< 利未記 27 >
2 你告訴以色列子民說:若人以人身許願,應將人身的代價獻給上主,
“Ka yi magana da Isra’ilawa, ka ce musu, ‘Duk sa’ad da mutum ya yi rantsuwa ta musamman zai keɓe wani ga Ubangiji, ta wurin biyan kuɗaɗen fansa,
3 二十隧道六十歲的男人,根據聖所的」協刻耳「,估價應是五十銀」協刻耳「;
ga yadda ma’aunin biyan zai kasance, mutum mai shekara tsakanin ashirin da sittin, za a biya azurfa hamsin.
Mace kuma za a biya azurfa talatin.
5 由五歲到二十歲,若是男性,估價應是二十」協刻耳「,女性為十」協刻耳「。
Saurayi mai shekara tsakanin biyar da ashirin, za a biya azurfa ashirin, yarinya kuma azurfa goma.
6 由一月到五歲,若是男性,估價為五銀」協刻耳「;若是女性,估價為三銀」協刻耳「。
Yaro mai shekara tsakanin wata ɗaya da shekara biyar, za a biya azurfa biyar,’yar yarinya kuma azurfa uku.
7 六十歲以上的人,若是男性,估價為十五」協刻耳「,女性為十」協刻耳「。
Namijin da ya fi shekara sittin, za a biya azurfa goma sha biyar, mace kuma azurfa goma.
8 但若是人窮,不能支付這估價,應帶他到司祭面前。司祭估定他的價格;司祭要按許願人的財力,估定價格。獸類的估價
In mai alkawarin matalauci ne da ba zai iya biyan ƙayyadadden abin da aka tsara ba, sai yă tafi wurin firist, shi firist kuma yă duba yadda mutumin da ya yi alkawarin zai iya biya. Sa’an nan mutumin zai biya abin da firist ya faɗa.
9 如所許的是可獻於上主作祭品的獸類獻於上主的任何走獸,應視為聖的,
“‘In abin da ya yi alkawarin yardajje ne a matsayin hadaya ga Ubangiji, wannan dabbar da aka bayar ga Ubangiji, za tă zama mai tsarki.
10 不可更換,不可替代,不能以好換壞,或以壞換好;如果人拿一隻走獸還另一隻,以前所許的和以後所換的,都應視為聖的。
Kada yă yi musayarta ko yă yi musaya mai kyau da marar kyau, ko marar kyau da mai kyau; in lalle ne yă yi musayar dabbar da wata, to, duk wannan da kuma wanda zai yi musayar da ita za su zama masu tsarki.
11 如所許的是一隻不潔,不堪獻於上主作祭品的走獸,就應將牠牽到司祭前,
In abin da ya yi alkawari dabba ce marar tsarki, wadda ba yardajje ba ce, a matsayin hadaya ga Ubangiji, dole a kai dabbar wa firist,
wanda zai yanke hukunci dacewarta, ko mai kyau ce, ko marar kyau. Duk darajar da firist ya kimanta, haka za tă zama.
13 如許願的人願把牠贖回,除了司祭估定的價值外,還應加五分之一。[房屋的估價]
In mai shi yana so yă fanshi dabbar, dole yă ƙara kashi ɗaya bisa biyar na darajarta.
14 若人把自己的房屋,獻於上主,司祭應估定它的好壞;司祭估多少,就是多少。
“‘In mutum ya miƙa gidansa a matsayin wani abu mai tsarki ga Ubangiji, firist zai daidaita dacewar ko mai kyau ne, ko marar kyau. Duk darajar da firist ya kimanta, haka za tă zama.
15 如果獻房屋的人願再贖回,除估定的價值外,還應加五分之一,房屋才可歸他。[田地的估價]
In mutumin da ya keɓe gidansa ya fanshe shi, dole yă ƙara kashi ɗaya bisa biyar na darajar, gidan kuma zai zama nasa.
16 若人將自己的一部份田產獻於上主,估價應按地播種所需要的數量;一」荷默爾「大麥種子,為五十銀」協刻耳「。
“‘In wani ya keɓe wa Ubangiji wani sashe daga cikin gonarsa ta gādo, sai yă kimanta kuɗin gonar daidai da yawan irin da za a iya shuka a gonar. Za a kimanta kuɗin a kan shekel hamsin na irin sha’ir.
17 若人由喜年起,獻了自己的田地,這個估價就是定價;
In ya keɓe gonarsa a Shekara ta Murna, darajar da aka kimanta za tă zauna.
18 但如果在喜年以後獻自己的田地,司祭應按至喜年尚餘的數量給他估價,把估價減低。
Amma in ya keɓe gonar bayan Shekara ta Murnan, firist zai kimanta darajar bisa ga yawan shekarun da suka rage har zuwa Shekara ta Murna mai zuwa, sai a rage darajar da aka kimanta a kanta.
