< 馬可福音 9 >
1 耶穌又對他們說:「我實在告訴你們:站在這裏的人中,就有幾個在未嘗到死味以前,必要看見又主的國帶著威能降來。」
Ya kuma ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, waɗansu da suke tsattsaye a nan ba za su mutu ba, sai sun ga mulkin Allah ya bayyana da iko.”
2 六天後,耶穌帶著伯多祿、雅各伯和若望,單獨帶領他們上了一座高山,在他們前變了容貌:
Bayan kwana shida, sai Yesu ya ɗauki Bitrus, Yaƙub da Yohanna tare da shi, ya kai su kan wani dutse mai tsawo, suka kasance su kaɗai a wurin. A can aka sāke kamanninsa a gabansu.
3 他的衣服發光,那樣潔白,世上沒有一個漂布的能漂得那樣白。
Tufafinsa suka zama fari suna ƙyalli, fiye da yadda wani a duniya zai iya yi su.
Iliya da Musa suka bayyana a gabansu, suna magana da Yesu.
5 伯多祿遂開口對耶穌說:「「師傅,我們在這裏真好! 讓我們搭三個帳棚:一個為你,一個為梅瑟,一個為厄里亞。」
Bitrus ya ce wa Yesu, “Rabbi, ya yi kyau da muke nan. Bari mu kafa bukkoki guda uku, ɗaya dominka, ɗaya domin Musa, ɗaya kuma domin Iliya.”
(Bai san abin da zai faɗa ba ne, gama sun tsorata ƙwarai.)
7 當時,有一團雲彩遮蔽了他們,從雲中有聲音說:「這是我的愛子,你們要聽從他!」
Sai wani girgije ya bayyana, ya rufe su, wata murya kuma ta fito daga girgijen, ta ce, “Wannan Ɗana ne, wanda nake ƙauna, ku saurare shi!”
8 他們忽然向四周一看,任誰都不見了,只有耶穌同他們在一起。
Farat ɗaya, da suka waiwaya, ba su ƙara ganin kowa tare da su ba, sai dai Yesu.
9 他們從山上下來的時候,耶穌囑咐他們,非等人子從死者中復活後,不要將他們所見的告訴任何人。
Da suna saukowa daga dutsen, Yesu ya umarce su kada su gaya wa kowa abin da suka gani, sai bayan Ɗan Mutum ya tashi daga matattu.
10 他們遵守了這話,卻彼此論從死者中復活是什麼意思。
Suka riƙe wannan zance a ɓoye tsakaninsu, suna tattaunawa ko mece ce ma’anar “tashi daga matattu.”
11 他們就問耶穌說:「為什麼經師們說厄里亞應該先來﹖」
Suka tambaye shi, suka ce, “Don me malaman dokoki suke cewa, sai Iliya ya fara zuwa?”
12 耶穌對他們說:「厄里亞固然要先來整理一切:但是經上關於人子應受許多痛苦,被人輕慢,是怎樣記載的呢﹖
Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya ne, Iliya zai zo da fari, yă kuma mayar da dukan abubuwa. Don me kuma aka rubuta cewa, dole Ɗan Mutum yă sha wahala sosai, kuma a ƙi shi?
13 可是,我告訴你們:厄里亞己經來了,人們任意對待了他,正如經上關於他所記載的。」
Amma ina faɗa muku, Iliya ya riga ya zo, kuma suka yi duk abin da suka ga dama da shi, kamar yadda aka rubuta game da shi.”
14 他們來到門徒那裏,看見一大群人圍著他們,經師和他們正在辯論。
Da suka dawo wurin sauran almajiran, sai suka ga babban taro kewaye da su, malaman dokoki suna gardama da su.
15 全民眾一看見了耶穌,就都驚奇,立刻向前跑去問候他。
Nan take da dukan mutanen suka ga Yesu, sai suka cika da mamaki, suka ruga da gudu don su gai da shi.
Ya tambaye su ya ce, “Gardamar me kuke yi da su?”
17 群眾中有一個人回答說:「師傅,我帶了我的兒子來見你,他附著一個啞吧魔鬼;
Wani mutum a cikin taron ya amsa ya ce, “Malam, na kawo maka ɗana mai wani ruhun da yake hana shi magana.
