< 創世記 6 >

1 當人在地上開始繁殖,生養女兒時,
Sa’ad da mutane suka fara ƙaruwa a duniya, aka kuma hahhaifi musu’ya’ya mata,
2 天主的兒子見人的女兒美麗,就隨意選取,作為妻子。
sai’ya’yan Allah maza suka ga cewa’ya’yan mutane mata suna da bansha’awa, sai suka zaɓi waɗanda suke so, suka aura.
3 上主於是說:「因為人既屬於血肉,我的神不能常在他內;他的壽數只可到一百二十歲。」
Sa’an nan Ubangiji ya ce, “Ruhuna ba zai zauna a cikin mutum har abada ba, saboda shi mai mutuwa ne, kwanakinsa za su zama shekaru ɗari da arba’in ne.”
4 當天主的兒子與人的兒女結合生子時,在地上已有一些巨人,(以後也有,)他們就是古代的英雄,著名的人物。
Nefilimawa suna nan a duniya a waɗancan kwanaki, da kuma kwanakin da suka bi baya, a sa’ad da’ya’yan Allah suka kwana da’ya’yan mutane mata, suka kuma hahhaifi musu’ya’ya. Ai, su ne jarumawan dā, mutanen da suka shahara.
5 上主見人在地上的罪惡重大,人心天天所思念的無非是邪惡;
Ubangiji kuwa ya lura cewa muguntar mutum ta yi yawa a duniya, kuma kowane abin da yake tunani a zuciyarsa mugu ne kawai a kowanne lokaci.
6 上主遂後悔在地上造了人,心中很是悲痛。
Ubangiji ya damu da ya yi mutum a duniya, abin ya zafe shi ƙwarai.
7 上主於是說:「我要將我所造的人,連人帶野獸、爬蟲和天空的飛鳥,都由地面上消滅,因為我後悔造了他們。」
Saboda haka Ubangiji ya ce, “Zan kawar da mutum, da dabbobi, da halittu masu rarrafe a ƙasa da kuma tsuntsayen sama waɗanda na halitta, daga doron ƙasa, saboda na damu da na yi su.”
8 惟有諾厄在上主眼中蒙受恩愛。
Amma Nuhu ya sami tagomashi a gaban Ubangiji.
9 以下是諾厄的小史:諾厄是他同時代惟一正義齊全的人,常同天主往來。
Ga tarihin Nuhu. Nuhu mutum ne mai adalci, marar abin zargi a cikin mutanen zamaninsa, ya kuma yi tafiya tare da Allah.
10 他生了三個兒子:就是閃、含、和耶斐特。
Nuhu yana da’ya’ya maza uku, Shem, Ham da Yafet.
11 大地已在天主面前敗壞,到處充滿了強暴。
Duniya dai ta lalace sosai a gaban Allah, ta kuma cika da tashin hankali.
12 天主見大地已敗壞,因為凡有血肉的人,品行在地上全敗壞了,
Allah ya ga yadda duniya ta lalace, gama dukan mutane a duniya sun lalatar da rayuwarsu.
13 天主遂對諾厄說:「我已決定要結果一切有血肉的人,因為他們使大地充滿了強暴,我要將他們由大地上消滅。
Saboda haka, Allah ya ce wa Nuhu, “Zan kawo ƙarshen dukan mutane, gama saboda su duniya ta cika da tashin hankali. Lalle zan hallaka su da kuma duniya.
14 你要用柏木造一隻方舟,舟內建造一些艙房,內外都塗上瀝青。
Saboda haka ka yi wa kanka jirgi da katakon Saifires, ka yi ɗakuna a cikinsa, ka shafe shi da ƙaro ciki da waje.
15 你要這樣建造:方舟要有三百肘長,五十肘寬,三十肘高。
Ga yadda za ka gina shi; jirgin zai kasance mai tsawon ƙafa 45, fāɗinsa ƙafa 75, tsayinsa kuma ƙafa 45.
16 方舟上層四面做上窗戶,高一肘,門要安在側面;方舟要分為上中下三層。
Ka yi masa rufi, ka kuma ba da fili inci 18 tsakanin rufin a kowane gefen jirgin. Ka sa ƙofa a gefen jirgin. Ka yi shi hawa uku, ka yi ƙofa a gefe.
17 看我要使洪水在地上氾濫,消滅天下一切有生氣的血肉;凡地上所有的都要滅亡。
Ga shi zan aiko da ambaliya ruwa a duniya, in hallaka dukan mai rai da yake a ƙarƙashin sama, kowace halittar da take numfashi a cikinta. Dukan abin da yake a duniya zai hallaka.
18 但我要與你立約,你以及你的兒子、妻子和兒媳,要與你一同進入方舟。
Amma zan kafa alkawarina da kai, kai kuma za ka shiga jirgin, kai da’ya’yanka maza da matarka da matan’ya’yanka tare da kai.
19 你要由一切有血肉的生物中,各帶一對,即一公一母,進入方舟,與你一同生活;
Za ka shigar da biyu na dukan halittu masu rai, namiji da ta mace a cikin jirgin, domin su rayu tare da kai.
20 各種飛鳥、各種牲畜、地上所有的各種爬蟲,皆取一對同你進去,得以保存生命。
Biyu na kowane irin tsuntsu, kowace irin dabba da kuma kowace irin halitta mai rarrafe a ƙasa, za su zo wurinka domin a bar su da rai.
21 此外,你還帶上各種吃用的食物,貯存起來,作你和他們的食物。」
Za ka ɗauki kowane irin abinci wanda za a ci, ka adana don yă zama abincinka da nasu.”
22 諾厄全照辦了;天主怎樣吩咐了他,他就怎樣做了。
Nuhu ya yi kome kamar yadda Allah ya umarce shi.

< 創世記 6 >

The World is Destroyed by Water
The World is Destroyed by Water