< 耶利米書 15 >

1 上主對我說:「縱使梅瑟和撒慕爾立在我面前,我的的心仍不轉向這人民;你由我面前將他們驅逐,叫他們離去。
Sai Ubangiji ya ce mini, “Ko da Musa da Sama’ila za su tsaya a gabana, zuciyata ba za tă komo ga mutanen nan ba. Ka kore su daga gabana! Su tafi!
2 假如人對你說:我們往哪裏去﹖你就對他們說:上主這樣說:「該死的就死,該殺的就殺,該挨餓的就挨餓,該被擄去的,就被擄去。
In kuma suka tambaye ka, ‘Ina za mu tafi?’ Sai ka faɗa musu, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa, “‘Waɗanda aka ƙaddara ga mutuwa, ga mutuwa za su; waɗanda aka ƙaddara ga takobi, ga takobi za su; waɗanda aka ƙaddara ga yunwa, ga yunwa za su; waɗanda aka ƙaddara ga zaman bauta, ga zaman bauta za su.’
3 我必用四種型罰來懲罰他們──上主的斷語──用刀劍來殺,用野狗來拖,用天空的飛鳥和地上的野獸來吞食,來消滅。
“Zan aika musu da iri masu hallakarwa guda huɗu,” in ji Ubangiji, “takobi zai kashe, karnuka za su kwashe, tsuntsaye da namun jeji kuma su cinye su kuma hallaka.
4 我為了猶大王希則克雅的兒子默納舍在耶路撒冷所行的事,必使他們成為地上萬國所恐怖的對象。
Zan sa su zama abin ƙyama ga dukan mulkokin duniya saboda abin da Manasse ɗan Hezekiya sarkin Yahuda ya aikata a Urushalima.
5 耶路撒冷! 誰還憐恤你,誰還同情你,誰還轉身向你安﹖
“Wa zai ji tausayinki, ya Urushalima? Wa zai yi makoki dominki? Wa zai dakata ya tambayi lafiyarki?
6 你既離棄了我──上主的斷語──轉身背著我,我就只有對你伸出我的手,將你消滅;我對寬恕已感厭倦:
Kin ƙi ni,” in ji Ubangiji. “Ki ci gaba da ja da baya. Ta haka zan ɗibiya hannuwana a kanki in hallaka ki; ba zan ƙara nuna miki jinƙai ba.
7 我要在這地的城門口,用簸箕將他們簸散,使他們喪失子女;我要消滅我的人民,因為他們不離開自己的行徑。
Zan sheƙe ki da abin sheƙewa a ƙofofin birnin ƙasar. Zan kawo baƙin ciki da hallaka a kan mutanena, gama ba su canja hanyoyinsu ba.
8 他們的寡婦已多過海邊的沙粒;我要給他們招來午間的破壞者,襲擊英俊勇士的母親,使痛苦和恐怖突然降到她身上。
Zan ƙara yawan gwaurayensu su fi yashin teku yawa. Da tsakar rana zan kawo mai hallakarwa a kan iyaye mata na samarinsu; farat ɗaya zan kawo musu wahala da razana.
9 生過七個子女的母親,現已身衰氣絕,還是白天,她的太陽已經西落,她只有絕望惆悵;至於他們的遺民,我必使他們在敵人面前死於刀下──上主的斷語。
Mahaifiya’ya’ya bakwai za tă suma ta ja numfashinta na ƙarshe. Ranarta zai fāɗi tun lokacin bai yi ba; za tă sha kunya a kuma wulaƙanta ta. Zan sa a kashe raguwa da takobi a gaban abokan gābansu,” in ji Ubangiji.
10 我的母親! 我真不幸! 你竟生了我這與普世對抗相的人。我沒有向人借貸,人也沒有向我借貸,人卻都辱罵我。
Kaitona, mahaifiyata, da kika haife ni, mutumin da dukan ƙasa take faɗa take kuma gardama da shi! Ban ba da bashi ko in ci bashi ba, duk da haka kowa yana zagina.
11 實在,上主,我豈沒有盡力事奉你﹖我豈沒有在災難禍患時向你懇求﹖
Ubangiji ya ce, “Tabbatacce zan cece ka don alheri; tabbatacce zan sa abokan gābanka su yi roƙo gare ka a lokacin masifa da kuma lokacin wahala.
12 人豈能折斷北方的鐵和銅﹖
“Mutum zai iya karye ƙarfe ƙarfe daga arewa, ko tagulla?
13 [我必使你的財產和寶藏,任人搶奪,為補償你在你全境內犯的罪惡,
“Dukiyarku da arzikinku zan ba da su ganima, babu tara, saboda duka zunubanku ko’ina a ƙasar.
14 叫你在你不認識的地方,給你的仇敵為奴,因為我的怒火已燃起,必對你們發作] 。
Zan bautar da ku ga abokan gābanku a ƙasar da ba ku sani ba, gama fushina zai yi ƙuna kamar wuta da za tă yi ƙuna a kanku.”
15 上主,你都知道,求你回念我,眷顧我,為我報復迫害我的人,不要因你太忍耐,就讓我死去;你該知道:正是為了你,我才受人侮辱。
Ka gane, ya Ubangiji; ka tuna da ni ka kuma lura da ni. Ka yi mini ramuwa a kan masu tsananta mini. Cikin jimirinka, kada ka ɗauke ni; ka tuna yadda na sha zagi saboda kai.
16 你的話一來到,我就去吞下去;你的話成了我的喜悅,我心中的歡樂,上主,萬軍的天主! 因為我是歸於你名下的,
Sa’ad da maganganunka suka zo, na cinye su; suka zama abin farin ciki zuciyata kuma ta yi murna, gama ana kirana da sunanka, Ya Ubangiji Allah Maɗaukaki.
17 我從沒有坐在歡笑者的集會中一同取樂;我卻依你的指示獨自靜坐,因為你使我憤怒填胸。
Ban taɓa zauna a cikin’yan tawaye ba, ban taɓa yi murna da su ba; na zauna ni kaɗai domin hannunka yana a kaina ka kuma sa na cika da haushi.
18 為什麼我的痛苦如此久長,我的創傷不可醫治,痊愈無望﹖你於我好像是一條不常有水,而變化無常的溪流!
Me ya sa wahalata ba ta ƙarewa mikina kuma ba ya warkuwa? Za ka zama mini kamar rafi mai yaudara ne, kamar maɓulɓulan da ta kafe ne?
19 為此上主這樣說:「你若回來,我必讓你回來,使你能在立在我面前;若能發表高尚而非荒謬的思想,你就可作我的口舌,使他們轉向你,而不是你轉向他們。
Saboda haka ga abin da Ubangiji yana cewa, “In ka tuba, zan maido da kai don ka bauta mini; in ka ambaci maganganu masu kyau, ba marasa kyau ba, za ka zama kakakina. Bari wannan mutane su juyo gare ka, amma kada ka juye gare su.
20 這樣,我必使你這人民成為一設防的銅牆,他們能攻打擊你,卻不能制勝你,因為有我與你同在,援助你,解救你──上主的斷語──
Zan mai da kai katanga ga wannan mutane, katanga mai ƙarfi na tagulla; za su yi yaƙi da kai amma ba za su yi nasara a kanka ba, gama ina tare da kai don in kuɓutar in kuma cece ka,” in ji Ubangiji.
21 我必解救你脫離惡人的手,由強暴人的掌握中將你贖回」。
“Zan cece ka daga hannuwan mugaye in ɓamɓare ka daga hannun marasa tausayi.”

< 耶利米書 15 >