< 約翰福音 8 >
Yesu ya je Dutsen Zaitun.
2 清晨他又來到聖殿,眾百姓都到他跟前來,他便坐下教訓他們。
Da sassafe ya dawo Haikali, dukan mutane kuma suka zo wurin sa; yazauna koya masu.
3 那時,經師和法利賽人帶來了一個犯姦淫時被捉住的婦人,叫她站在中間,
Sai marubuta da Farisawa suka kawo mace wadda aka kama ta tana zina. Su ka sa ta a tsakiya.
4 便向耶穌說:「師傅! 這婦人是正在犯姦淫時被捉住的,
Sai su ka ce da shi, “Malam, wannan mace an kama ta tana cikin yin zina.
5 在法律上,梅瑟命令我們該用石頭砸死這樣的婦人;可是,你說什麼呢?」
A cikin shari'a, Musa ya bamu umurni mu jejjefe irin wandannan mutume, kai me ka ce game da ita?”
6 他們說這話,是要試探耶穌,好能控告他;耶穌卻彎下身去,用指頭在地上畫字。
Sun fadi haka ne domin su gwada shi su sami abinda za su zarge shi da shi, amma Yesu ya sunkuya yayi rubutu da yatsansa a kasa.
7 因為他們不斷地追問,他便直起身來,向他們說:「你們中間誰沒有罪,先向她投石罷! 」
Sa'adda suka cigaba da tambayar sa, ya mike tsaye yace masu, “shi wanda ba shi da zunubi a cikin ku, ya fara jifar ta da dutse.”
Ya sake sunkuyawa, ya yi rubutu da yatsansa a kasa.
9 他們一聽這話,就從年老的開始到年幼的,一個一個地都溜走了,只留下耶穌一人和站在那裡的婦人。
Da suka ji haka, sai suka fita dai-dai da dai-dai, kama daga babbansu. A karshe dai aka bar Yesu shi kadai, tare da matar wadda ta ke a tsakiyar su.
10 耶穌遂直起身來向說: 「婦人!他們在那裏呢?沒有人定你的罪嗎?」
Yesu ya tashi tsaye ya ce da ita, “mace, ina masu zargin ki? Ba wanda ya kashe ki?
11 她說: 「主!沒有人。」耶穌向她說: 「我也不定你的罪;去罷! 從今以後,不要再犯罪了! 」
Ta ce, “Ba kowa, Ubangiji” Yesu ya ce, “Ni ma ban kashe ki ba. Ki yi tafiyar ki, daga yanzu kada ki kara yin zunubi.”
12 耶穌又向眾人講說: 「我是世界的光;跟隨我的,決不在黑暗中行走,必有生命的光。」
Yesu ya kara yin magana da mutanen cewa, “Ni ne hasken duniya, shi wanda ya biyo ni, ba zai yi tafiya cikin duhu ba, amma za ya sami hasken rai.
13 法利賽於是對對他說: 「你為你自己作證,你的證據是不可憑信的。」
Farisawa suka ce masa, “Kana bada shaida a kan ka, shaidarka ba gaskiya ba ce.”
14 耶穌回答說:「我即便為我自己作證,我的證據是可憑信的,因為我知道:我從那裏來,往那裏去;你們卻不知道: 我從那裏來,或往那裏去。
Yesu ya amsa ya ce masu, “Ko ma na bada shaida a kai na, shaidata gaskiya ce, na san daga inda na fito da inda zan tafi, amma ku baku san daga inda na fito ba, baku kuma san inda zan tafi ba.
Kuna shari'a ta son kai, ni ko ban yi wa kowa shari'a ba.
16 即使我判斷,我的判斷仍是真實的,因為我不是獨自一個,而是有我,還有派遣我來的父。
Ko ma da na yi shari'a, shari'ata gaskiya ce domin ba ni kadai ba ne, amma ina tare da Uba wanda ya aiko ni.
17 在你們的法律上也記載著: 兩個人的作證是可憑信的。
I, a cikin dokarku an rubuta cewa shaidar mutum biyu gaskiya ce.
18 今有我為我自己作證,也有派遣我的父,為我作證。」
Ni ne ni ke shaidar kaina, kuma Uba wanda ya aiko ni ya na shaida ta.
19 他們使問他說: 「你的父在那裏?」耶穌答覆說:「你們不認識我,也不認識我的父;若是你們認識了我,也就認識我的父了。」
Su ka ce da shi, “Ina ubanka?” Yesu ya amsa ma su ya ce, “baku san ni ba balle Ubana, in da kun san ni da kun san Uba na kuma. “
20 這些話是耶穌於聖殿施教時,在銀庫院裏所講的。誰也沒有捉拿,因為的時辰還沒有到。
Ya fadi wadannan kalmomi a kusa da wurin ajiya sa'adda ya ke koyarwa a cikin haikali, kuma ba wanda ya kama shi saboda sa'arsa bata yi ba tukuna.
21 那時,耶穌又向他們說:「我去了,你們要尋找我,你們必要死在你們的罪惡中;我所去的地方,你們不能去。」
Ya kara cewa da su,”Zan tafi, za ku neme ni ba za ku same ni ba, za ku mutu cikin zunubinku. Inda ni ke tafiya, ba za ku iya zuwa ba”.
