< 馬太福音 5 >
1 耶穌一見群眾,就上了山,坐下;他的門徒上他跟前來,
Ganin taron mutane, sai ya hau kan gefen dutse ya zauna. Almajiransa kuwa suka zo wurinsa,
sai ya fara koya musu. Yana cewa,
“Masu albarka ne waɗanda suke matalauta a ruhu, gama mulkin sama nasu ne.
Masu albarka ne waɗanda suke makoki, gama za a yi musu ta’aziyya.
Masu albarka ne waɗanda suke masu tawali’u, gama za su gāji duniya.
Masu albarka ne waɗanda suke jin yunwa da ƙishirwa don gani an yi adalci, gama za a ƙosar da su.
Masu albarka ne waɗanda suke masu jinƙai, gama za a nuna musu jinƙai.
Masu albarka ne waɗanda suke masu tsabtar zuciya, gama za su ga Allah.
9 締造和平的人是有福的,因為他們要稱為天主的子女。
Masu albarka ne waɗanda suke masu ƙulla zumunci, gama za a kira su’ya’yan Allah.
Masu albarka ne waɗanda ake tsananta musu don gani an yi adalci, gama mulkin sama nasu ne.
11 幾時人為了我而辱罵迫害你們,你們是有福的,捏造一切壞話毀謗你們,你們是有福的。
“Masu albarka ne ku, sa’ad da mutane suke zaginku, suna tsananta muku, suna kuma faɗin kowace irin muguwar magana a kanku saboda ni.
12 你們歡喜踴躍罷!因為你們在天上的賞報是豐富的,因為在你們以的先知,人也曾這樣迫害過他們。
Ku yi murna ku kuma yi farin ciki, domin ladarku mai yawa ne a sama, gama haka suka tsananta wa annabawan da suka riga ku.
13 你們是地上的鹽,鹽若失了味,可用什麼使它再鹹呢﹖它再毫無用途,只好拋在外邊,任人踐踏罷了。
“Ku ne gishirin duniya, amma in gishiri ya rabu da daɗin ɗanɗanonsa, yaya za a sāke mai da daɗin ɗanɗanonsa? Ba shi da sauran amfani, sai dai a zubar da shi mutane kuma su tattaka.
“Ku ne hasken duniya. Birnin da yake a bisan tudu ba ya ɓoyuwa.
15 人點燈,並不是於在斗底下,而是於在燈台上,照耀屋人所有的人。
Mutane ba sa ƙuna fitila su rufe ta da murfi. A maimako, sukan ajiye ta a kan wurin ajiye fitila, takan kuma ba da haske ga kowa a cikin gida.
16 照樣,你們的光也當在人前照耀,好使他們看見你們的善行,光耀你們在天之父。
Haka ma, bari haskenku yă haskaka a gaban mutane, domin su ga ayyukanku masu kyau, su kuwa yabi Ubanku da yake cikin sama.
17 你們不要以為我來是廢除法律或先知;我來不為廢除,而是為成全。
“Kada ku yi tsammani na zo ne domin in kawar da Doka ko kuma Annabawa; ban zo domin in kawar da su ba ne, sai dai domin in ciccika su.
18 我實在告訴你們:既使天地過去了,一撇或一劃也決不會從法律上過,必待一切完成。
Gaskiya nake gaya muku, kafin sama da ƙasa sun shuɗe, babu ko ɗan wasali, babu wani ɗigo ta kowace hanya da zai ɓace daga Dokar, sai an cika kome.
19 所以,誰若廢除這些誡命中最小的一條,也這樣教訓人,在天國裏他將稱為最小的;但誰若實行,也這樣教訓人,這人在天國裏將稱為大的。
Duk wanda ya karya ɗaya daga cikin mafi ƙanƙanta na umarnan nan, ya kuma koya wa waɗansu su yi haka, za a ce da shi mafi ƙanƙanta a mulkin sama. Amma duk wanda ya aikata, ya kuma koyar da waɗannan umarnai, za a kira shi mai girma a cikin mulkin sama.
