< 以賽亞書 1 >

1 在烏齊雅、約堂、阿哈次和希則克雅為猶大王時,阿摩茲的兒子依撒意亞,關於猶大和耶路撒冷所見的異象如下:
Wahayi game da Yahuda da Urushalima wanda Ishaya ɗan Amoz ya gani a zamanin da Uzziya, Yotam, Ahaz da Hezekiya, suka yi mulkin Yahuda.
2 諸天,請諦聽!大地,請側耳! 因為上主有話說:「我把孩子撫養長大,他們竟背叛了我 !
Ku kasa kunne, ya sammai! Ki saurara, ya duniya! Gama Ubangiji ya yi magana, “Na yi renon’ya’ya, na kuma raya su, amma sun tayar mini.
3 牛認識自己的主人,驢也認識自己主人的槽,以色列卻毫不知情,我的百姓卻一點不懂。」
Saniya ta san maigidanta, jaki ya san wurin sa wa dabbobi abinci maigidansa, amma Isra’ila ba su sani, mutanena ba su gane ba.”
4 禍哉,犯罪的民族,惡貫滿盈的百姓,作惡的後裔,敗壞的子孫!他們離棄了上主,蔑視了以色列的聖者,轉身背棄了他。
Kash, ya ke al’umma mai zunubi, mutane cike da laifi, tarin masu aikata mugunta,’ya’yan da aka miƙa wa lalaci! Sun yashe Ubangiji; sun rena Mai Tsarkin nan na Isra’ila suka juya masa baya.
5 你們為什麼還繼續叛逆,再遭受打擊呢﹖整個頭已患了病,整個心已經焦悴;
Me ya sa za a ƙara yin muku dūka? Me ya sa kuka nace ga yin tayarwa? An yi wa dukan kanku rauni, zuciyarku duk tana ciwo.
6 從腳掌直到頭頂已體無完膚,盡是創痍、傷痕和新的傷口;沒有擠淨,沒有包紮,也沒有軟膏滋潤。
Daga tafin ƙafarku zuwa saman kanku ba lafiya, sai miyaku da ƙujewa da manyan gyambuna, ba a tsabtacce su ba ko a daure ko shafa musu magani.
7 你們的地區變成荒蕪,你們的城市被火燒盡,你們面前的莊田被異民吞併,變成一片荒涼,宛如索多瑪的廢墟;
Ƙasarku ta zama kufai, an ƙone biranenku da wuta; baƙi suna ƙwace gonakinku a idanunku, ta zama kango kamar sa’ad da baƙi suka rushe ta.
8 僅存的熙雍女兒,有如葡萄園裏的茅舍,胡瓜園中的草廬,被圍困著的城市。
An bar diyar Sihiyona kamar rumfar mai ƙumu a gonar inabi, kamar bukka a gonar kabewa, kamar birnin da aka kewaye da yaƙi.
9 若非萬軍的上主給我們留下些許殘餘,我們早已如同索多瑪,相似哈摩辣了。
Da ba a ce Ubangiji Maɗaukaki ya bar mana raguwar masu rai ba, da mun zama kamar Sodom, da mun zama kamar Gomorra.
10 索多瑪的統治者,請聽上主的話!哈摩辣的百姓,請聽天主的訓示:「
Ku saurari maganar Ubangiji, ku masu mulkin Sodom; ku kasa kunne ga dokar Allahnmu, ku mutanen Gomorra!
11 你們為什麼向我奉獻那麼多的犧牲﹖--上主說:我已飽饜了公羊的燔祭和肥犢的脂膏;牛犢、羔羊和山羊的血我已不喜歡;
Ubangiji ya ce, “Yawan hadayunku, mene ne suke a gare ni?” Ina da isashen hadayun ƙonawa, na raguna da na kitsen dabbobi masu ƙiba; ba na jin daɗin jinin bijimai da na tumaki da kuma na awaki.
12 你們來見我的面時,誰向你們要求了這些東西﹖這簡直是蹂躪我的殿院。
Sa’ad da kuka zo don ku bayyana a gabana, wa ya nemi wannan daga gare ku, da kuke kai da kawowa a filayen gidana?
13 不要再奉獻無謂的祭品!馨香已為我所憎惡,月朔、安息日、集會、齋戒和盛大的宴會,我已都不能容受。
Ku daina kawo hadayu marasa amfani! Turarenku abin ƙyama ne gare ni. Ina ƙin bukukkuwanku na Sabon Wata, da na ranakun Asabbaci, da taronku na addini, ba zan iya jure wa mugun taronku ba.
14 我的心痛恨你們的月朔和你們的慶節,它們為我是種累贅,使我忍無可忍。
Bukukkuwanku na Sabon Wata da na tsarkakan ranaku na ƙi su. Sun zama mini kaya; na gaji da ɗaukansu.
