< 路加福音 10 >
1 此後,主另外選定了七十二人,派遺他們兩個兩個地在祂在前面,到祂自己將要去的各城地去。
Bayan haka, Ubangiji ya naɗa waɗansu mutum saba’in da biyu, ya aike su biyu-biyu, su riga shi yin gaba zuwa kowane gari da kowane wuri da zai shiga.
2 祂對他們說:「莊稼多而工人少,所以你們應當求莊稼的主人,派遺工人來,收割祂的莊稼。
Ya ce musu, “Girbi na da yawa, amma ma’aikata kaɗan ne. Saboda haka, ku roƙi Ubangijin girbi ya aikar da ma’aikata zuwa gonarsa.
Ku tafi! Ina aikan ku kamar tumaki cikin kyarketai.
4 你們不要帶錢囊,不要帶口袋,也不要帶鞋;路上也不要向人請安。
Kada ku ɗauki jakar kuɗi, ko jaka, ko takalma. Kada ma ku gai da kowa a kan hanya.
“Sa’ad da kuka shiga wani gida, ku fara da cewa, ‘Salama a gare ku mutanen gida.’
6 那裡如有和和平之子,你們的平安就要停留在他身上;否則仍歸於你們。
In akwai mutum mai salama a gidan, salamarku za tă kasance tare da shi, in kuwa babu, salamarku za tă koma muku.
7 你們要住在那一家,吃喝他們所供給的,因為工人自當有他的工資;你們不可從這一家挪到那一家。
Ku zauna a wannan gidan, kuna ci kuna shan duk abin da suka ba ku, gama ma’aikaci ya cancanci albashinsa. Kada ku yi yawan sāke masauƙi, daga gida zuwa gida.
8 不論進了那座城,人若接納你們,給你們擺上什麼,你們就吃什麼。
“Sa’ad da kuka shiga garin, kuma aka karɓe ku, ku ci ko mene ne da aka ajiye a gabanku.
9 要醫治城中的病人,並給他們說:天主國已經臨近你們了。
Ku warkar da marasa lafiya da suke wurin. Ku kuma faɗa musu cewa, ‘Mulkin Allah yana kusa da ku.’
10 不論進了那座城,人如不接納你們,你們就出來,到街市上說:
Amma sa’ad da kuka shiga garin, kuma ba a karɓe ku ba, ku bi titi-titi ku ce,
11 連你們城中粘在我們腳上的塵土,我們也要給你們拂下來;但是你們當知道:天主的國已經臨近了。
‘Ko ƙurar garinku da kuke manne a ƙafafunmu, mun karkaɗe muku. Duk da haka, ku tabbatar da wannan, “Mulkin Allah yana kusa.”’
12 我告訴你們:在那一日,索多瑪所受的懲罰,要比這座城容易忍受。」
Ina dai faɗa muku, a ranan nan, za a fi jin tausayin Sodom fiye da wannan garin.
13 苛辣匝因啊,你是禍的了! 貝特賽達啊,你是禍的了! 因為在你們那裡所行的異能,如果行在提洛和漆冬,她們早已披上苦衣,坐在灰塵中,而改過自新了。
“‘Kaitonki, Korazin! Kaitonki, Betsaida!’ Ai, da a ce a Taya da Sidon ne aka yi ayyukan banmamaki da aka yi a cikinku, da tuni sun tuba, suna zama cikin rigar makoki da toka.
14 但是在審判時,提洛和漆冬所受的懲罰,要比你們容易忍受。
A ranar shari’a, za a fi jin tausayin Taya da Sidon fiye da ku.
15 還有你葛法翁啊! 莫非你要被高舉到天上嗎﹖將來你必被推下陰府。 (Hadēs )
Ke kuma Kafarnahum, kina tsammani za ki sami ɗaukaka ne? A’a, za a hallaka ki. (Hadēs )
16 聽你們的,就是聽我;拒絕你們的,就是拒絕我;拒絕我的,就是拒絕那派遺我的。」
“Wanda ya saurare ku, ni yake saurara. Wanda ya ƙi ku, ni yake ƙi. Amma wanda ya ƙi ni kuwa, ya ƙi wanda ya aiko ni ne.”
