< 創世記 49 >
1 雅各伯叫了他的兒子們來說:「你們聚在一起,我要將你們日後所遇到的事告訴你們。
Sai Yaƙub ya kira’ya’yansa maza ya ce, “Ku tattaru don in faɗa muku abin da zai faru gare ku, a kwanaki masu zuwa.
2 雅各伯的兒子! 你們集合靜聽,靜聽你們父親以色列的話:
“Ku tattaru, ku saurara,’ya’yan Yaƙub maza; ku saurari mahaifinku, Isra’ila.
3 勒烏本,你是我的長子,我的力量,我壯年的首生;你過於暴燥,過於激烈,
“Ruben, kai ne ɗan farina, ƙarfina, alamar farko ta ƙarfina, mafi matsayi, kuma mafi iko.
4 沸騰有如滾水。你不能佔據首位,因為你侵犯了你父親的床第,上去玷污了我的臥榻。
Mai tumbatsa kamar ruwa, amma ba za ka ƙara zama mai daraja ba, gama ka hau gadon mahaifinka ka hau kujerata, ka kuma ƙazantar da shi.
5 西默盎和肋未實是一對兄弟;他們的刀劍是殘暴的武器。
“Simeyon da Lawi’yan’uwa ne, takubansu makamai ne na tā da hankali.
6 我的心靈決不加入他們的陰謀,我的心神決不參與他們的聚會;因為他們在盛怒下屠殺了人,任意割斷了牛的腿筋。
Ba zan shiga shawararsu ba, ba zan shiga taronsu ba, gama sun kashe maza cikin fushinsu cikin ganin dama suka kashe bijimai.
7 他們的忿怒這樣激烈,他們的狂暴這樣凶狠,實可詛咒! 我要使他們分散在雅各伯內,使他們散居在以色列中。
La’ananne ne fushinsu, mai tsanani ne ƙwarai, hasalarsu kuwa, muguwa ce ƙwarai! Zan warwatsa su cikin Yaƙub in kuma daidaita su cikin Isra’ila.
8 猶大! 你將受你兄弟的讚揚;你的手必壓在你仇敵的頸上;你父親的兒子要向你俯首致敬。
“Yahuda,’yan’uwanka za su yabe ka; hannuwanka za su kasance a wuyan abokan gābanka,’ya’yan mahaifinka maza za su rusuna maka.
9 猶大是隻幼獅;我兒,你獵取食物後上來,屈身伏臥,有如雄獅,又如母獅,誰敢驚動﹖
Kai ɗan zaki ne, ya Yahuda, ka dawo daga farauta, ɗana. Kamar zaki, yakan kwanta a miƙe, kamar zakanya, wa yake da ƙarfin halin tashe shi?
10 權杖不離猶大,柄杖不離他腳間,直到那應得權杖者來到,萬民都要歸順他。
Kursiyi ba zai tashi daga Yahuda ba, ba kuwa sandan mulki daga tsakani ƙafafunsa ba, sai ya zo ga wanda yake mai shi. Biyayyar al’umma kuwa tasa ce.
11 他將自己的驢繫在葡萄樹上,將自己的驢駒拴在優美的葡萄樹上;在酒中洗自己的衣服,在葡萄汁中洗自己的外氅。
Zai daure jakinsa a kuringa, aholakinsa a rassa mafi kyau; zai wanke tufafinsa cikin ruwan inabi rigunansa cikin inabi ja wur kamar jini.
Idanunsa za su duhunce fiye da ruwan inabi, haƙorarsa farare kamar madara.
13 則步隆將居於海濱,成為船隻停泊的口岸,與漆冬毗連。
“Zebulun zai zauna a bakin teku, yă zama tasar jiragen ruwa; iyakarsa za tă nausa zuwa Sidon.
“Issakar doki mai ƙarfi, kwance tsakanin buhunan sirdi.
15 他覺得安居美好,地方優雅;便屈肩負重,成為服役的奴隸。
Sa’ad da ya ga yadda wurin hutunsa yana da kyau da kuma daɗin da ƙasarsa take, zan tanƙware kafaɗarsa ga nauyi yă miƙa kai ga aikin dole.
“Dan zai tanada adalci wa mutanensa kamar ɗaya cikin kabilan Isra’ila.