22 猶太人便說: 「他說: 我所去的地方,你你們不能去;莫非他要自殺嗎?」
Yahudawa su ka ce,”Zai kashe kansa ne, da ya ce inda ni ke tafiya ba za ku iya zuwa ba?”
23 耶穌向他們說: 「你們是出於下,我卻是出於上;你們是出於這個世界,我卻不是出於這個世界。
Yesu ya ce masu ku daga kasa kuke, Ni kuwa daga bisa ni ke. Ku na wannan duniya ne, Ni kuwa ba na wannan duniya ba ne.
24 因此,我對你們說過: 你但要死在你們的罪惡中。的確,你們若不相信我就是那一位,你們必要死在你們的罪惡中。」
Shiyasa na ce maku za ku mutu cikin zunubanku. In ba kun bada gaskiya NI NE ba, za ku mutu cikin zunubanku.
25 於是,他們問耶穌說: 「你到底是誰?」耶穌回答他們說: 「難道從起初我沒有對你們講論過嗎?
Sai kuma suka ce da shi,”Wanene kai?” Yesu ya ce masu, “Abin da na gaya maku tun daga farko.
26 對你們我有許多事要說,要譴責;但是派遣我來者是真實的;我由他聽來的,我就講給世界聽。」
Ina da a bubuwa da yawa da zan gaya maku, in kuma hukunta ku a kai. Duk da haka, wanda ya aiko ni, mai gaskiya ne, abubuwan da naji daga wurin sa, wadannan abubuwan su ni ke gaya wa duniya.”
Ba su gane ba yana yi masu magana a kan Uban.
28 耶穌遂說: 「當你們高舉了人子以後,你們便知道我就是那一位。我由我自己不作什麼;我所講論的,都是依照父所教訓我的。
Yesu ya ce, “Sa'adda kuka tada Dan Mutum sama sa'annan za ku gane NI NE, kuma ban yi komi domin kaina ba. Kamar yadda Uba ya koya mani, haka nike fadin wadannan abubuwa.
29 派遣我來者與我在一起,他沒有留下我獨自一個,因為我常作他所喜悅的事。」
Shi wanda ya aiko ni, yana tare da ni kuma bai bar ni ni kadai ba, domin kullum ina yin abubuwan da suke faranta masa rai.”
Sa'adda Yesu ya ke fadin wadannan abubuwa, dayawa suka bada gaskiya gare shi.
31 於是,耶穌對那些信他的猶太人說: 「你們如果固守我的話,就確是我的門徒,
Yesu ya gayawa wadancan Yahudawa da suka bada gaskiya gare shi, “Idan kun tsaya a cikin magana ta ku almajiraina ne na gaskiya,
Kuma za ku san gaskiya, gaskiya kuwa zata 'yantar da ku.”
33 他們回答說: 「我們是亞巴郎的後裔,從未給人做過奴隸;怎麼你說:你們要成為自由的呢?」
Suka amsa masa, “Mu zuriyar Ibrahim ne kuma bamu taba yin bauta wurin kowa ba, yaya za ka ce, 'Za a 'yantar da ku'?”
34 耶穌答覆說: 「我實實在在告訴你們: 凡是犯罪的,就是罪惡的奴隸。
Yesu ya ce masu, “Hakika, hakika, ina ce maku, dukan wanda ya ke aika zunubi bawan zunubi ne.
35 奴隸不能永遠住在家裏,兒子卻永遠居住。 (aiōn )
Bawa kuwa, ba ya zama a gida dindindin, da yana zama dindindin. (aiōn )
36 那麼,如果天主子使你們自由了,你們的確是自由的。
Saboda haka, idan Dan ya 'yantar da ku zaku zama 'yantattu sosai.
37 我知道你們是亞巴郎後裔,你們圖謀殺害我,因為你們容納不下我的話。
Na san ku zuriyar Ibrahim ne, kuna so ku kashe ni saboda kalma ta bata da wurin zama a cikin ku.
38 我說的,是我在父那裏所看見的;而你們行的,卻是你們從你們的父那裏所學習的。」
Na fadi abubuwan da na gani a wurin Ubana, ku kuma kuna yin abubuwan da kuka ji daga wurin ubanku.”
39 他們回答說: 「我們的父是亞巴郎。」耶穌對他們說: 「假如你們是亞巴郎的子女,你們就該作啞巴郎的事。
Suka amsa suka ce masa, “Ibrahim ne ubanmu” Yesu ya ce masu, “Da ku 'yayan Ibrahim ne da kun yi ayukan da Ibrahim ya yi.
40 如今,你們竟圖謀殺害我──這個給你們說出從天主那裏所聽到的真理的人──亞巴郎卻沒有做過言這樣的事。
Amma, yanzu kuna so ku kashe ni, mutumin da ya gaya maku gaskiyar da ya ji daga wurin Allah. Ibrahim bai yi haka ba.
