< 馬太福音 17 >
1 天以後,耶穌帶著伯多祿,雅各伯和他的兄弟若望,單獨帶領他們上了一座高山,
Bayan kwana shida Yesu ya dauki Bitrus da Yakubu, da Yahaya dan'uwansa, ya kai su kan wani dutse mai tsawo su kadai.
2 在他們面前變了容貌發光有如太陽,他的衣服潔白如光。
Kamanninsa ya canja a gabansu. Fuskarsa ta haskaka kamar rana, kuma rigunansa suka yi kyalli fal.
3 忽然,梅瑟和厄里亞也顯現給他們,正在同耶穌談論。
Sai ga Musa da Iliya sun bayyana garesu suna magana da shi.
4 伯多祿就開口對耶穌說:「主啊! 我們在這裏真好!你若願意,我就在這裏搭三個帳棚:一個為你,一個為梅瑟,一個為厄里亞。」
Bitrus ya amsa ya ce wa Yesu, “Ubangiji, ya yi kyau da muke a wurin nan. In kana so, zan yi bukkoki uku daya dominka, daya domin Musa, daya domin Iliya.”
5 他還在說話的時候,忽然有一片光耀的雲彩遮敝了他們,並且雲中有聲因說:「這是我的愛子,我所喜悅的,你們要聽從他!」
Sa'adda yake cikin magana, sai, girgije mai haske ya rufe su, sai murya daga girgijen, tana cewa, “Wannan kaunattacen Dana ne, shi ne wanda yake faranta mani zuciya. Ku saurare shi.”
Da almajiran suka ji haka, suka fadi da fuskokinsu a kasa, saboda sun tsorata.
Sai Yesu ya zo ya taba su ya ce, “Ku tashi, kada ku ji tsoro.”
8 他們舉目一看,任誰都不見了,只有耶穌獨自一人。
Amma da suka daga kai ba su ga kowa ba sai Yesu kadai.
9 他們從山上下來的時候,耶穌囑咐他們說:「非等人子由死者中復活,你們不要將所見告的告訴任何人」
Yayin da suke saukowa daga dutsen, Yesu ya umarce su, ya ce, “Kada ku fadawa kowa wannan wahayin, sai Dan Mutum ya tashi daga matattu.”
10 門徒便問耶穌說:「那麼,為什麼經師說:厄里亞應該先來呢?」
Almajiransa suka tambaye shi, suka ce, “Don me marubuta ke cewa lallai ne Iliya ya fara zuwa?”
11 耶穌回答說:「厄里亞的確要來,且要重整一切;
Yesu ya amsa ya ce, “Hakika, Iliya zai zo ya maido da dukan abubuwa.
12 但我告訴你們:厄里亞已經來了,人們卻不認識他,反兒任意待了他;照樣,人子也要受他們的磨難。」
Amma ina gaya maku, Iliya ya riga ya zo, amma ba su gane shi ba. A maimakon haka, suka yi masa abin da suka ga dama. Ta irin wanan hanya, Dan Mutum kuma zai sha wuya a hannunsu.
13 門徒這纔明白耶穌給他們所說的,是指的洗者若翰。
Sa'annan almajiransa suka fahimci cewa yana yi masu magana a kan Yahaya mai Baftisma ne.
14 當他們來到群眾那裏時,有一個人來到耶穌跟前,跪下說:
Da suka iso wurin taron, wani mutum ya zo gunsa, ya durkusa a gaban sa, ya ce,
15 「主啊,可憐我的兒子罷!他患癲癇病很苦,屢次跌在火中,又屢次跌在水裏。
“Ubangiji, ka ji tausayin yarona, domin yana da farfadiya, kuma yana shan wuya kwarai, domin sau da yawa yana fadawa cikin wuta ko ruwa.
16 我把他帶到你的們徒跟前,他們卻不能治好他。」
Na kawo shi wurin almajiran ka, amma ba su iya su warkar da shi ba.”
17 耶穌回答說:「哎!無信敗壞的世代,我同你們在一起要到幾時呢? 我容忍你們要到幾時呢?把他給我帶到這裏來!」
Yesu ya amsa ya ce, “Marasa bangaskiya da karkataccen zamani, har yaushe zan kasance tare da ku? Har yaushe zan jure da ku? Ku kawo shi nan a wurina.”
18 耶穌遂叱責魔鬼,魔鬼就從還子身上出去了;從那時刻,孩子就好了。
Yesu ya tsauta masa, sai aljanin ya fita daga cikinsa. Yaron ya warke nan take.
19 以後,門徒前來私下對耶穌說:「為什麼我們不能逐出這魔鬼呢?」
Sai almajiran suka zo wurin Yesu a asirce suka ce, “Me ya sa muka kasa fitar da shi?”
20 耶穌對他們說:「由於你們缺少信德;我實在告訴你們:假如你們有像芥子那麼大的信德,你們向這座山說:從這邊移到那邊去!它必會移過去的;為你們沒有不可能的事。
Yesu ya ce masu, “Saboda karancin bangaskiyarku. Domin hakika, ina gaya maku, in kuna da bangaskiya ko da kamar kwayar mastad, za ku ce wa wannan dutse, 'Matsa daga nan ka koma can,' zai kuwa matsa kuma ba abin da zai gagare ku.
21 『但這類魔鬼非用祈禱和禁食,是不能趕出去的。』
[Irin wannan aljanin bashi fita sai tare da addu'a da azumi].
22 當耶穌同門徒在加里肋亞周遊時,耶穌對他們說:「人子將被交於人們手中。
Suna zaune a Galili, Yesu ya ce wa almajiransa, “Za a bada Dan Mutum ga hannun mutane.
23 他們要殺害他,第三天他必要復活。門徒就非常憂鬱。
Kuma za su kashe shi, a rana ta uku zai tashi.” Sai almajiransa suka yi bakin ciki kwarai.
24 他們來到葛法翁時,收殿稅的人來到伯多祿跟前說:「你們的師傅不納殿稅嗎?」
Da suka iso Kafarnahum, mutane masu karbar haraji na rabin shekel suka zo wurin Bitrus suka ce, “Malaminku na ba da rabin shekel na haraji?”
25 伯多碌說:「自然納的。」他一進到屋裏,耶穌就先對他說:「西滿!你以為怎樣?地上的君王向誰征收關稅或丁稅呢?向自己的兒子,或是向外人?
Sai ya ce, “I.” Amma da Bitrus ya shiga cikin gida, Yesu ya fara magana da shi yace, “Menene tunaninka Saminu? Sarakunan duniya, daga wurin wa suke karbar haraji ko kudin fito? Daga talakawansu ko daga wurin baki?”
26 伯多碌說:「向外人。」耶穌對他說:「所以兒子是免稅的了。
Sai Bitrus ya ce, “Daga wurin baki,” Yesu ya ce masa, “Wato an dauke wa talakawansu biya kenan.
27 但是,為避免使他們疑怪,你往海邊去垂釣,拿釣上來的第一條魚,開了它的口,就會找到一塊「斯塔特。」拿去交給他們,當作我和你的殿稅。」
Amma don kada mu sa masu karbar harajin su yi zunubi, ka je teku, ka jefa kugiya, ka cire kifin da ya fara zuwa. Idan ka bude bakinsa, za ka sami shekel. Ka dauke shi ka ba masu karbar harajin nawa da naka.