< 約書亞記 22 >

1 那時若蘇厄將勒烏本人加特人和默納協半支派的人召來,
Yoshuwa ya kira mutanen Ruben, mutanen Gad, da rabin kabilar Manasse
2 對他們說:「上主僕人梅瑟吩咐你們的一切,你們都遵守了,在我吩咐他們的一切事上,你們也都聽了我的話。
ya ce musu, “Kun yi duk abin da Musa bawan Ubangiji ya umarta, kun kuma yi mini biyayya cikin dukan umarnan da na ba ku.
3 這許多日子,你們從來沒有你們的的弟兄,直到今天,忠信遵守了上主你們天主的命令。
Dukan waɗannan yawan kwanaki, har zuwa yau, ba ku yashe’yan’uwanku Isra’ilawa ba, amma kuka kiyaye umarnin da Ubangiji Allahnku ya ba ku.
4 現在上主我們的天主,照衪所應許的,使你們的弟兄獲得了安居,你們現在可返回自己的帳幕,回到上主的僕人梅瑟在約旦河東岸,賜你們為產業的地方去,
Yanzu da Ubangiji Allahnku ya ba’yan’uwanku hutu kamar yadda ya yi alkawari, sai ku koma gidajenku a ƙasar da Musa bawan Ubangiji ya ba ku a Urdun.
5 只要要你們遵守上主的僕人梅瑟吩咐你們的誡命和法律:愛慕上主你們的天主,遵行衪的一切道路,謹守衪的誡命,全心人靈歸屬上主,服事上主。」
Amma ku yi hankali, ku kiyaye umarnai da kuma dokokin da Musa bawan Ubangiji ya ba ku. Ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku, ku yi tafiya kan hanyarsa, ku yi biyayya da umarnansa, ku riƙe shi sosai, ku bauta masa da dukan zuciyarku da kuma dukan ranku.”
6 若蘇厄於是祝福了他們,打發他們回去;他們就返回了自己的帳幕。──
Sai Yoshuwa ya sa musu albarka, ya sallame su, suka kuwa tafi gidajensu.
7 梅瑟在巴商已分給了默納協半支派土地。至於另半個支派,若蘇厄在約旦河西,在他們的弟兄中,也分給了他們土地,此外,當若蘇厄打發他們回帳幕的時候,祝福了他們,
(Musa ya riga ya ba rabin kabilar Manasse gādo a Bashan; sauran rabin kabilar kuma Yoshuwa ya ba su gādo tare’yan’uwansu a yammacin hayin Urdun.) Sa’ad da Yoshuwa ya sallame su su tafi gida, ya sa musu albarka,
8 向他們說:「現在你們帶著這許多財物、牛、羊、金銀、銅鐵,和大批衣服回到自己的帳幕,也要將你們從由敵人奪得的財物,分給你們的弟兄! 」
ya ce, “Ku koma gidajenku tare da dukiya mai yawa, babban garken dabbobi, azurfa da zinariya, tagulla da ƙarfe, da tufafi masu yawa sosai, sai ku raba ganimar da kuka samu daga abokan gābanku, da’yan’uwanku.”
9 勒烏本人、召集人和默納協半支派的人,於是從客納罕的史羅起身,離開以色列人,回到自己得為產業的基肋阿得,即上主藉梅瑟吩咐給他們作為產業的地方。
Saboda haka sai mutanen Ruben, mutanen Gad da kuma rabin mutanen kabilar Manasse, suka bar Isra’ilawa a Shilo cikin Kan’ana don su koma Gileyad, ƙasarsu, wadda suka samu bisa ga umarnin Ubangiji ta wurin Musa.
10 當勒烏本人、加得和默納協半支派的人來到屬客納罕地的約旦河附近地區時,在約旦河邊築了一座祭壇,一座高大可觀的祭壇。
Da suka kai Gelilot kusa da Urdun cikin ƙasar Kan’ana, sai mutanen Ruben, mutanen Gad da kuma rabin mutanen kabilar Manasse suka gina bagade a can, a Urdun.
11 以色列人聽見說:「看,勒烏本人、加得人和默納協半支派的人,在屬客納罕地的約旦河附近地區,以色列子民境內,築了一座祭壇。」
Sa’ad da Isra’ilawa suka ji cewa sun gina bagade a iyakar Kan’ana, a Gelilot kusa da Urdun wajen gefensu na Isra’ilawa,
12 以色列子民一聽說這事,全會眾便聚集在史羅,要去作戰攻打他們。
sai dukan Isra’ilawa suka taru a Shilo don su je su yaƙe su.