17 丹必似路邊的長蟲,道旁的毒蛇,咬傷馬蹄,使騎士向後跌下。
Dan zai zama maciji a gefen hanya, kububuwa a bakin hanya, da take saran ɗiɗɗigen doki domin mahayinsa yă fāɗi da baya.
“Ina zuba ido ga cetonka, ya Ubangiji.
“Masu fashi za su fāɗa wa Gad, amma zai runtume su.
“Abincin Asher zai zama a wadace, zai yi tanadin abinci iri-iri da suka dace don sarki.
“Naftali sakakkiyar barewa ce da take haihuwar kyawawan’ya’ya.
22 若瑟是一株茂盛的果樹,一株泉旁茂盛的果樹;枝條蔓延牆頭。
“Yusuf kuringa ce mai ba da amfani. Kuringa mai ba da amfani kusa da rafi wadda rassanta na hawan bango.
Da ɗaci rai mahara suka fāɗa masa; suka harbe shi babu tausayi.
24 但他的弓仍舊有力,他的手臂依然靈活;這是因了雅各伯的大能者之手,因了以色列的牧者和磐石之名;
Amma bakansa yana nan daram hannuwansa masu ƙarfi ba sa jijjiguwa saboda hannun Maɗaukaki na Yaƙub, saboda Makiyayi, Dutsen Isra’ila,
25 這是因為你父親的天主扶助了你,全能者天主,以天上高處的祝福,以地下深淵蘊藏的祝福,以哺乳和生育的祝福,祝福了你。
saboda Allah na mahaifinka, wanda ya taimake ka, saboda Maɗaukaki, wanda yake albarkace ka da albarkar sama da take bisa albarkun zurfafa da suke ƙarƙashin ƙasa albarkun mama da kuma mahaifa.
26 你父親的祝福,遠超過古山岳的祝福,永遠丘陵的願望;願這些祝福都降在若瑟頭上,降在他兄弟中被選者的額上。
Albarkun mahaifi suna da girma fiye da albarkun daɗaɗɗun duwatsu fiye da yalwar madawwaman tuddai. Bari dukan waɗannan su zauna a kan Yusuf, a goshin ɗan sarki a cikin’yan’uwansa.
27 本雅明是隻掠奪的豺狼:早上吞食獵物,晚上分贓。」
“Benyamin kyarkeci ne mai kisa; da safe yakan cinye abin da ya farauto da yamma yakan raba ganima.”
28 以上是以色列十二支派,以及他們的父親對他們所說的話。他祝福了他們,以適合每人的祝福,祝福了他們。
Dukan waɗannan su ne kabilu goma sha biyu na Isra’ila, kuma abin da mahaifinsu ya faɗa musu ke nan sa’ad da ya albarkace su, yana ba kowane albarkar da ta dace da shi.
29 以後雅各伯又囑咐他們,對他們說:「我快要歸到我親族那裏去,你們應將我葬在赫特人厄斐龍田裏的山洞裏,與我的祖先在一起。
Sa’an nan ya ba su waɗannan umarnai ya ce, “Ina gab da a tara ni ga mutanena. Ku binne ni tare da kakannina a kogon da yake cikin filin Efron mutumin Hitti,
30 這山洞是在客納罕地,面對瑪默勒的瑪革培拉的田內;這塊田原是亞巴郎由赫特人厄斐龍買了來作為私有墳地,
kogon da yake cikin filin Makfela, kusa da Mamre a Kan’ana, wanda Ibrahim ya saya tare da filin, yă zama makabarta daga Efron mutumin Hitti.
31 在那裏葬了亞巴郎和他的妻子撒辣,在那裏葬了依撒格和他的妻子黎貝加;我也在那裏葬了肋阿。
A can aka binne Ibrahim da matarsa Saratu, a can aka binne Ishaku da matarsa Rebeka, a can kuma na binne Liyatu.
Filin tare da kogon da yake ciki, an saya daga Hittiyawa.”
33 雅各伯給他的兒子們立完遺囑以後,便將腳縮到床上,斷氣而死,歸到他親族那裏去了。
Sa’ad da Yaƙub ya gama ba da umarnan ga’ya’yansa maza, sai ya ɗaga ƙafafunsa zuwa gado, ya ja numfashinsa na ƙarshe, aka kuwa tara shi ga mutanensa.