< 哈巴谷書 3 >
Addu’ar annabi Habakkuk. A kan shigiyont.
2 上主,我聽到了你的報道;上主,我見到你的作為;求你在歲月的過程中,彰顯你的作為,求你在歲月的過程中,宣佈出來! 但願你發怒時,也懷念仁慈。
Ya Ubangiji, na ji irin shaharar da ka yi; na yi al’ajabi game da ayyukanka, ya Ubangiji. Ka maimaita su a kwanakinmu, ka sanar da su a lokacinmu; ka yi jinƙai ko a lokacin da kake fushi.
3 天主自特曼而來,聖者由帕蘭山而至(休止);衪的威嚴遮蓋諸天,衪的榮耀充滿地。
Allah ya zo daga Teman, Mai Tsarkin nan daga Dutsen Faran. (Sela) Ɗaukakarsa ta rufe sammai yabonsa kuma ya cika duniya.
4 衪的光輝明輝如日;衪手中射出的光芒,蘊藏著衪的威能。
Darajarsa ta yi kamar fitowar rana; ƙyalƙyali ya wulga daga hannunsa, inda ikonsa yake a ɓoye.
Annoba ta sha gabansa; cuta kuma tana bin bayansa.
6 衪一停立,大地就動搖;衪一注視,萬民就戰慄;太古的山嶽崩裂,久遠的丘陵沉沒;衪自永遠即在其上行走。
Ya tsaya, ya kuwa girgiza duniya; ya duba, sai ya sa al’ummai suka yi rawan jiki. Tsofaffin duwatsu sun wargaje daɗaɗɗun tuddai kuma suka rurrushe. Hanyoyinsa dawwammamu ne.
Na ga tentin Kushan cikin azaba; wuraren zaman Midiyan cikin damuwa.
8 上主! 當你騎著馬,乘著凱旋車時,是否是向河流發怒﹖或是向海洋洩憤﹖
Ka ji haushin koguna ne, ya Ubangiji? Ko kuwa ka hasala da rafuffuka ne? Ko ka yi fushi da teku ne sa’ad da ka hau dawakanka da kuma kekunan yaƙinka masu nasara?
9 你抽出了你的弓弩,囊中裝滿了箭羽(休止);你劈地成河,
Ka ja bakanka, ka nemi a ba ka kibiyoyi masu yawa. (Sela) Ka raba duniya da koguna;
10 叢山見你而戰慄;驟雨由雲中降下,深潚發出巨響,太陽齔了昇起,
duwatsu sun gan ka sai suka ƙame. Ruwaye masu hauka sun yi ta fantsamawa; zurfafa suka yi ruri suka tā da raƙuman ruwansu sama.
11 月亮停於居所:這是因了你放射箭羽的光芒,你槍矛閃爍的光亮。
Rana da wata suka tsaya cik a sammai da ganin kibiyoyinka masu wucewa fyu, da ganin hasken māshinka mai walƙiya.
Cikin hasala ka ratsa duniya cikin fushi kuma ka tattake ƙasashe.
13 你出征是為了你的百姓,是為了你的受傅者;你折毀了惡人的屋頂,使屋基露出,直到磐石(休止)
Ka fito don ka fanshi mutanenka, don ceci shafaffenka. Ka ragargaza shugaban ƙasar mugaye, ka tuɓe shi daga kai har ƙafa. (Sela)
14 你用箭他戰士的頭,因為他們衝來要驅散我們,且高興的有如在暗中吞食貧民的人。
Da māshinsa ka soki kansa sa’ad da jarumawansa suka fito don su tarwatse mu, suna farin ciki sai ka ce masu shirin cinye matalautan da suke a ɓoye.
Ka tattake teku da dawakanka, kana kaɗa manyan ruwaye.
16 我一聽見,我的我的臟腑發抖;對此消息,我的口脣打顫;痲痺侵入 下骨骸,我的步伐在我下面已零亂。我在靜待那因難的日子,因為那日子必要臨於進攻我們的民族身上。
Na ji sai zuciyata ta buga, leɓunana sun yi rawa da jin murya; ƙasusuwana suka ruɓe, ƙafafuna kuma sun yi rawa. Duk da haka zan jira da haƙuri ga ranar bala’i ta zo a kan al’umman nan mai kawo mana hari.
17 縱然無花果樹不發芽,葡萄樹不結實,橄欖樹一無所產,麥田不出產食糧,羊棧內沒有羊,牛欄中沒有牛,
Ko da yake itace ɓaure bai tohu ba, ba kuma’ya’ya a kuringar inabi, ko da yake zaitun bai ba da amfani ba, gonaki kuma ba su ba da abinci ba, ko da yake babu tumaki a garke, ba kuma shanu a turaku,
duk da haka zan yi farin ciki da Ubangiji, zan yi murna da Allah Mai Cetona.
19 我主上主是我的力量,衪使我的腳有如鹿腳,引我在高處步行。──交於樂官,和以絃樂。
Ubangiji Mai Iko Duka shi ne ƙarfina; yakan mai da ƙafafuna kamar na barewa, yakan sa in yi tafiya a wurare masu tsayi. Domin mai bi da kaɗe-kaɗe. A kan kayan kiɗi masu tsirkiyata.