< 耶利米書 28 >

1 同年,即猶大王漆德克雅即位之初第四年五月,基貝紅人阿組爾的兒子哈納尼雅先知,在上主殿裏當著司祭和全體人民對我說:「
A wata na biyar na wannan shekara, shekara ta huɗu, a farkon sarautar Zedekiya sarkin Yahuda, sai annabi Hananiya ɗan Azzur, wanda ya fito daga Gibeyon, ya zo wurina a gidan Ubangiji a gaban firistoci da kuma dukan mutane,
2 萬軍的上主,以色列的天主這樣說:我已折斷了巴比倫王的軛。
“Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila ya ce, ‘Zan karya karkiyar sarkin Babilon.
3 還有兩年,我就要取回巴比倫王拿步高,由這地取去,帶往巴比倫的一切上主殿的器皿,再放在這地方,
Cikin shekaru biyu zan komo da dukan kayayyakin gidan Ubangiji da Nebukadnezzar sarkin Babilon ya kwashe daga wannan wuri ya kai Babilon.
4 且領回猶大王約雅金的兒子耶苛尼雅及一切流徙至巴比倫的猶大俘虜,再來到這地方──上主的斷語──因為我要折斷巴比倫王的軛。」
Zan kuma komo da Yekoniya ɗan Yehohiyakim sarkin Yahuda da kuma dukan sauran masu zaman bauta daga Yahuda waɗanda suka tafi Babilon,’ in ji Ubangiji, ‘gama zan karya karkiyar sarkin Babilon.’”
5 耶肋米亞先知立當著站在上主殿裏的司祭和全體人民,答覆了先知哈納尼雅。
Sai annabi Irmiya ya amsa wa annabi Hananiya a gaban firistoci da kuma dukan mutane waɗanda suke tsaye a gidan Ubangiji.
6 耶肋米亞先知說:「盼望是這樣! 惟願上主這樣做! 惟願上主實踐你預言的話,使上主殿宇的器皿和一切俘虜,從巴比倫再回到這地方來!
Ya ce, “Amin! Ubangiji yă sa yă zama haka! Ubangiji yă cika maganar da ka yi annabci ta wurin komo da kayayyakin gidan Ubangiji da kuma dukan masu zaman bauta zuwa wannan wuri daga Babilon.
7 不過請聽我當面願對你和全體人民要說的這一句話:
Duk da haka, ka saurari abin da zan faɗa a kunnenka da kuma a kunnen duka mutane,
8 自古以來,在我和你以前的先知,對多少地區和強盛的王國,曾預言過戰爭,饑饉和瘟疫。
Daga farko fari annabawan da suka riga ka da ni sun yi annabcin yaƙi, masifa da annoba a kan ƙasashe masu yawa da kuma manyan mulkoki.
9 至於預言和平的先知,只在這先知的話實現以後,纔可認出這先知確是上主派遣的。
Amma annabin da ya yi annabcin salama shi za a ɗauka a matsayin wanda Ubangiji ya aika in har abin da ya furta ya zama gaskiya.”
10 哈納尼雅先知便從耶肋米亞先知頸上取下木軛,折斷了,
Sai annabi Hananiya ya cire karkiya daga wuyar annabi Irmiya ya karya ta,
11 然後對全體人民說:「上主這樣說:還有兩年,我要這樣從一切民族的頸上,折斷巴比倫王拿步高的軛。」於是耶肋米亞先知只得自行離去。
ya ce a gaban dukan mutane, “Ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘A haka zan karya karkiyar Nebukadnezzar sarkin Babilon daga wuyan dukan al’ummai a cikin shekaru biyu.’” Da wannan, annabi Irmiya ya yi tafiyarsa.
12 哈納尼雅先知從耶肋米亞先知頸上取下木軛折斷以後,即有上主的話傳給耶肋米亞說:「
Ba a daɗe ba bayan annabi Hananiya ya karya karkiya daga wuyan annabi Irmiya, sai maganar Ubangiji ta zo wa Irmiya cewa,
13 你去告訴哈納尼雅說:上主這樣說:;你折斷了木軛,但我必做鐵軛來代替。
“Je ka faɗa wa Hananiya cewa, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa, ka karya karkiyar katako, amma a wurinsa za ka sami karkiyar ƙarfe.
14 因為萬軍的上主,以色列的天主這樣說:我要將鐵軛放在這一切民族的頸上,使他們服事拿步高巴比倫王;他們該服事他,因為連田野的走獸我也交給了他。」
Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa zan sa karkiyar ƙarfe a wuyan dukan waɗannan al’ummai don in sa su bauta wa Nebukadnezzar sarkin Babilon, za su kuwa bauta masa. Zan ma sa shi ya mallaki namun jeji.’”
15 耶肋米亞先知於是對哈納尼雅先知說:「哈納尼雅! 請聽,上主並沒有派遣你,你竟使這人民相信謊言。
Sa’an nan annabi Irmiya ya ce wa annabi Hananiya, “Ka saurara, Hananiya! Ubangiji bai aike ka ba, duk da haka ka lallashe wannan al’umma su dogara ga ƙarya.
16 為此,上主這樣說:看,我要把你趕出地面;今年你必要死,因為你說了背叛上主的話。」
Saboda haka, ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘Ina shirin kawar da kai daga fuskar duniya. A wannan shekara za ka mutu, domin ka yi wa’azin tawaye a kan Ubangiji.’”
17 哈納尼雅先知就死在那年七月。
A wata na bakwai na wannan shekara, annabi Hananiya ya mutu.

< 耶利米書 28 >