< 約伯記 12 >
2 的確,只有你們是有知識的子民;那麼,你們一死,智慧也與你們一同喪亡!
“Ba shakka ku ne mutanen nan, hikima za tă mutu tare da ku!
3 其實,我和你們有同樣的心理,我並不亞於你們! 誰不知道這些事﹖
Amma ni ma ina da hankali kamar ku; ba ku fi ni ba. Wane ne bai san duk waɗannan abubuwan ba?
4 我這呼籲天主而蒙應允的人,卻被他的友人所嘲笑,無辜的義人卻成了笑柄。
“Na zama abin dariya ga abokaina, ko da yake na yi kira ga Allah ya kuwa amsa mini, duk da haka suka yi mini riya ko da yake ni mai adalci ne kuma marar laifi!
5 幸運的人心想:遭難的人應受蔑視,失足的人應再予以打擊。
Mutanen da ba su da damuwa suna jin daɗin ganin waɗanda suke dab da fāɗuwa.
6 但是,強盜的帳幕竟能安全,觸怒天主的人,以勢力為神的人卻享平安。
Amma wurin zaman’yan fashi yana nan ba mai damunsu, waɗanda kuma suke saɓa wa Allah suna zamansu lafiya, har ma da masu ɗaukar allahnsu a hannuwansu.
7 請你詢問走獸,牠們也會開導你;詢問天上的飛鳥,牠們也會告訴你;
“Amma ka tambayi dabbobi, za su kuma koya maka, ko kuma tsuntsayen sararin sama kuma za su gaya maka.
8 地上的爬蟲也會教訓你,海中的魚族也會給你說明。
Ko ka yi magana da duniya, za tă kuma koya maka, ko kuma ka bar kifin teku su sanar da kai.
Wane ne cikin waɗannan bai san cewa hannun Ubangiji ne ya yi wannan ba?
10 因為一切活物的生魂,一切血肉之人的靈魂,都握在他手中。
Ran kowace halitta yana a hannunsa, haka kuma numfashin dukan’yan adam.
Ko kunne ba ya gwada kalmomi kamar yadda harshe yake ɗanɗana abinci?
Ko ba a wurin tsofaffi ake samun hikima ba? Ba tsawon rai yana kawo ganewa ba?
13 但智慧和能力同在天主內,智慧與見識是天主所有。
“Allah ne mai iko da kuma hikima, shawara da ganewa nasa ne.
14 他若拆毀,人不能再建;他若拘禁,人不得開釋。
Abin da ya rushe ba a iya ginawa ba; in ya kulle mutum ba a iya buɗe shi a sake shi ba.
15 他若制水,水便乾涸;他若放水,水便沖毀大地。
Idan ya hana ruwan sama, za a yi fări; in kuma ya saki ruwa za a yi ambaliya.
16 力量與才能,為他所有;受騙者與騙人者,都屬於他。
Shi ne mai ƙarfi da kuma mai nasara; mai ruɗi da wanda aka ruɗa, duk nasa ne.
Yakan sa mashawarta su zama marasa hikima yă kuma sa wawaye su zama masu shari’a.
18 他解除君王所繫的玉帶,將繩索捆在他們的腰間;
Yana cire sarƙar da sarakuna suka ɗaura yă kuma ɗaura musu wata tsumma a kwankwaso.
Yakan ƙasƙantar da firistoci yă kuma tumɓuke masu ikon da aka kafa tun da daɗewa.
Yana sa amintattun mashawarta su yi shiru yakan kawar da hikimar dattawa.
Yakan sa masu iko su ji kunya yă kuma ƙwace ƙarfin masu ƙarfi.
Yana buɗe abubuwan da suke cikin duhu yă kuma kawo haske a wuraren da ba haske;
yana sa al’ummai su zama manya, sai kuma yă hallaka su; yana sa al’ummai su ƙasaita, yă kuma watsar da su.
Yana hana shugabannin duniya ganewa; Ya bar su su yi ta makuwa, su ruɗe, su ɓata.
Suna lallube cikin duhu ba haske; yă sa su yi ta tangaɗi kamar bugaggu.