41 你們正做你們父親的事業。」他們向他說:「我們不是由淫亂生的,我們只有一個父親: 就是天主。」
Kuna yin ayyukan ubanku. Suka ce masa, “mu ba a haife mu cikin fasikanci ba, muna da Uba daya: Allah.”
42 耶穌回答說:「假如天主是你們的父親,你們必愛我,因為我是由天主出發而來的,並不是由我自己來的,而是那一位派遣了我。
Yesu ya ce masu, “Inda Allah Ubanku ne, da kun kaunace ni, gama na zo daga wurin Allah kuma ga ni anan, gama ba domin kaina nazo ba, shine ya aiko ni.
43 為什麼你們不明白我的講論呢?無非是你們不肯聽我的話。
Meyasa baku gane magana ta ba? Ai saboda ba za ku iya jin maganata ba ne.
44 你們是出於你們的父親魔鬼並願意追隨你們父親的慾望。從起初,他就是殺人的兇手,不站在真理上,因為在他內沒有真理;他幾時撒謊,正出於他的本性,因為他是撒謊者,而且又是撒謊者的父親。
Ku na ubanku, shaidan ne, kuma kuna so ku yi nufe-nufe na ubanku. Shi mai kisan kai ne tun daga farko kuma ba ya tsayawa gaskiya saboda da babu gaskiya a cikin sa. Sa'anda yake fadin karya, yana maganar halinsa ne domin shi dama makaryaci ne da uban karya kuma.
Dayake ina fadin gaskiya baku bada gaskiya gare ni ba.
46 你們中誰能指證我有罪?若是我說真理,為什麼你們卻不信我呢?
Wanene a cikin ku ya kama ni da zunubi? Idan na fadi gaskiya don me ba ku gaskanta ni ba?
47 出於天主的,必聽天主的話;你們所以不聽,因為你們不是出於天主。」
Shi wanda yake na Allah ya kan ji maganar Allah, ku ba kwa jin maganar Allah da yake ku ba na Allah bane,”
48 猶太人遂向他說: 「我們說你是個撒瑪黎雅人,並附有魔鬼,豈不正對嗎?」
Yahudawa suka amsa suka ce masa, “Bamu fadi gaskiya ba da muka ce kai Basamariye ne kuma kana da aljan?”
49 耶穌答覆說: 「我沒有附魔,我只是尊敬我的父,你們卻侮辱我。
Yesu ya amsa, “Ni ba ni da aljan, ina girmama Ubana, ku kuma ba kwa girmama ni.”
50 然而,我不尋求我的光榮,有為我尋求而行判斷的一位。
Ba na neman daraja domin kaina, akwai wanda ke nema yana kuma hukuntawa.
51 我實實在在告訴你們: 「誰如果遵行我的話, 永遠見不到死亡。」 (aiōn )
Hakika, hakika, iIna ce maku, dukan wanda ya kiyaye maganata, ba za ya ga mutuwa ba.” (aiōn )
52 猶太向他說: 「現在我們知道: 你附有魔鬼;亞巴郎和先知都死了;你卻說: 誰如果遵行我的話,永遠嚐不到死味。 (aiōn )
Sai Yahudawa su ka ce masa, Yanzu mun sani kana da aljan. Ibrahim da annabawa sun mutu, amma kai ka ce, 'dukan wanda ya yi biyayya da maganata ba zai dandana mutuwa ba'. (aiōn )
53 難道你比我們的父親亞巴郎還大嗎?他死了,先知們也死了。你把你自己當作什麼人呢?」
Ai baka fi ubanmu Ibrahim girma ba wanda ya mutu, ko ka fi shi? Annabawa kuma sun mutu. Wa kake daukar kanka ne?”
54 耶穌答覆說: 「我如果光榮我自己,我的光榮算不了什麼;那光榮是我的,是我的父,就是你們所稱的「我們的天主」。
Yesu ya amsa, “Idan na daukaka kaina, daukaka ta banza ce, Ubana ne ya daukaka ni. Wanda kuka ce shi ne Allahnku.
55 你們不認識他,我卻認識他;我若說我不認識他,我便像你們一樣是個撒謊者;但是,我認識他,也遵守他的話。
Ku kuwa ba ku san shi ba, amma ni na san shi. Idan na ce ban san shi ba, na zama kamar ku kenan, makaryaci. Sai dai, Ni na san shi ina kiyaye maganarsa.
56 你們的父親亞巴郎曾歡欣喜樂地企望看到我的日子,他看見了極其高興。」
Ubanku Ibrahim ya yi farinciki da ganin rana ta; ya gan ta kuma ya yi murna.”
57 猶太就對他說: 「你還沒有五十歲,就見過亞巴郎嗎?」
Yahudawa su ka ce masa, “Baka kai shekara hamsin ba tukuna, ka taba ganin Ibrahim?”
58 耶穌回答說: 「我實實在在告訴你們: 在亞巴郎出現以前我就有。」
Yesu ya ce masu, “Hakika, hakika, ina ce maku, kafin a haifi Ibrahim, NI NE.”
59 他們就拿起石頭來要向他投去;耶穌卻隱沒了,從聖殿裏出去了。
Suka dauki duwatsu za su jefe shi, amma Yesu ya boye kansa, ya fita daga haikali.