< 以賽亞書 63 >

1 「那由厄東而來,身穿染紅了的衣服,那由波責辣而來,衣著華麗,力量強大,闊步前進的是誰啊﹖」「是宣佈正義,具有拯救大能的我。」「
Wane ne wannan mai zuwa daga Edom, daga Bozra, saye da jajjayen rigunarsa? Wane ne wannan, sanye cikin daraja, tafe cikin girmar ƙarfinsa? “Ni ne, mai magana cikin adalci, mai ikon ceto.”
2 你的服裝怎麼成了紅色,你的衣服好似一個踏酒醡的呢﹖」「
Me ya sa rigunanka suka yi ja, sai ka ce na wanda yake tattaka’ya’yan inabi?
3 因為唯獨我一人踐踏了酒醡,我的人民中沒有一個與我在一起。我在怒氣中踐踏了他們,我在怒火中蹂躪了他們,因此他們的血液濺到我的衣服上,我的服裝就完全染污了。
“Na tattake’ya’yan inabi ni kaɗai; cikin al’ummai kuma babu wani tare da ni. Na tattake su cikin fushina Na matse su cikin hasalata; jininsu ya fantsamar wa rigunana, na kuma ɓata dukan tufafina.
4 因為復仇的日子已在我心中,我施救的歲月已經來到。
Gama ranar ɗaukan fansa tana a cikin zuciyata, kuma shekarar fansata ta zo.
5 我四下觀看,但沒有人輔助;我驚愕四顧,但沒有人支持;因此惟有用我的手臂自行拯救,以我的怒氣來支持自己。
Na duba, amma babu wanda zai taimaka, na yi mamaki cewa ba wanda ya goyi baya; saboda haka hannuna ya yi mini ceto, fushina kuma ya rayar da ni.
6 我在怒氣中踐踏了民眾,我在怒火中粉碎了他們,使他們的鮮血流倒地下。」
Na tattake al’ummai cikin fushina; cikin hasalata kuma na sa sun bugu na kuma zub da jininsu a ƙasa.”
7 我要依照上主以他的大慈大悲賜與我們的一切,和對以色列家所賜的宏福,稱頌上主的慈惠和上主可讚頌的作為。
Zan ba da labarin alherin Ubangiji, ayyukan da suka sa a yabe shi, bisa ga dukan abubuwan da Ubangiji ya yi mana, I, ayyuka masu kyan da ya yi domin gidan Isra’ila, bisa ga jinƙansa da yawan alheransa.
8 他曾說過:「他們的確是我的百姓,不行虛偽的子民;」因此他成了他們一切困難中的拯救者。
Ya ce, “Babu shakka su mutanena ne,’ya’ya maza waɗanda ba za su ruɗe ni ba”; ta haka ya zama Mai Cetonsu.
9 並不是使者,也不是天使拯救他們,而是他自己。他以自己的愛情和憐憫贖回了他們;在往日,他時常扶持他們,懷抱他們。
Cikin dukan damuwarsu shi ma ya damu, mala’ikan da yake gabansa ya cece su. Cikin ƙauna da jinƙai ya fanshe su; ya kuma ɗaga su ya riƙe su dukan kwanakin dā
10 但是他們成了叛徒,刺傷了他的聖神;因此他變成了他們的敵人,親自攻擊他們。
Duk da haka suka yi tawaye suka ɓata wa Ruhu Mai Tsarki rai. Saboda haka ya juya ya kuma zama abokin gābansu shi kansa kuma ya yaƙe su.
11 那時,他們想起古來的日子,想起他的僕人梅瑟。那引領羊群的牧者出離海洋的在那裏呢﹖那曾在他心中賦與自己聖神的在那裏呢﹖
Sa’an nan mutanensa suka tuna kwanakin dā, kwanakin Musa da mutanensa, ina yake shi wanda ya fitar da su ta teku, da makiyayan garkensa? Ina shi yake wanda ya sa Ruhunsa Mai Tsarki a cikinsu,
12 那在梅瑟右邊以其榮耀的手臂,在百姓前分開海水,使自己獲得永遠聲譽的在那裏呢﹖
wanda ya aika hannu ɗaukakarsa mai iko ya kasance a hannun dama na Musa, wanda ya raba ruwaye a gabansu, don yă sami wa kansa madawwamin suna,
13 那領導他們走過深淵,有如馬行於曠野而不顛躓的在那裏呢﹖
wanda ya bishe su cikin zurfafa? Kamar doki a fili, ba su yi tuntuɓe ba;
14 上主的神怎樣領導走獸下到山谷,你也怎樣領導了你的百姓,好使你獲得一個光榮的名號。
kamar shanun da suke gangarawa zuwa kwari, haka Ruhun Ubangiji ya ba su hutu. Ga yadda ka bishe mutanenka don ka ba wa kanka suna mai ɗaukaka.
15 如今求你從天垂顧,從你光榮的聖所俯視!你的熱愛,你的大能和你的同情心在那裏呢﹖求你不要停止你的慈悲,
Ka duba daga sama ka gani daga kursiyinka da yake bisa, mai tsarki da kuma mai ɗaukaka. Ina kishinka da kuma ikonka? Ka janye juyayi da kuma tausayin da kake yi mana daga gare mu.
16 因為你是我們的父親;亞巴郎雖不認識我們,以色列雖不記得我們,你上主卻是我們的父親,「我們自古以來的救主」就是你的名。
Amma kai Ubanmu ne, ko Ibrahim bai san mu ba Isra’ila kuma bai yarda da mu ba; kai, ya Ubangiji, kai ne Ubanmu, Mai Fansarmu tun fil azal ne sunanka.
17 上主! 你為什麼讓我們離開你的道路﹖使我們的心變硬而不敬畏你﹖求你為了你的僕人,為了你產業的各支派,回心轉意罷!
Don me, ya Ubangiji, ka sa muna barin hanyoyinka muka kuma taurare zukatanmu don kada mu girmama ka? Ka komo domin darajar bayinka, kabilan da suke abin gādonka.
18 你為什麼讓惡人踐踏你的聖殿﹖為什麼讓我們的敵人蹂躪你的聖所﹖
Gama a ɗan lokaci mutanenka suka mallaki wurinka mai tsarki, amma yanzu abokan gābanmu sun tattake wurinka mai tsarki.
19 我們儼然成了一個從未受你治理,從未屬你名下的民族。啊!
Mu naka tun fil azal; ba ka taɓa yin mulki a kansu ba, ba a taɓa kira su da sunanka ba.

< 以賽亞書 63 >