< 約書亞記 1 >
1 上主的僕人梅瑟死了以後,上主對農的兒子,梅瑟的待從若蘇厄說:
Bayan mutuwar Musa bawan Ubangiji, sai Ubangiji ya ce wa Yoshuwa ɗan Nun, mataimakin Musa,
2 「我的的僕人梅瑟死了,你現在起來,和全體百姓萵約旦河,往我賜給他們,即以色列子民的地方去。
“Bawana Musa ya mutu. Yanzu sai ka tashi tare da mutanen nan duka, ku yi shirin ƙetare kogin Urdun zuwa cikin ƙasar da zan ba su Isra’ilawa.
3 凡你們的腳踏過的地方,照我對梅瑟說的,我必賜給你們;
Zan ba ku duk ƙasar da za ku taka, kamar yadda na yi wa Musa alkawari.
4 從曠野直到黎巴嫩,由大河,即幼發拉的河,赫特人的全境,直到大海日落之地,都是你們的領土。
Ƙasar da ta kama daga hamada zuwa Lebanon, zuwa babban Kogin, wato, Kogin Yuferites, da dukan ƙasar Hittiyawa zuwa Bahar Rum, wajen yamma.
5 你有生之日,沒有人能抵抗你;過去我怎樣和梅瑟同在,也要怎樣和你同在,決不捨棄你。
Ba wanda zai yi tsayayya da kai dukan kwanakin ranka. Yadda na kasance tare da Musa, haka zan kasance tare da kai; ba zan taɓa rabuwa da kai ba; ba zan yashe ka ba.
6 你應勇敢果斷,因為你必須使這百姓,佔領我曾向他們祖先起誓賜給他們作產業的地方。
“Ka yi ƙarfin hali ka kuma kasance da rashin tsoro, gama kai za ka bi da mutanen nan har su karɓi ƙasar da na yi wa kakanninsu alkawari zan ba su.
7 你只須勇敢,堅決果斷,不偏左右,謹守奉行我僕人梅瑟所吩咐你們的一切訓示,好使你無往不利。
Ka yi ƙarfin hali ka kuma kasance da rashin tsoro, ka yi lura fa, ka yi biyayya da dokokin da bawana Musa ya ba ka; kada ka kauce ga bin dokokin ko hagu ko dama, domin ka yi nasara a duk, inda za ka je.
8 這部法律書總不要離開你的口,你要日夜默想,好叫你能謹守奉行其中所記載的一切;這樣,你必能順利,必能成功。
Kada ka bar Littafin Dokokin nan yă rabu da bakinka, sai dai ka yi ta tunani game da shi dare da rana, don ka lura, ka yi duk abin da aka rubuta a ciki, ta haka ne za ka yi nasara cikin duk abin da za ka yi.
9 我不是吩咐了你,你應勇敢果斷嗎﹖所以你不要害怕,也不要膽怯,因為你無論到那裏,上主你的的天主必與你同在。」
Ba ni na umarce ka ba? Ka yi ƙarfin hali ka kuma kasance da rashin tsoro. Kada ka ji tsoro; kada ka karaya, gama Ubangiji Allahnka zai kasance tare da kai duk inda za ka je.”
Saboda haka sai Yoshuwa ya umarci shugabannin mutane,
11 「應走遍全營,吩咐百姓說:你們應準備食物,因為還有三天,就要過這約旦河,去佔領上主你的的天主賜與你的作產業的土地。
“Ku ratsa cikin sansani, ku gaya wa mutane, ‘Ku shirya guzurinku. Nan da kwana uku za ku ƙetare Urdun a nan, don ku je ka mallaki ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku ta zama taku.’”
12 若蘇厄又對勒烏本人、加得人和默納協半支派的人說:
Amma Yoshuwa ya ce wa mutanen Ruben, mutanen Gad da kuma rabin mutanen kabilar Manasse,
13 「你們應記起上主的僕人梅瑟吩咐你的的事。他說過:上主你的的天主將這地賜給你們,使你們獲得安居,
“Ku tuna da umarnin da Musa bawan Ubangiji ya yi muku. ‘Ubangiji Allahnku ya ba ku hutawa, ya kuma ba ku wannan ƙasa.’
14 你們的婦孺和牲畜,可留在梅瑟在約旦河東賜你的的地方;但你們中所有的英勇戰士,都應武裝起來,在你們弟兄前過河,協助他們,
Matanku, da yaranku, da kuma dabbobinku za su kasance a ƙasar da Musa ya ba ku a gabashin Urdun, amma dole mayaƙanku, su yi shirin yaƙi su haye, su yi gaba tare da’yan’uwanku, za ku taimaki’yan’uwanku
15 到直上主使你們的弟兄,像你們一樣,佔領了上主你們的天主,賜給他們作為產業的地方,即上主的僕人梅瑟在約旦河東,日出之地,賜予你們的地方。
har sai lokacin da Ubangiji ya ba su hutawa, kamar yadda ya yi muku, kuma har sai su ma sun ƙwace ƙasar da Ubangiji Allahnku ya yi alkawari zai ba su. Bayan haka ne za ku koma ku mallaki ƙasarku, wadda Musa bawan Ubangiji ya ba ku a gabashin Urdun.”
16 他們回答若蘇厄說:「凡你命令我們的,我們必都照辦;凡你派我們去的地方,我們一定去。
Sai suka amsa wa Yoshuwa suka ce, “Duk abin da ka ce mu yi, za mu yi. Duk inda kuma ka aike mu, za mu je.
17 我們在一切事上怎樣服從了梅瑟,也怎樣服從你;惟願上主你的的天主與你同在,如同與梅瑟同在一樣。
Kamar yadda muka yi wa Musa biyayya, haka za mu yi maka biyayya. Ubangiji Allahnka ya kasance tare da Musa.
18 無論誰違背你的命令,不服從你吩咐他的一切訓示,必處死刑。但你應該勇敢果斷。」
Duk wanda ya yi wa maganarka tawaye, ya ƙi yă yi biyayya da maganarka, ko da umarnin da ka ba shi, za a kashe shi. Ka dai ƙarfafa ka kuma yi ƙarfi hali!”