< 約拿書 2 >
Daga ciki cikin kifi, Yunana ya yi addu’a ga Ubangiji Allahnsa.
2 他說:「我在患難中,呼求上主,衪便應允了我,我從陰府的深處呼求,你便俯聽了我的呼聲。 (Sheol )
Ya ce, “A cikin damuwata na yi kira ga Ubangiji, ya kuwa amsa mini. Daga cikin zurfi kabari na yi kiran neman taimako, ka kuwa saurari kukata. (Sheol )
3 你將我拋入海心深處,大水包圍了我;你的波濤和巨浪漫過了我。
Cikin tashin hankali, ka jefa ni cikin zurfafa, a tsakiyar teku, ka kuma jujjuya ni a cikin ruwa; dukan raƙuman ruwanka da ambaliyarka sun bi ta kaina.
4 我曾說:我雖從你面前被拋棄,但我仍要瞻仰你的聖殿。
Sai na ce, ‘An kore ni daga fuskarka; duk da haka zan sāke duba wajen haikalinka mai tsarki.’
5 大水圍困我,危及卜性命;深淵包圍我,海草纏住我的頭。
Ruwayen da suke kewaye da ni sun yi mini barazana, zurfi kuma ya kewaye ni, ciyayin ruwa suna nannaɗe kewaye da ni.
6 我下深直到礁底,大地的門閂永為我關閉。上主,卜天主! 你卻從坑裏救出了我的性命。
Na nutsa har ƙarƙashin tuddai; a ƙarƙashin duniya, ka rufe ni har abada. Amma ka dawo da raina daga rami, Ya Ubangiji Allahna.
7 當我奄奄一息時,我記起了上主;我的祈禱達於你前,達於你的聖殿中。
“Sa’ad da na ji raina yana rabuwa da ni, na tuna da kai ya Ubangiji, addu’ata kuma ta kai gare ka, a haikalinka mai tsarki.
“Waɗanda suka maƙale wa gumaka marasa amfani, sukan ƙyale alherin da zai kasance nasu.
9 至於我,我要在頌謝的歌聲中,向你獻祭,償還我許的誓願。救恩屬於上主! 」
Amma ni, da waƙar godiya, zan miƙa tawa hadaya gare ka. Abin da na yi alkawari, shi ne zan yi. Ceto yakan zo ne kawai daga wurin Ubangiji.”
10 當時,上主命令那魚,那魚便將約納吐在陸地上。
Sai Ubangiji ya umarci kifin, kifin kuwa ya amayar da Yunana a gaɓan teku.