< 利未記 3 >
1 若有人奉獻和平祭,如所獻的是牛,應在上主面前獻一頭無瑕的公牛或母牛,
“‘In hadayar wani mutum, hadaya ta salama ce, ya kuma miƙa’yar dabba daga garke, ko namiji ko ta mace ce, sai yă miƙa dabbar da ba ta da lahani a gaban Ubangiji.
2 先按手在犧牲頭上,後在會幕門口宰了;亞郎的兒子司祭們,將血灑在祭壇四週。
Yă kuma ɗibiya hannunsa bisa kan hadayarsa, yă yanka ta a mashigin Tentin Sujada. Sa’an nan’ya’yan Haruna waɗanda suke firistoci za su yayyafa jinin a kan bagade a kowane gefe.
3 由和平犧牲中,應取出獻與上主做火祭的是:遮蓋內臟的脂肪,和貼在內臟上所有的脂肪,
Daga hadaya ta zumuncin da zai kawo, sai a miƙa waɗannan hadayu na ƙonawa ga Ubangiji a wuta; wato, dukan kitsen da ya rufe kayan ciki ko kuwa da sun shafe su,
4 左右兩腎和兩腎靠腰部的脂肪,以及兩腎一起取出的肝葉。
da ƙodoji biyu tare da kitsen da yake kansu kusa da kwiɓi, da kuma murfin hanta waɗanda zai cire tare da ƙodoji.
5 亞郎的兒子們應將這一切放在祭壇上的柴火上,同全燔祭犧牲一起焚燒,作為中悅上主的馨香火祭。
’Ya’yan Haruna za su ƙone shi a kan bagade a bisa hadaya ta ƙonawa wadda take a kan itacen da yake cin wuta, kamar hadayar da ka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.
6 若有人給上主奉獻一隻羊作和平祭犧牲,應奉獻一隻無瑕的公羊或母羊。
“‘In ya miƙa dabba ce daga garke a matsayin hadaya ta salama ga Ubangiji, zai miƙa namiji ko ta mace marar lahani.
In ya miƙa ɗan rago ne, zai kawo shi a gaban Ubangiji.
8 先按手在犧牲頭上,後會在會幕前宰了;亞郎的兒子將血灑在祭壇四週。
Zai ɗibiya hannu a kan hadayarsa, yă yanka shi a gaban Tentin Sujada. Sa’an nan’ya’yan Haruna maza za su yayyafa jinin dabbar a kowane gefe na bagade.
9 那人由和平祭犧牲中應取出脂肪作獻與上主的火祭:即靠脊骨割下的整個肥尾,遮蓋內臟的脂肪,貼在內臟上所有的脂肪,
Daga hadaya ta zumuncin zai kawo, sai a miƙa waɗannan hadayu na ƙonawa ga Ubangiji a wuta, wato, kitsen, ƙibabbiya wutsiyar gaba ɗaya da ya yanka gab da ƙashin gadon baya, dukan kitsen da ya rufe kayan ciki, ko kuwa da suka shafe su,
10 左右兩腎和兩腎靠腰部的脂肪,以及兩腎一起取出的肝葉。
da ƙodoji biyu tare da kitsen da yake kansu kusa da kwiɓi, da kuma murfin hanta waɗanda zai cire tare da ƙodoji.
11 司祭應將這一切放在祭壇上焚燒,有如食物,作為獻與上主的火祭。
Firist zai ƙone su a kan bagade kamar hadayar abinci, wato, hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji.
12 如果奉獻的祭品是一隻山羊,應將他牽到上主前,
“‘In yana miƙa akuya ce, zai kawo ta a gaban Ubangiji.
13 先按手在犧牲頭上,後會在會幕前宰了;亞郎的兒子將血灑在祭壇四週。
Zai ɗibiya hannunsa a kanta yă kuma yanka ta a gaban Tentin Sujada. Sa’an nan’ya’yan Haruna maza za su yayyafa jininta a kowane gefe na bagade.
14 那人由犧牲中應取出獻與上主作火祭的是:遮蓋內臟的脂肪,貼在內臟上所有的脂肪,
Daga abin da zai miƙa sai a miƙa waɗannan hadayu na ƙonawa ga Ubangiji a wuta, wato, dukan kitsen da ya rufe kayan cikin, ko kuwa da suka shafe su,
15 左右兩腎和兩腎靠腰部的脂肪,以及兩腎一起取出的肝葉。
da ƙodoji biyu tare da kitsen da yake kansu kusa da kwiɓi, da kuma murfin hanta waɗanda zai cire tare da ƙodoji.
16 司祭應將這一切放在祭壇上焚燒,有如食物,作為中悅上主的馨香火祭。
Firist zai ƙone su a kan bagade kamar abinci, hadaya ce da aka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi. Dukan kitsen na Ubangiji ne.
17 一切脂肪應歸於上主。凡是脂肪和血,你們都不可吃:這為你們世世代代,在你們任何所居之地,是一條永久的法令。
“‘Wannan dawwammamiyar farilla ce ga tsararraki masu zuwa, a inda za ku zauna. Ba za ku ci wani kitse ko wani jini ba.’”