18 無論在那裏,魔鬼抓住他,就把他摔倒,他就口吐白沫,咬牙切齒,並且僵硬了。我曾請你的門徒把魔鬼逐出,他們卻不能。」
Duk lokacin da mugun ruhun ya kama shi, yakan jefa shi a ƙasa. Bakinsa yakan yi kumfa, yă cije haƙorarsa, yakan sa jikinsa ya sandare, yă zama da ƙarfi. Na roƙi almajiranka su fitar da ruhun, amma ba su iya ba.”
19 耶穌開口向他們說:「哎! 無信的世代! 我與你們在一起要到幾時呢﹖我容忍你們要到幾時呢﹖帶他到我這裏來! 」
Yesu ya ce, “Ya ku zamani marar bangaskiya, har yaushe zan kasance tare da ku? Har yaushe zan yi haƙuri da ku? Kawo mini yaron.”
20 他們就把孩子領到耶穌跟前。魔鬼一見耶穌,立時使那孩子拘攣了一陣,那孩子便倒在地上,打滾吐沫。
Sai suka kawo shi. Da ruhun ya ga Yesu, nan da nan sai ya buge yaron da farfaɗiya. Ya fāɗi a ƙasa, yana birgima, bakinsa yana kumfa.
21 耶穌問他的父親說:「這事發生在他身上有多少時候了﹖」他回答說:「從小的時候;
Yesu ya tambayi mahaifin yaron ya ce, “Tun yaushe yake haka?” Ya ce, “Tun yana ƙarami.
22 魔鬼屢次把他投到火裏或水裏,要害死他。但是,你若能做什麼,你就憐憫我們,幫助我們罷!」
Ya sha jefa shi cikin wuta, ko ruwa don yă kashe shi. Amma in za ka iya yin wani abu, ka ji tausayinmu ka taimake mu.”
23 耶穌對他說:「『你若能,』為信的人,一切都是可能的! 」
Yesu ya ce, “‘In za ka iya’? Ai, kome mai yiwuwa ne ga wanda ya gaskata.”
24 小孩子的父親立刻喊說:「我信! 請你補助我的無信罷!」
Nan da nan mahaifin yaron ya faɗa da ƙarfi ya ce, “Na gaskata, ka taimake ni in sha kan rashin bangaskiyata!”
25 耶穌看見群眾都跑過來,就叱責邪魔說:「又聾又啞的魔鬼,我命你從他身上出去! 不要再進入他內!」
Da Yesu ya ga taron suna zuwa can a guje, sai ya tsawata wa mugun ruhun ya ce, “Kai ruhun kurma, da na bebe, na umarce ka, ka fita daga cikinsa, kada kuma ka ƙara shigarsa.”
26 魔鬼就喊叫起來,猛烈使那孩子拘攣了一陣,就出去了;那孩子好像死了一樣,以致有許多人說:「他死了! 」
Sai ruhun ya yi ihu, ya buge shi da ƙarfi da farfaɗiya, ya fita. Yaron ya kwanta kamar matacce, har mutane da yawa suka ce, “Ai, ya mutu.”
27 但是,耶穌握住他的手,拉他起來,他就起來了。
Amma Yesu ya kama shi a hannu ya ɗaga, ya kuwa tashi tsaye.
28 耶穌進到家裏,他的門徒私下問他說:「為什麼我們不能趕他出去﹖」
Da Yesu ya shiga gida, almajiransa suka tambaye shi a ɓoye, suka ce, “Me ya sa ba mu iya fitar da shi ba?”
29 耶穌對他們說:「這一類,非用祈禱[和禁食,]是不能趕出去的。」
Ya amsa ya ce, “Sai da addu’akaɗai irin wannan yakan fita.”
30 他們從那裏起身,經過加里肋亞;耶穌卻不願叫人知道。
Suka bar wurin suka bi ta Galili. Yesu bai so wani yă san inda suke ba,
31 因為那時他教訓他的門徒,給他們說:「人子將要被交在人手中,為人所殺;被殺以後,過了三天, 他必要復活。」
gama yana koya wa almajiransa. Ya ce musu, “Za a ci amanar Ɗan Mutum, a ba da shi ga hannun mutane. Za su kashe shi, bayan kwana uku kuma zai tashi.”
Amma ba su fahimci abin da yake nufi ba, suka kuma ji tsoro su tambaye shi game da wannan.
33 他們來到葛法翁,到了家裏,耶穌問他們說:「你們在路上爭論了什麼﹖」
Suka iso Kafarnahum. Da yana cikin gida, sai ya tambaye su ya ce, “Gardamar me kuke yi a hanya?”