20 我告訴你們:除非你們的義德超過經師和法利賽人的義德,你們決進不了天國。
Gama ina faɗa muku cewa in dai adalcinku bai fi na Farisiyawa da na malaman dokoki ba, faufau, ba za ku shiga mulkin sama ba.
21 你們一向聽過給古人說:『不可殺人!』誰吝殺了人,應受裁判。
“Kun dai ji an faɗa wa mutanen dā cewa, ‘Kada ka yi kisankai; kuma duk wanda ya yi kisankai za a hukunta shi.’
22 我卻對你們說:凡向自己弟兄發怒的,就要受裁判,誰若向自己的弟兄說「傻子」,就要受議會的裁判;誰若說「瘋子」就要受火獄的罰。 (Geenna )
Amma ina gaya muku, duk wanda ya yi fushi da ɗan’uwansa, za a hukunta shi. Kuma duk wanda ya ce wa ɗan’uwansa ‘Raka,’za a kai shi gaban Majalisa. Amma duk wanda ya ce, ‘Kai wawa!’ Zai kasance a hatsarin shiga jahannama ta wuta. (Geenna )
23 所以,你們若在祭壇前,要獻你們的禮物時,在那裏想起你們的弟兄有什麼怨你的事,
“Saboda haka, in kana cikin ba da baikonka a kan bagade, a can kuwa ka tuna cewa ɗan’uwanka yana riƙe da kai a zuci,
24 就把你們的禮物留在那裏,留在祭壇前,先去和你們的弟兄和好,然後再來獻你的禮物。
sai ka bar baikonka a can gaban bagade. Ka je ka shirya tukuna da ɗan’uwanka; sa’an nan ka zo ka ba da baikonka.
25 當你和你的對頭還在路上,趕快與他和解,免得對頭把你交給判官,判官交給差役,把你投在獄裏。
“Ka yi hanzari ka shirya al’amura da maƙiyinka wanda yake ƙararka a kotu. Ka yi haka, tun kana tare da shi a kan hanya, in ba haka ba, zai miƙa ka ga alƙali, alƙali kuma yă miƙa ka ga ɗan sanda, mai yiwuwa kuwa a jefa ka a kurkuku.
26 我實在告訴你。非到你還了最後的一文,決不能從那裏出來。
Gaskiya nake gaya maka, ba za ka fita ba, sai ka biya kobo na ƙarshe.
“Kun dai ji an faɗa, ‘Kada ka yi zina.’
28 我卻對你們說:凡注視婦女,有意貪戀她的,他已在心裏奸淫了她。
Amma ina gaya muku, duk wanda ya dubi mace, sa’an nan ya yi sha’awarta a zuci, ya riga ya yi zina ke nan da ita a zuciyarsa.
29 若是你的右眼使你跌倒,剜出它來,從你身上扔掉,因為喪失你一個肢體,比你全身投入地獄裏,為你更好; (Geenna )
In idonka na dama yana sa ka yin zunubi, ƙwaƙule shi ka yar. Zai fiye maka ka rasa ɗaya daga cikin gaɓoɓin jikinka, da a jefa jikinka ɗungum a cikin jahannama ta wuta. (Geenna )
30 若你的右手手使你跌倒,砍下它來,從你身上扔掉,因為喪失你一個肢體,比你全身投入地獄裏為你更好。 (Geenna )
In kuma hannunka na dama yana sa ka yin zunubi, yanke shi ka yar. Zai fiye maka ka rasa ɗaya daga cikin gaɓoɓin jikinka, da a jefa jikinka ɗungum a cikin jahannama ta wuta. (Geenna )
“An kuma faɗa, ‘Duk wanda ya saki matarsa, dole yă ba ta takardar saki.’