15 你們伸出手時,我必掩目不看;你們行大祈禱時,我決不俯聽,因為你們的手染滿了血!
Sa’ad da kuka ɗaga hannuwanku wajen yin addu’a, zan ɓoye fuskata daga gare ku; ko da kun miƙa addu’o’i masu yawa, ba zan kasa kunne ba. Hannuwanku sun cika da jini!
16 你們應該洗滌,應該自潔,從我眼前革除你們的惡行,停止作孽,
Ku yi wanka ku kuma tsabtacce kanku. Ku kawar da mugayen ayyukanku daga gabana; Ku daina aikata mugunta.
17 學習行善,尋求正義,責斥壓迫人的人,為孤兒伸冤,為寡婦辯護。
Ku koyi yin nagarta; ku nemi adalci. Ku ƙarfafa waɗanda aka zalunta. Ku ba wa marayu hakkinsu, ku taimaki gwauruwa.
18 現在你們來,讓我們互相辯論--上主說:你們的罪雖似朱紅,將變成雪一樣的潔白;雖紅得發紫,仍能變成羊毛一樣的皎潔。
Ubangiji ya ce, “Yanzu fa ku zo, bari mu dubi batun nan tare, Ko da zunubanku sun yi ja kamar garura, za su zama fari kamar ƙanƙara; ko da sun yi ja kamar mulufi, za su zama kamar ulu.
19 假使你們樂意服從,你們將享用地上的美物;
In kuna da niyya kuna kuma yi mini biyayya, za ku ci abubuwa masu kyau daga ƙasar;
20 假使你們拒絕反抗,你們將為刀劍所吞滅。」這是上主親口說的。
amma in kuka yi tsayayya kuka kuma yi tayarwa, za a kashe ku da takobi.” Ni Ubangiji na faɗa.
21 忠貞的城邑,怎麼變成了蕩婦! 昔日充滿著正義,寄居著公平的,現今卻住滿了謀殺的兇手!
Dubi yadda amintacciyar birni ta zama karuwa! Dā ta cika da yin gaskiya; dā masu adalci a can suke zama, amma yanzu sai masu kisankai kaɗai!
22 你的銀子變成了渣滓,你的美酒攙和了水份;
Azurfarki ta zama jebu, an gauraye ruwan inabinki mafi kyau da ruwa.
23 你的首領謀反作亂,成了盜賊的幫兇;他們都愛好賄賂,索取報酬,不為孤兒伸冤,不受理寡婦的訴訟。
Masu mulkinki’yan tawaye ne, abokan ɓarayi; dukansu suna ƙaunar cin hanci suna bin kyautai. Ba sa taɓa tsare marayu a ɗakin shari’a; ba sa taimakon gwauruwa.
24 因此吾主,萬軍的上主,以色列的大能者說:「哎!我必向我的敵人雪恨,我必向我的仇人復仇。
Saboda haka Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki, Mai Iko nan na Isra’ila, ya furta, “Kai, zan sami hutu daga maƙiyana in kuma yi ramuwa a kan abokan gābana.
25 我必向你伸出我的手,用爐火煉盡你的渣滓,除去你所有的鉛錫。
Zan juye hannuna a kanki; zan wanke ke sarai in fitar da dukan ƙazantarki.
26 我要使你的民長復興如初;使你的參謀恢復如初;以後你將被稱為正義的城市,忠貞的城邑。」
Zan maido da alƙalanki kamar yadda suke a dā can, mashawartanki kamar yadda suke da fari. Bayan haka za a ce da ke Birnin Masu Adalci, Amintacciyar Birni.”
27 熙雍將因正直獲得救贖,她的居民將因正義蒙受救恩;
Za a fanshi Sihiyona da adalci, masu tubanta kuma da aikin gaskiya.
28 然而惡人和罪人必將一同滅亡,背棄上主的人必要滅絕。
Amma za a karye’yan tawaye da masu zunubi, waɗanda suka rabu da Ubangiji kuma za su hallaka.
29 你們必因你們所喜愛的橡樹而蒙羞,必因你們所選擇的花園而慚愧;
“Za ku ji kunya saboda masujadan ƙarƙashin itatuwan oak da kuka yi farin ciki; za a kunyata ku saboda lambun da kuka zaɓa.
30 你們將變成一棵落葉的橡樹,一座無水的花園。
Za ku zama kamar itacen oak mai busasshen ganyaye, kamar lambu marar ruwa.
31 強者將似麻絮,他的工作猶如火花:二者必要同時焚燒,無人予以熄滅。
Mutum mai ƙarfi zai zama kamar rama, aikinsa kuma kamar tartsatsin wuta; duka za su ƙone tare, ba kuwa wanda zai kashe wutar.”

< 以賽亞書 1 >