿羊和公羔羊應同獻的素祭和奠祭,依數照例奉獻。
Tare da bijiman, ragunan da kuma’yan raguna, a miƙa hadayunsu na gari, da hadayun sha bisa ga adadin da a ƙayyade.
34 除日常全燔祭及同獻的素祭和奠祭外,還應獻一隻金山羊作贖罪祭。
A haɗa da bunsuru guda a matsayin hadaya don zunubi, ban da hadaya ta ƙonawa ta kullum tare da hadayarta ta hatsi da hadayarta ta sha.
35 第八日,你們應召開盛會,一切勞工都不許做。
“‘A rana ta takwas kuwa za a yi tsattsarkan taro, ban da aikin da aka saba.
36 應獻全燔祭作為中悅上主的馨香火祭:即公牛犢一頭,公綿羊一隻,一歲無瑕疵的七隻。
A miƙa hadayar da aka yi da wuta mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji, a yi hadaya ta ƙonawa da bijimi guda, rago guda, da’yan raguna bakwai, bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani.
37 至於與公牛犢、公山羊和公羔羊及同獻的素祭和奠祭,依數照例奉獻。
Tare da bijimin, ragon da kuma’yan ragunan, a miƙa hadayunsu na gari da hadayu na sha bisa ga adadin da aka ƙayyade.
38 除日常全燔祭及同獻的素祭和奠祭外,還應獻一隻公山羊作贖罪祭。
A haɗa da bunsuru guda a matsayin hadaya don zunubi, ban da hadaya ta ƙonawa ta kullum, tare da hadayarta ta hatsi da hadayarta ta sha.
39 這是你們在慶節內,除那些為還願或自願所獻全燔祭、素祭、奠祭及和平祭外,所應獻給上主的祭獻」。
“‘Ban da abin da kuka yi alkawari, da kuma sadakokinku na yardar rai, a miƙa waɗannan ga Ubangiji a lokacin bukukkuwanku, hadayunku na ƙonawa, hadayu na gari, hadayu na sha da hadayu na salama.’”
40 梅瑟全照上主所吩咐的一切,教訓了以色列子民。
Musa ya faɗa wa Isra’ilawa dukan abin da Ubangiji ya umarce shi.

< 民數記 29 >