32 我卻對你們說:除了姘居外,凡休自已的妻子的,便是叫她受奸污;並且誰若娶被休的婦人,就是犯奸淫。
Amma ina gaya muku, duk wanda ya saki matarsa in ba a kan laifin zina ba, ya sa ta zama mazinaciya ke nan, kuma duk wanda ya auri macen da mijinta ya sake, shi ma yana zina ne.
33 你們又一向聽過對古人說:『不可發虛誓,要向上主償還你的誓願!』
“Har wa yau dai kun ji an faɗa wa mutane a dā, ‘Kada ka karya alkawarinka, sai dai ka cika alkawaran da ka yi wa Ubangiji.’
34 我卻對你們說:你們總不可發誓:不可指天,因為天是天主的寶座;
Amma ina gaya muku, Kada ku yi rantsuwa sam, ko da sama, domin kursiyin Allah ne;
35 不可指地,地是他的腳凳,不可指耶路撒冷,因它是大王的城市;
ko da ƙasa, domin matashin ƙafafunsa ne; ko kuma da Urushalima, domin birnin Babban Sarki ne.
36 也不可指你的頭發誓,因為你不能使一根頭髮變白或變黑。
Kada kuma ka rantse da kanka, domin ba za ka iya mai da ko gashi ɗaya yă zama fari ko baƙi ba.
37 你們的話當是:是就說是,非就說非;其他多餘的便是出於邪惡。
Abin da ya kamata ku ce kawai, shi ne, I, ko A’a. Abin da ya wuce haka kuwa daga wurin Mugun nan yake.
“Kun dai ji an faɗa, ‘Ido domin ido, haƙori kuma domin haƙori.’
39 我卻對你們說:不要抵抗惡人:而且,若有人掌擊你的右頰,你把另一面也轉給他。
Amma ina gaya muku, Kada ku yi tsayayya da mugun mutum. In wani ya mare ka a kumatun dama, juya masa ɗayan ma.
40 那願與你爭訟,拿你的內衣的,你連外衣也讓給他。
In kuma wani yana so yă yi ƙararka yă ƙwace rigarka, to, ba shi mayafinka ma.
In wani ya tilasta ka yin tafiya mil ɗaya, to, tafi tare da shi mil biyu.
Ka ba wa duk wanda ya roƙe ka abu, kada kuma ka hana wa wanda yake neman bashi daga gare ka.
43 你們一向聽說過:『你應愛你的近人,恨你的仇人!』
“Kun dai ji an faɗa, ‘Ka ƙaunaci maƙwabcinka, ka kuma ƙi abokin gābanka.’
44 我卻對你們說:你們當愛你們的仇人,當為迫害你們的人祈禱,
Amma ina gaya muku, ku ƙaunaci abokan gābankukuma ku yi wa waɗanda suke tsananta muku addu’a,
45 好使你們成為你們在天之父的子女,因為衪使太陽上升,光照惡人,也光照善人;降雨給義,也給不義的人。
don ku zama’ya’yan Ubanku na sama. Shi yakan sa ranarsa ta haskaka a kan mugaye da masu kirki; yakan kuma sako ruwan sama a bisa masu adalci da marasa adalci.
46 你們若只愛那愛你們的人,你們還有什麼賞報呢? 稅吏不是也這樣做嗎﹖
In masoyarku kawai kuke ƙauna, wace lada ce gare ku? Ko masu karɓar haraji ma ba haka suke yi ba?
47 你們若只問候你們的弟兄,你們做了什麼特別的呢? 外邦人不是也這樣做嗎﹖
In kuwa kuna gai da’yan’uwanku ne kaɗai, me kuke yi fiye da waɗansu? Marasa bin Allah ma ba haka suke yi ba?
48 所以你們應當是成全的,如同你們的父是成全的一樣。
Saboda haka sai ku zama cikakku, yadda Ubanku na sama yake cikakke.