13 以色列子民便委派厄肋阿匝爾的兒子丕乃哈斯司祭,到基肋阿得地方去見勒烏本人、加得人和默納協半支派人,
Saboda haka sai Isra’ilawa suka aiki Finehas ɗan Eleyazar, firist, zuwa ƙasar Gileyad, wurin mutanen Ruben, mutanen Gad da kuma rabin mutanen kabilar Manasse.
14 和他們同去的尚有十位領袖,每支派一個,他們都是以色列各家族的族長。
Suka aiki shugabanni guda goma su tafi tare da shi, ɗaya daga kowace kabilar Isra’ila, kowannensu shugaba ne a iyalansa.
15 他們來到基肋阿得地方,見勒烏本人、加得人和默納協半支派人,向他們說:
Sa’ad da suka je Gileyad, wurin mutanen Ruben, mutanen Gad da kuma rabin mutanen kabilar Manasse, sai suka ce musu,
16 「上主的全會眾這樣說:你們相反以色列的天主,犯這不信的罪,有什麼意思﹖為什麼你們今天離開上主,另建立祭壇,公開背叛上主﹖
“Dukan jama’ar Ubangiji sun ce yaya za ku juya wa Allah na Isra’ila baya haka? Yaya za ku daina bin Ubangiji ku gina wa kanku bagade, ku yi masa tawaye yanzu?
17 以前敬拜培敖爾的罪萵為我們還不夠嗎﹖為了那個罪過,災禍降於上主的會眾,直到今天,我們還沒洗淨:
Zunubin da Feyor ya yi bai ishe mu ba ne? Ga shi, har yanzu ba mu gama tsarkakewa daga wannan zunubi ba, ko da yake annoba ta auko wa mutanen Ubangiji!
18 看,你們今天又要離開上主,你們今天違背上主,明天衪必向以色列全會眾發怒。
Yanzu za ku daina bin Ubangiji ne? “In kuka yi wa Ubangiji tawaye yau, gobe zai yi fushi da dukan mutanen Isra’ila.
19 如果你們認為所得的地方不潔,可以回到上主的地方,上主帳幕的所在地,住在我們中間;決不可違背上主,激怒我們,在上主我們的祭壇以外,為自己另築祭壇。
Idan ƙasar mallakarku ƙazantacciya ce, sai ku haye zuwa ƙasar Ubangiji, inda tabanakul yake, mu zauna tare. Amma kada ku yi wa Ubangiji, ko kuma ku yi mana tawaye ta wurin gina wa kanku bagade wanda ba na Ubangiji Allahnmu ba.
20 以前則辣黑的子孫阿干,在應毀滅的財物上犯了不忠之罪,雖只他一人犯罪,憤怒豈不是臨到以色列全會眾﹖死在他罪過中的不只他一人」。
Lokacin da Akan ɗan Zera ya yi rashin aminci game da kayan da aka keɓe, fushinsa Ubangiji bai auko a kan mutanen Isra’ila duka ba? Ai, ba shi kaɗai ya mutu don zunubinsa ba.”
21 勒烏本人、加得和默納協半支派的人,回答以色列的首長說:
Sai mutanen Ruben, mutanen Gad da kuma rabin mutanen kabilar Manasse suka amsa wa shugabannin iyalan Isra’ila suka ce,
22 「大能者天主上主,大能者天主上主清楚知道,以色列也明白:如果我們有違背或干犯上主的事,願衪今天別救我們!
“Maɗaukaki, Allah, Ubangiji! Maɗaukaki, Allah, Ubangiji ya sani! In mun yi wannan cikin tawaye ko rashin biyayya ga Ubangiji ne, kada ku bar mu da rai yau.
23 如果我們建築這祭壇,有意離開上主,或有意在祭壇上祭全燔祭、素祭或和平祭,願上主自己懲罰我們!
Idan mun bar bin Ubangiji, muka gina wa kanmu bagade don mu miƙa hadayun ƙonawa, ko kuwa hadayun gari, ko kuwa hadayun salama, to, bari Ubangiji kansa ya sāka mana.
24 我們做這事,其實正是顧慮到:將來你們的子孫會對我們的子孫說:你們和上主以色列的天主有什麼關係﹖
“A’a! Mun yi haka ne don tsoro, kada nan gaba’ya’yanku su ce wa’ya’yanmu, ‘Me ya haɗa ku da Ubangiji, Allah na Isra’ila?