17 那七十二人歡喜地歸來,說:「主,因著你的名號,連惡魔都屈服於我們。」
Mutum saba’in da biyun nan suka dawo da murna, suka ce, “Ubangiji, har mun sha ƙarfin aljanu ma a cikin sunanka.”
18 耶穌向他們說:「我看見撒旦如同閃電一般自天跌下。
Sai ya amsa ya ce, “Na ga Shaiɗan ya fāɗi daga sama kamar walƙiya.
19 看我已經授於你們權柄,使你們踐踏在蛇蠍上,並能制伏仇敵的一切勢力,沒有什麼能傷害你們。
Na ba ku iko da za ku tattaka macizai, da kunamai, ku kuma shawo kan dukan ikon abokin gāba, kuma ba wani lahani da zai same ku.
20 但是,你們不要因為魔鬼屈服於你們的這件事而喜歡,你們應當喜歡的,乃是因為你們的名字,已經登記在天上了。
Duk da haka, kada ku yi farin ciki da cewa, kun sha ƙarfin ruhohi, amma ku yi farin ciki, domin an rubuta sunayenku a sama.”
21 就在那時刻,耶穌因聖神而歡欣說:「父啊! 天地的主宰,我稱謝你,因為你將這些事瞞往了智慧和明達的人,而啟示了給小孩子。是的,父啊! 你原來喜歡這樣做。
A wannan lokaci, Yesu, cike da murna ta wurin Ruhu Mai Tsarki ya ce, “Na yabe ka, ya Uba, Ubangijin sama da ƙasa, domin ka ɓoye waɗannan abubuwa ga masu hikima, da masu ilimi, ka kuma bayyana su ga ƙananan yara. I, ya Uba, gama wannan shi ne nufinka mai kyau.
22 我父將一都交給我,除了父,沒有一個認識子是誰,除了子及子所願啟示的人外,也沒有一個認識父是誰的。
“Ubana ya danƙa mini dukan kome. Ba wanda ya san Ɗan sai Uban, kuma ba wanda ya san Uban, sai Ɗan, da kuma waɗanda Ɗan ya zaɓa ya bayyana musu shi.”
23 耶穌轉過身來私下對們徒說:「見你們所見的眼睛是有福的。
Sai ya juya wajen almajiransa, ya ce musu a ɓoye, “Albarka ga idanun da suka ga abin da kuke gani.
24 我告訴你們:曾經有許多先知及君王希望看你們所見的,而沒有看見;聽你們所聽的,而沒有聽到。
Ina faɗa muku, annabawa da sarakuna da yawa sun so su ga abin nan da kuke gani, amma ba su gani ba. Sun so su ji abin da kuke ji, amma ba su ji ba.”
25 有一個法學士起來,試探耶穌說:「師傅,我應當做什麼,才能獲得永生﹖」 (aiōnios )
Wata rana, sai wani masanin dokoki ya miƙe tsaye don yă gwada Yesu. Ya tambaya ya ce, “Malam, me zan yi don in gāji rai madawwami?” (aiōnios )
26 耶穌對他說:「法律上記載了什麼﹖你是怎樣讀的﹖」
Yesu ya amsa ya ce, “Me aka rubuta a cikin Doka? Yaya kake karanta ta?”
27 他答說:「你應當全心,全靈,全力,全意愛上上,你的天主;並愛近人如你自己。」
Sai ya amsa ya ce, “‘Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan ƙarfinka, da kuma dukan hankalinka’; kuma, ‘Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.’”
28 耶穌向他說:「你答應的對,你這樣做,必得生活。」
Yesu ya ce, “Ka amsa daidai. Ka yi haka, kuma za ka rayu.”
29 但是,他願意顯示自己理直,又對耶穌說:「畢竟誰是我的近人﹖」
Amma domin ya kāre kansa, sai ya tambayi Yesu ya ce, “Shin, wane ne maƙwabcina?”
