< 以賽亞書 23 >
1 有關提洛的神諭:你們哀號罷!塔爾史士的船隻!因為你們的保壘已遭破壞。由基廷地歸來的,他們得到了這消息。
Abin da Allah ya faɗa game da Taya. Ku yi kuka mai zafi, ya jiragen ruwan Tarshish! Gama an hallaka Taya aka kuma bar su babu gida ko tasha. Daga ƙasar Saifurus magana ta zo musu.
Ku yi shiru, ku mutanen tsibiri da ku’yan kasuwan Sidon waɗanda masu ciniki a teku suka azurta.
3 在大水之上運來的,是史曷爾的穀物;尼羅河的收穫,是她的財富;她成了萬民的商場。
A manyan ruwaye hatsin Shihor suka iso; girbin Nilu ne kuɗin shiga na Taya ta kuma zama kasuwar al’ummai.
4 漆冬!羞慚罷!因為海說過:【即海中的保壘說過:】「我沒有分娩過,也沒有生產過;沒有撫養過青年,也沒有養育過處女。」
Ki ji kunya, ya ke Sidon, da ke kuma, kagarar teku, gama teku ya yi magana ya ce, “Ban taɓa naƙuda ba balle in haifi’ya’ya; ban taɓa goyon’ya’ya maza ba balle in reno’ya’ya mata.”
5 這風聲一傳到了埃及,大家都為了提洛的消息而戰慄。
Sa’ad da magana ta kai Masar, za su razana da jin labari daga Taya.
6 你門過海到塔爾史士去罷!海濱的居民你們哀號罷!
Ku haye zuwa Tarshish; ku yi kuka mai zafi, ku mutanen tsibiri.
7 這就是你們所誇耀的城嗎﹖她本起源於上古,她的雙腳曾將她帶至遠方寄居。
Wannan ce birnin murnanku, birnin nan na tun dā wadda ƙafafunta suka kai ta zama a ƙasashe masu nesa?
8 是誰策劃了這事,來反對加過冕的提洛﹖她得商賈本來都是王侯,商販本來都是地上的顯要。
Wane ne ya ƙulla wannan a kan Taya ita da take ba da rawanin sarauta, wadda’yan kasuwanta sarakuna ne, wadda masu cinikinta sanannu ne a duniya?
9 是萬軍的上主策劃了這事,為打擊她一切自矜的狂傲,侮辱地上所有的顯要。
Ubangiji Maɗaukaki ya ƙulla shi, don yă kawo ƙarshen girman kan dukan darajarta ya kuma ƙasƙantar da dukan waɗanda suke sanannu a duniya.
Ki nome ƙasarki har zuwa wajen Nilu, Ya Diyar Tarshish, gama ba ki da tashan jirgin ruwa kuma.
11 上主的手已伸在海上,使萬國戰慄震驚;上主對客納罕已決定,要摧毀她的要塞。
Ubangiji ya miƙa hannunsa a bisa teku ya kuma sa mulkokinsa suka yi rawar jiki. Ya ba da umarni game da Funisiya cewa a hallaka kagararta.
12 他說過:「漆冬女兒!遭虐待的處女,你不要再歡樂!起來,往基廷去!在那裏你也得不到安寧!」
Ya ce, “Ba za ki ƙara yin murna ba, Ya ke Budurwa Diyar Sidon, yanzu da kike ragargajiya! “Tashi, ki ƙetare zuwa Saifurus; a can ɗin ma ba za ki huta ba.”
13 看基廷的地域!【她已不成為民族,亞述已將她委棄予野獸;】人設立了高塔,毀壞了她的宮殿,使她成了一片廢 墟。
Dubi ƙasar Babiloniyawa, wannan mutanen da yanzu ba su da wani amfani! Assuriyawa sun mai da ita wurin zaman halittun hamada; sun gina hasumiyoyin kwanto, suka ragargaza kagararta ƙaf suka mai da ita kango.
14 塔爾史士的船隻! 你們哀號罷! 因為你們的保壘已遭破壞!
Ku yi kuka mai zafi, ku jiragen ruwan Tarshish; an rurrushe kagararku!
15 到那天,提洛將被遺忘七十年之久,有如一位君王的歲月。過了七十年,提洛要像妓女歌曲中所唱的:「
A wannan lokaci za a manta da Taya har shekaru saba’in, tsawon rayuwar sarki. Amma a ƙarshen waɗannan shekaru saba’in, zai zama wa Taya kamar yadda yake a waƙar karuwa cewa,
16 被遺忘的妓女!拿琴遊城罷﹖巧彈多唱罷!好使人再記起你來!」
“Ɗauki garaya, ki ratsa birni, Ya ke karuwar da aka manta da ita; kaɗa garaya da kyau, ki rera waƙoƙi masu yawa, saboda a tuna da ke.”
17 過了七十年,上主要眷顧提洛,她要再接受纏頭,與地面世上各國交易。
A ƙarshen shekaru saba’in, Ubangiji zai magance Taya. Za tă koma ga aikinta na karuwanci za tă kuma yi kasuwancinta da dukan mulkokin duniya.
18 她的贏利和她的進項將祝聖與上主,必不再貯藏積蓄起來,因為她的贏利將歸於那些在上主面前度日的人,使他們吃得飽,穿得體面。
Duk da haka za a keɓe ribarta da kuɗin shigarta wa Ubangiji; ba za a yi ajiyarsu ko a ɓoye su. Ribarta za tă tafi ga waɗanda suke yi wa Ubangiji sujada, don su sami yalwataccen abinci da tufafi masu kyau.