< 何西阿書 6 >
1 「來,我們回到上主那裏去,因為衪撕碎了我們,也必要治愈;衪打傷了我們,也必要包紮。
“Ku zo, mu koma ga Ubangiji. Ya yayyage mu kucu-kucu amma zai warkar da mu; ya ji mana ciwo amma zai daure mana miyakunmu.
2 兩天後衪必使田復生,第三天衪必使我們興起,生活在衪的慈顏下。
Bayan kwana biyu zai rayar da mu, a rana ta uku zai tashe mu, don mu rayu a gabansa.
3 讓我們認識上主,讓我們努力認識上主! 衪定要像曙光一樣出現,衪要來到我們中間,有如秋雨,有如滋潤田地的春雨。」
Bari mu yarda da Ubangiji; bari mu nace gaba don mu yarda da shi. Muddin rana tana fitowa, zai bayyana; zai zo mana kamar ruwan bazara, kamar ruwan saman farko da yake jiƙe ƙasa.”
4 厄弗辣因,我可對你們作什麼﹖因為你們的仁愛有如旱晨的浮雲,有如易於消散的朝露。
“Me zan yi da kai Efraim? Me zan yi da kai Yahuda? Ƙaunarku tana kamar hazon safiya, kamar raɓar safiya da takan ɓace.
5 因此,我藉先知們砍伐了他們,以我口中的言語殺死戳了他們;我的的裁判出現有如光明:
Saboda haka na yayyaga ku kucu-kucu tare da annabawana, na kashe ku da kalmomin bakina; hukuntaina sun haskaka kamar walƙiya a kanku.
6 因為我喜歡仁慈勝過祭獻,喜歡人認識天主勝過全燔祭。
Gama jinƙai nake bukata, ba hadaya ba, ku kuma san Allah a maimakon hadayun ƙonawa.
Kamar Adamu, sun tā da alkawari, sun yi mini rashin aminci a can.
Gileyad birni ce ta mugayen mutane, da tabon alamun jini.
9 一隊司祭就如埋伏的強盜,在往舍根的路上行兇;的確,他們行了可恥的事
Kamar yadda mafasa sukan yi fakon mutum, haka ƙungiyoyin firistoci suke; suna kisa a hanya zuwa Shekem, suna aikata laifofi bankunya.
10 在貝特耳我見了可惡的事:在那裏厄弗辣因行了淫,以色列玷污了自己
Na ga wani abu mai bantsoro a gidan Isra’ila. A can Efraim ya miƙa wuya ga karuwanci Isra’ila kuma ta ƙazantu.
11 當我轉變我百姓的命運時,猶大啊! 為你也注定了一個收割期。
“Ku kuma, ya mutanen Yahuda, na shirya muku ranar girbi. “A duk sa’ad da zan mayar da dukiya wa mutanena,