30 耶穌答說:「有一個人從耶路撒冷下來,到了耶利哥,遭遇了強盜;他們剝去他的衣服,並加以擊傷,將他半死半活地丟下走了。
Yesu ya amsa ya ce, “Wani mutum ya tashi daga Urushalima za shi Yeriko, sai ya fāɗi a hannun mafasa, wato,’yan fashi. Suka ƙwace tufafinsa, suka yi masa dūka, suka bar shi nan bakin rai da mutuwa.
31 正巧有一個司祭那條上下來,看了看他,便從旁邊走過去。
Ya zamana wani firist ya bi kan wannan hanya. Da ya ga mutumin, sai ya bi gefe ya wuce abinsa.
32 又有一個肋未人,也是一樣;他到了那裡,看了看他,也從旁邊走過去。
Haka ma wani daga kabilar Lawi, mai hidima cikin haikali, da ya zo wurin, ya gan shi, sai shi ma ya bi gefe ɗaya, ya wuce abinsa.
33 但有一個撒馬利亞人,路過他那裏,一看見就動了憐憫的心,
Amma wani mutumin Samariya da yake kan tafiya, da ya kai inda mutumin yake, ya gan shi, sai ya ji tausayinsa.
34 遂上前,在他的傷處注上油與酒,包紮好了,又扶他騎上自己的牲口,把他帶客店裏,小心照料他。
Ya je wurinsa, ya daddaure masa raunukansa, sa’an nan ya zuba mai, da ruwan inabi. Ya ɗauki mutumin ya sa a kan jakinsa, ya kai shi wani masauƙi, ya yi jinyarsa.
35 第二天,取出兩個銀錢交給店主說:請你小心看護他! 不論餘外花費多少,等我回來時,必要補還你。
Kashegari, sai ya ɗauki dinari biyu, ya ba wa mai masauƙin ya ce, ‘Ka lura da shi, bayan na dawo, zan biya ka duk abin da ka ƙara kashewa a kansa.’
36 你以為這三個人中,誰是那遭遇那強盜的近人呢﹖
“A ganinka, a cikin waɗannan mutane uku, wane ne maƙwabcin mutumin da ya fāɗi a hannun mafasa?”
37 那人答說:「是憐憫他的那人。」耶穌遂給他說:「你去也照樣做吧! 」
Masanin dokoki ya amsa ya ce, “Wanda ya nuna masa jinƙai.” Yesu ya ce masa, “Je ka, ka yi haka nan.”
38 他們走路的時候,耶穌進了一個村莊。一個名叫瑪爾大的女人,把耶穌接到家中。
Yayinda Yesu da almajiransa suna cikin tafiya, sai ya kai wani ƙauye inda wata mace mai suna Marta ta marabce shi a gidanta.
39 她有一個妹妹,名叫瑪利亞,坐在主的腳前聽祂講話。
Tana da’yar’uwa mai suna Maryamu, wadda ta zauna a gaban Ubangiji tana jin maganarsa.
40 瑪爾大為伺候耶穌,忙碌不已,便上前來說:「主! 我妹妹丟下我一個人伺候,你不介意嗎﹖請叫她來幫助我吧! 」
Marta kuwa, aikin hidima da ya kamata a yi, ya ɗauke mata hankali, sai ta zo wurin Yesu, ta ce, “Ubangiji, ba ka damu da yadda’yar’uwata ta bar mini aiki ni kaɗai ba? Gaya mata ta taimake ni!”
41 主回答她說:「瑪爾大,瑪爾大! 妳為了許多事操心忙碌,
Amma Ubangiji ya amsa ya ce, “Marta, Marta, hankalinki ya tashi, kuma kina damuwa a kan abubuwa da yawa.
42 其實需要的惟有一件。瑪利亞揀選了更好的份,一是不能從她奪去的。」
Amma abu ɗaya tak ake bukata, Maryamu ta zaɓi abin da ya fi kyau, kuma ba za a raba ta da shi ba.”