< 約伯記 42 >

1 約伯回答上主說:
Sa’an nan Ayuba ya amsa wa Ubangiji,
2 我知道你事事都能,你所有的計劃,沒有不實現的。
“Na san cewa za ka iya yin dukan abubuwa; ba wanda zai iya ɓata shirinka.
3 是我以無智的話,使你的計劃模糊不明;是我說了無知的話,說了那些超越我智力的話。
Ka yi tambaya, ‘Wane ne wannan da ya ƙi karɓar shawarata shi marar ilimi?’ Ba shakka na yi magana game da abubuwan da ban gane ba, abubuwan ban al’ajabi da sun fi ƙarfin ganewata.
4 請你聽我發言;我求你指教我。
“Ka ce, ‘Saurara yanzu, zan kuma yi magana zan tambaye ka, kuma za ka amsa mini.’
5 以前我只聽見了有關你的事,現今我親眼見了你。
Kunnuwana sun ji game da kai amma yanzu na gan ka.
6 為此,我收回我所說過的話,坐在灰塵中懺悔。
Saboda haka na rena kaina na kuma tuba cikin ƙura da toka.”
7 上主對約伯說完這些話,就對特曼人厄里法次說:「我應向你和你的兩個友人發怒,因為你們講論我,不如我僕約伯講論的正確。
Bayan Ubangiji ya gaya wa Ayuba waɗannan abubuwa, ya ce wa Elifaz mutumin Teman, “Ina fushi da kai da abokanka guda biyu domin ba ku faɗi abin da yake daidai game da ni ba, kamar yadda bawana Ayuba ya yi.
8 現在你們要牽七頭公牛,和七隻公羊到我僕約伯那裏,叫他為你們奉獻全燔祭,也叫他為你們祈禱,因為我要看他的情面,不懲罰你們的糊塗,因為你們講論我,不如我僕約伯講的正確。」
Saboda haka yanzu sai ku ɗauki bijimai guda bakwai, da raguna bakwai, ku je wurin bawana Ayuba ku miƙa hadaya ta ƙonawa domin kanku. Bawana Ayuba zai yi muku addu’a zan kuwa karɓi addu’arsa in bi da ku nisa da wawancinku. Ba ku faɗi abin da yake daidai game da ni ba yadda bawana Ayuba ya yi ba.”
9 於是,特曼人厄里法次、叔亞人彼耳達得、納阿瑪人左法爾依照上主所吩咐的作了;上主就看了約伯的情面,饒恕了他們。
Saboda haka Elifaz mutumin Teman, Bildad mutumin Shuwa da Zofar mutumin Na’ama, suka yi abin da Ubangiji ya gaya masu; Ubangiji kuma ya karɓi addu’ar Ayuba.
10 約伯為他的朋友祈禱之後,上主就恢復了約伯原有的狀況,還照約伯以前所有的,加倍地賜給了他。
Bayan Ayuba ya yi wa abokansa addu’a, Ubangiji ya sa shi ya sāke zama mai arziki ya ninka abin da yake da shi a dā sau biyu.
11 約伯的兄弟和姊妹,並以前相識的人都來看望他,在他家中同他一起用飯;對於上主降於他的一切災禍,都向他表示同情,安慰他;每人還贈給他一枚金幣和一個金戒指。
Dukan’yan’uwansa maza da mata da duk waɗanda suka san shi a dā suka zo suka ci abinci tare da shi a cikin gidansa. Suka ta’azantar da shi suka ƙarfafa shi game da duk wahalar da Ubangiji ya auka masa, kowannensu kuma ya ba shi azurfa da zobe na zinariya.
12 上主賜給約伯以後的福分,遠勝過以前所有的;他擁有一萬四千隻羊,六千匹駱駝,一千對牛,一千頭母驢。
Ubangiji ya albarkaci ƙarshen Ayuba fiye da farkonsa. Yana da tumaki guda dubu goma sha huɗu, raƙuma guda dubu shida; shanun noma guda dubu da jakuna guda dubu.
13 他又生了七個兒子和三個女兒。
Ya kuma haifi’ya’ya maza bakwai, mata uku.
14 他給長女起名叫耶米瑪,次女叫刻漆雅,三女叫刻楞哈普客。
’Yar farko ya kira ta Yemima, ta biyun Keziya ta ukun Keren-Haffuk.
15 那地方的女子沒有比約伯的女兒更美麗的;她們的父親也使她們和兄弟們一樣承受家產。
Duk a cikin ƙasar ba a samu kyawawan mata kamar’ya’yan Ayuba ba, kuma babansu ya ba su gādo tare ta’yan’uwansu maza.
16 以後,約伯又活了一百四十歲,見了他的兒子、孫子,直到第四代。
Bayan wannan Ayuba ya rayu shekara ɗari da arba’in; ya ga’ya’yansa da’ya’yansu har tsara ta huɗu.
17 約伯壽高年老,已享天年,遂與世長辭。
Sa’an nan Ayuba ya rasu da kyakkyawan tsufa.

< 約伯記 42 >