34 他們都默不作聲,因為他們在路上彼此爭論誰最大。
Amma suka yi shiru, don a hanya suna gardama ne, a kan ko wane ne a cikinsu ya fi girma?
35 耶穌坐下,叫過那十二人來,給他們說:「誰若想做第一個,他就得做眾人中最末的一個,並要做眾人的僕役。」
Da Yesu ya zauna, sai ya kira Sha Biyun ya ce, “In wani yana so yă zama na fari, dole yă zama na ƙarshe duka, da kuma bawan kowa.”
36 遂領過一個小孩子來,放在門徒中間,抱起他來,給他們說:
Ya ɗauki wani ƙaramin yaro ya sa yă tsaya a tsakiyarsu. Ya ɗauke shi a hannunsa, ya ce musu,
37 「誰若因我的名字,收留一個這樣的小孩子,就是收留我;誰若收留我, 並不是收留我,而是收留那派遣我來的。」
“Duk wanda ya karɓi ɗaya daga cikin waɗannan ƙananan yara a cikin sunana, ni ya karɓa. Duk wanda kuma ya karɓe ni, ba ni ya karɓa ba, amma wanda ya aiko ni ne ya karɓa.”
38 若望向耶穌說:「師傅! 我們見過一個人,他因你的名字驅魔,我們禁止了他,因為他不跟從我們。」
Yohanna ya ce, “Malam mun ga wani mutum yana fitar da aljanu a cikin sunanka, sai muka ce yă daina, domin shi ba ɗaya daga cikinmu ba ne.”
39 耶穌說:「不要禁止他,因為沒有任何人,以我的名字行了奇跡,就會立刻毀謗我的,
Yesu ya ce, “Kada ku hana shi. Ba wanda yake yin ayyukan banmamaki a cikin sunana, nan take yă faɗi wani abu mummuna game da ni.
Gama duk wanda ba ya gāba da mu, namu ne.
41 「誰若因你們屬於基督,而給你們一杯水喝,我實在告訴你們:他決不會失掉他的賞報。
Gaskiya nake gaya muku, duk wanda ya ba ku ruwan sha a sunana, saboda ku na Kiristi ne, lalle, ba zai rasa ladarsa ba.
42 誰若使這些信者中的一個小子跌倒,倒不如拿一塊驢拉的磨石,套在他的脖子上,投在海裏,為他更好。
“Idan kuma wani yă sa ɗaya daga cikin waɗannan’yan yara masu gaskatawa da ni yă yi laifi, zai fiye masa a rataya wani babban dutsen niƙa a wuyarsa, a jefa shi cikin teku.
43 倘若你的手使你跌倒,砍掉它! (Geenna )
In hannunka yana sa ka yin zunubi, yanke shi. Ai, gwamma ka shiga rai da hannu ɗaya, da ka shiga jahannama ta wuta, inda ba a iya kashe wutar ba, da hannuwanka biyu. (Geenna )
44 你殘廢進入生命,比有兩隻手而往地獄裏,到那不滅的火裏去更好。 ()
45 倘若你的腳使你跌倒,砍掉它! (Geenna )
In kuma ƙafarka tana sa ka yin zunubi, yanke ta. Ai, gwamma ka shiga rai da ƙafa ɗaya, da a jefa ka cikin jahannama ta wuta, da ƙafafunka biyu. (Geenna )
46 你瘸腿進入生命,比有雙腳被投入地獄裏更好。 ()
47 倘若你的眼使你跌倒,剜出它來! 你一隻眼進入天主的國,比有兩隻眼被投入地獄裏更好, (Geenna )
In kuma idonka yana sa ka zunubi, ƙwaƙule shi. Ai, gwamma ka shiga mulkin Allah da ido ɗaya, da a jefa ka cikin jahannama ta wuta, da idanu biyu, (Geenna )
inda “‘tsutsotsinsu ba sa mutuwa, wutar kuma ba a iya kashewa.’
Za a tsarkake kowa da wuta.
50 鹽是好的;但鹽若成了不鹹的,你們可用什麼去調和它﹖在你們中間當有鹽,又該彼此和平相處。」
“Gishiri yana da daɗi, amma in ya rabu da ɗanɗanonsa, ta yaya za a sāke mai da ɗanɗanonsa? Ku kasance da gishiri a cikinku, ku kuma yi zauna lafiya da juna.”