19 如獻田地的人再願贖回,除司祭估定的價錢之外,還應加五分之一,田地仍歸於他;
In mutumin da ya keɓe gonar, yana so yă fanshe ta, to, dole yă ƙara kashi ɗaya bisa biyar na darajarta, gonar kuwa tă zama nasa.
20 但若他不但沒有把田地贖回反而賣給別人,不能再贖回;
In kuma bai fanshe gonar ba, ko kuwa in ya sayar wa wani dabam, ba za a taɓa fanshe ta ba.
21 一到喜年,田地應退還時,應獻於上主,當作禁田,歸於司祭,成為他的產業。
Sa’ad da aka saki gonar a Shekara ta Murna, za tă zama mai tsarki, a matsayin gonar da aka miƙa ga Ubangiji, za tă zama mallakar firistoci.
“‘In mutum ya keɓe gonar da ya saya, wadda take ba sashe na gonar iyali ba, ga Ubangiji,
23 司祭就應估定這田地直到喜年所有的價值,那人應在當天支付你估定的價錢,這是歸上主的聖物。
firist zai kimanta darajarta har Shekara ta Murna, dole kuma mutumin yă biya darajarta a ranar, a matsayin wani abu mai tsarki ga Ubangiji.
24 一到喜年,這田地應退給賣田的人,歸於這塊田地的原有人。
A Shekara ta Murna ɗin, gonar za tă dawo ga mutumin da aka saye ta daga wurinsa, wanda yake mai gonar.
25 一切估價都應按聖所的」「協刻耳」;一「協刻耳」等於二十「革辣」。[頭胎牲畜]
A kimanta kowace daraja bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, gera ashirin ga shekel.
26 至於頭胎牲畜,既是頭胎,應屬於上主,人不能再奉獻;不論是牛是羊,以屬於上主。
“‘Ba wani da zai iya keɓe ɗan farin dabba, da yake ɗan fari ya riga ya zama na Ubangiji, ko na saniya, ko na tunkiya, na Ubangiji ne.
27 若是不潔牲畜的頭胎,人應照估價贖回,再加五分之一;如不贖回,應照估價賣掉。[禁物]
In tana cikin dabbobin da suke marasa tsarki, zai iya saye ta a darajar da aka kimanta, yă ƙara da kashi ɗaya bisa biyar na darajarta. In bai fanshe ta ba, sai a sayar da ita a darajar da aka kimanta.
28 凡照禁物法獻於上主之物,凡人所有的,不論是人,或是牲畜,或是一部份田產,便不可變賣,亦不可贖回;凡禁物都是屬於上主得至聖之物。
“‘Amma babu abin da mutum ya mallaka, ya kuma keɓe ga Ubangiji, ko mutum ne, ko dabba, ko ganar iyali da za a sayar, ko a fansa; kome da aka keɓe a wannan hanya, mafi tsarki ne ga Ubangiji.
29 凡照禁物法應處置的人,便佈可贖回,應將他處死。[什一之物]
“‘Babu wani da aka keɓe don hallaka da za a fansa; dole a kashe shi.
30 凡土地的出產,或是田地的穀物,或是樹木的果實,十分之一應歸於上主,是獻於上主的聖物。
“‘Ushirin kome daga gona, ko hatsi daga ƙasa, ko’ya’yan itatuwa daga itatuwa, na Ubangiji ne, mai tsarki ne ga Ubangiji.
31 人若願意把應獻的十分之一贖回一部份,除物價外,應另加五分之一。
In mutum ya fanshi wani zakansa, dole yă ƙara kashi ɗaya bisa biyar na darajar.
32 凡牛群或羊群,由牧童杖下經過的每第十隻,亦即全群十分之一,應獻於上主;
Ushirin gaba ɗaya na garken shanu, da na tumaki, kowane kashi ɗaya bisa goma na dabbar da ta wuce ƙarƙashin sandan mai kiwo, za tă zama mai tsarki ga Ubangiji.
33 不應追究是好是壞,亦不可將牠更換;更換了,以前所有的和以後所換的,都應視為聖物,不得贖回」。
Kada kuwa ya zaɓa mai kyau daga marar kyau, ko yă yi musaya. In ya yi musaya kuwa, dabbar da wadda ya musayar, za su zama masu tsarki, ba kuma za a fanshe su ba.’”
34 這是上主在西乃山為以色列子民向梅瑟吩咐的法令。
Waɗannan su ne dokokin da Ubangiji ya ba wa Musa a Dutsen Sinai saboda Isra’ilawa.