25 天主定了約旦河為我們和你們勒烏本和和得人之間的界限,你們和上主已沒有分子。這樣你們的子孫必使我們的的子孫不再敬畏上主。
Ubangiji ya sa Urdun ya zama iyaka tsakaninmu da ku, ku mutanen Ruben da mutanen Gad! Ba ku da rabo cikin Ubangiji.’’Ya’yanku za su iya sa’ya’yanmu su daina tsoron Ubangiji.
26 因此我們想:我們還是建築一座祭壇,不是為獻全燔祭,也不是為祭獻犧牲,
“Shi ya sa muka ce, ‘Bari mu yi shiri mu gina bagade, amma ba na ƙona hadayu ko na sadaka ba.’
27 只是為在你我之間,在你我後人之間作一證據,證明我們願在上主面前以全燔祭犧牲及和平祭敬禮上主,免得日後你們的子孫對我們的子孫說:你們與上主已沒有分子o
Sai dai yă zama shaida tsakaninmu da ku, da kuma waɗanda za su zo a baya, cewa za mu yi wa Ubangiji sujada a wurinsa mai tsarki, za mu miƙa hadayunmu na ƙonawa, hadayu na zumunta. Sa’an nan, nan gaba’ya’yanku ba za su ce wa’ya’yanmu, ‘Ba ku da rabo a cikin Ubangiji ba.’
28 因此我們想:日後如有人對我們或我們的子孫說,我們可以說:你們試看我們的祖先所築的上主的祭壇的式樣,不是為獻全燔祭,也不是為獻犧牲,而是為作你我之間的證劇。
“Muka kuma ce, ‘In har suka ce mana, ko’ya’yanmu haka, sai mu amsa mu ce ku dubi bagaden da yake daidai da na Ubangiji wanda iyayenmu suka gina, ba don ƙona hadayu da kuma yin sadaka ba, sai dai don yă zama shaida tsakaninmu da ku.’
29 我們今天沒有意思違背上主,離開上主,在上主我們天主的帳幕前的祭壇以外,為獻全墦祭、素祭和犧牲,另建立一祭壇。」
“Allah ya sawwaƙa mana mu tayar wa Ubangiji mu bar binsa, har mu gina bagade don miƙa hadayu na ƙonawa, da na gari, da na sadaka, ban da bagaden Ubangiji Allahnmu wanda yake tsaye a gaban tabanakul.”
30 司祭丕乃哈斯和同他同來的會眾的首領,即以色列人的族長,聽了勒烏本人、加得人和默納協人所的話,都表示滿意。
Da Finehas firist, da shugabannin mutanen, shugabannin iyalan Isra’ila, suka ji abin da mutanen Ruben, mutanen Gad da kuma rabin mutanen kabilar Manasse suka ce, sai suka ji daɗi.
31 厄肋阿則爾的兒子丕乃哈司祭對勒烏本人、加得人和默納協人說:「今天我們知道上主是在我們中間,因為你們對上主沒有犯過這樣不忠信的罪,現在你們由上主手中救了以色列子民。」
Sai Finehas ɗan Eleyazar, firist, ya ce wa mutanen Ruben, mutanen Gad da kuma rabin mutanen kabilar Manasse, “Yau mun san Ubangiji yana tare da mu, domin ba ku yi wa Ubangiji rashin aminci cikin wannan abu ba. Yanzu kun kuɓutar da Isra’ilawa daga hannun Ubangiji.”
32 厄肋阿則爾的兒子丕乃哈司祭和首領便離開勒烏本人、加得人和默納協半支派的人,從基肋阿得地方回到客納罕地見以色列子民,給他們報告了這事。
Sai Finehas ɗan Eleyazar, firist, da shugabannin suka koma Kan’ana daga saduwa da mutanen Ruben da mutanen Gad a Gileyad, suka kai wa Isra’ilawa rahoto.
33 以色列子民對這報告都表示滿意,遂頌揚上主,不再想作戰攻打勒烏本人和加得人,毀滅他們所住的地方。
Isra’ilawa suka ji daɗin rahoton da suka ji, suka kuma yi wa Allah yabo. Ba su sāke yin maganar zuwa yaƙi don su rushe ƙasar da mutanen Ruben da mutanen Gad suke ciki ba.
34 勒烏本人和加得人給那祭壇起名叫「赫得,」因為他們說:「這祭壇在我們中間證明上主是真天主。」
Sai mutanen Ruben da mutanen Gad suka ba wa wannan bagaden sunan, Shaida Tsakaninmu, cewa Ubangiji Allah ne.

< 約書亞記 22 >