< 瑪拉基書 2 >
“Yanzu fa wannan gargaɗi dominku ne, ku firistoci.
2 如果你們不聽從,不把光榮我名的事放在心上──萬軍的上主說──我必使詛咒臨到你們身上,使你們的祝福變為詛咒。我已詛咒了,因為中誰也沒有把這事放在心上。
In ba ku saurara ba, in kuma ba ku sa zuciyarku ga girmama sunana ba, zan aukar muku da la’ana, zan kuma la’antar da albarkunku. I, na riga na la’anta su, domin ba ku sa zuciyarku ga girmama ni ba, in ji Ubangiji Maɗaukaki.
3 看,我必要砍斷你們的手臂,把糞污,即你們祭牲的糞污,撒在你們的臉上,使你們滿面慚愧。
“Saboda ku zan tsawata wa zuriyarku; zan watsa kashin dabbobin hadayunku a fuskokinku, a kuma kwashe ku tare da shi.
4 這樣你們便知道,我為你們提出了這警告,是為保存我與肋未所訂立的盟約,──萬軍的上主說。
Za ku kuwa san cewa ni ne na aika muku da wannan gargaɗi domin alkawarina da Lawi yă ci gaba,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.
5 我與他訂立的盟約,是有關生命及平安的盟,所以我賜給了他生命和平安;同時又是敬畏的盟約,所以他敬畏我,對我的名有所尊敬;
“Alkawarina da shi, alkawari ne na rai da salama, wanda na ba shi; domin yă girmama ni, ya kuwa girmama ni, ya kuma ji tsoron sunana ƙwarai.
6 在他口中有真實教訓,在他脣舌上從不見謊言;他心懷虔誠和正直與我來往,使多人遠離了罪惡。
Umarnin gaskiya yana a bakinsa, ba a kuma sami wani ƙarya a leɓunansa ba. Ya yi tafiya tare da ni cikin salama da adalci, ya kuwa juyo da mutane masu yawa daga zunubi.
7 的確,司祭的脣應保衛智識,人也應該從他的口中得到教訓,因為他是萬軍上主的使者。
“Gama ya kamata leɓunan firist su kiyaye ilimi, ya kamata kuma mutane su nemi umarni daga bakinsa, domin shi ne manzon Ubangiji Maɗaukaki.
8 但是你們卻離棄正道,使許多人在法律上跌倒;你們破壞了我和肋未所立的盟約──萬軍的上主說。
Amma sai kuka kauce hanya, ta wurin koyarwarku kuma kuka sa mutane da yawa suka yi tuntuɓe; kun keta alkawarin da na yi da Lawi,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.
9 為,此我也使你們受全體人民的輕視,因為你們沒有遵行我的道,在施教訓上觀情顧面。
“Saboda haka na sa a rena ku, a kuma wulaƙanta ku a gaban dukan mutane, domin ba ku bi hanyoyina ba amma kuka nuna sonkai a al’amuran shari’a.”
10 我們是共有一個父親嗎﹖不是一個天主造生了我們嗎﹖為什麼我們彼此欺騙褻瀆我們祖先的盟約﹖
Ashe, ba Mahaifi guda dukanmu muke da shi ba? Ba Allah ɗaya ne ya halicce mu ba? Don me muka keta alkawarin kakanninmu ta wurin cin amanar juna?
11 猶大不守信義,在以色列和耶路撒冷行了醜惡的事,因為猶大褻瀆了上主所愛的聖所,娶了供奉邦神祗的女子。
Yahuda ya ci amana. An yi abin kunya a Isra’ila da kuma a Urushalima. Yahuda ya ƙazantar da wuri mai tsarkin da Ubangiji yake ƙauna, ta wurin auren’yar wani baƙon allah.
12 惟願上主將行這事的人,連証證的人和監誓人,從雅各伯的會幕中剷除,由向萬軍的上主奉獻祭物的集會中剷除。
Game da mutumin da ya aikata wannan, ko wane ne shi, bari Ubangiji yă yanke shi daga tentunan Yaƙub, ko da ma ya kawo hadayu ga Ubangiji Maɗaukaki.
13 其次,你們還行了這件事:你們向上主的祭壇灑盡了眼淚,哭泣呻吟,
Ga kuma wani abin da kuke yi. Kukan cika bagaden Ubangiji da hawaye. Kukan yi kuka kuna ihu gama Ubangiji ba ya mai da hankali ga hadayunku ko yă karɓe su da farin ciki.
14 你們還問:「這是為什麼﹖」是因為上主是你與你青年時所娶的妻子之間的証人。她雖是你的伴侶,是你結盟的髮妻,你道對她不守信義。
Kukan ce, “Don me ba ya karɓan hadayunmu?” Ai, domin Ubangiji ya zama shaida tsakaninka da matar ƙuruciyarka, gama ka keta amanar da ka yi mata, ko da yake ita abokiyar zamanka ce, matar aurenka ta alkawari.
15 上主不是造了他們成為一體,一個肉身,一個性命嗎﹖為什麼要結為一體﹖是為求得天主的子女;所以應關心你們的性命,對你青年結髮的妻子不要背信。
Ashe, Ubangiji bai maishe su ɗaya ba? Cikin jiki da ruhu, su nasa ne. Me ya sa suke ɗaya? Domin yana neman’ya’ya masu tsoron Allah. Saboda haka sai ka lura da kanka, kada kuma ka ci amanar matar ƙuruciyarka.
16 上主以色列的天主說:我憎恨休妻,休妻使人在自己的衣服上沾滿了不義,萬軍的上主聲明說。所以你們當關心你們的性命,不要不守信莪。
“Na ƙi kisan aure,” in ji Ubangiji, Allah na Isra’ila. “Na kuma ƙi mutumin da ya rufe kansa da tashin hankali kamar riga,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. Saboda haka sai ka lura da kanka, kada kuma ka ci amana.
17 你們的言談使上主生厭,你們還問:「我們在什麼事上使衪生厭﹖」即在你們說:「凡作惡的,在天主眼裏都是善的,而且衪還喜悅他們,」或說:「公義的天主在哪裏﹖」的時候。
Kun sa Ubangiji Maɗaukaki ya gaji da maganganunku. Sai kuka ce, “Yaya muka sa ya gaji?” Kun yi haka ta wurin cewa, “Duk waɗanda suke aikata mugunta, mutanen kirki ne a gaban Ubangiji, yana kuwa jin daɗinsu,” kuna kuma cewa, “Ina Allah mai adalci yake?”