< 創世記 48 >
1 這些事以後,有人告訴若瑟說:「你的父親病了。」若瑟遂帶了他的兩個兒子,默納協和厄弗辣因同去。
Bayan wani lokaci aka faɗa wa Yusuf, “Mahaifinka yana ciwo.” Sai ya ɗauki’ya’yansa maza biyu, Manasse da Efraim suka tafi tare da shi.
2 人告訴雅各伯說:「你兒子若瑟來看你。」以色列遂勉強由床上坐起。
Sa’ad da aka faɗa wa Yaƙub, “Ɗanka Yusuf ya zo gare ka,” sai Isra’ila ya ƙoƙarta ya tashi ya zauna a kan gado.
3 雅各伯對若瑟說:「全能者天主曾在客納罕地路次顯現給我,祝福了我,
Yaƙub ya ce wa Yusuf, “Allah Maɗaukaki ya bayyana gare ni a Luz a ƙasar Kan’ana, a can ya albarkace ni
4 對我說:看! 我要使你繁殖增多,成為一大民族;我要將這地方賜給你未來的後裔,作為永久的產業。
ya kuma ce mini, ‘Zan sa ka yi ta haihuwa ka kuma riɓaɓɓanya, za ka ƙaru a yawa. Zan mai da kai al’ummar mutane, zan kuma ba ka wannan ƙasa tă zama madawwamiyar mallaka ga zuriyarka a bayanka.’
5 我未到埃及見你以前,你在埃及國所生的兩個兒子,由今起應歸於我;厄弗辣因和默納協屬我全如勒烏本和西默盎一樣。
“To, yanzu,’ya’ya mazanka biyu da aka haifa maka a Masar kafin in zo a nan za su zama nawa; Efraim da Manasse za su zama nawa, kamar yadda Ruben da Simeyon suke nawa.
6 在他們以後所生的子女,盡歸於你;不過在分產業時,他們應歸他們兄弟的名下。
Duk waɗansu’ya’yan da aka haifa maka bayansu za su zama naka; a yankin da suka gāda za a lissafa a ƙarƙashin sunayen’yan’uwansu.
7 當我由帕丹回來時,在離厄弗辣大還有一段路程時,在路上你母親辣黑耳,就在我的悲痛中死在客納罕地,我就將她葬在去厄弗辣大,即白冷的路旁。」
Yayinda nake dawowa daga Faddan Aram, cikin baƙin cikina Rahila ta rasu a ƙasar Kan’ana yayinda muke kan hanya,’yar rata daga Efrata. Saboda haka na binne ta a can kusa da hanya zuwa Efrata” (wato, Betlehem).
Sa’ad da Isra’ila ya ga’ya’yan Yusuf maza, sai ya yi tambaya, “Su wane ne waɗannan?”
9 若瑟回答父親說:「是天主在此地賜給我的兒子。」以色列說:「帶他們到我跟前來,我要祝福他們。」
Yusuf ya ce wa mahaifinsa, “Su ne’ya’yan da Allah ya ba ni a nan.” Sa’an nan Isra’ila ya ce, “Kawo mini su saboda in albarkace su.”
10 以色列因年老眼目昏花,看不清楚;若瑟遂領他們到他跟前;他就口親他們,抱住他們。
Yanzu fa idanun Isra’ila sun fara rasa ƙarfi saboda tsufa, har ba ya iya gani sosai. Saboda haka Yusuf ya kawo’ya’yansa maza kusa da shi, sai mahaifinsa ya sumbace su ya rungume su.
11 以色列對若瑟說:「連見你的面我都沒有料到;現今,看,天主還使我見到了你的後裔。」
Isra’ila ya ce wa Yusuf, “Ban yi tsammani zan ga fuskarka kuma ba, yanzu kuwa Allah ya bar ni in ga’ya’yanka su ma.”
12 若瑟遂由他父親膝間將孩子拉出來,俯伏在地下拜。
Sa’an nan Yusuf ya ɗauke su daga gwiwoyin Isra’ila ya rusuna da fuskarsa har ƙasa.
13 然後若瑟又領他們兩個,右手領厄弗辣因到以色列左邊,左手領默納協到以色列右邊,到父親面前。
Yusuf ya ɗauke su biyu, Efraim a damansa zuwa hagun Isra’ila, Manasse kuma a hagunsa zuwa hannun daman Isra’ila, ya kuma kawo su kusa da shi.
14 以色列卻伸出右手,放在次子厄弗辣因的頭上,伸出左手放在長子默納協的頭上,故意交叉著自己的手。
Amma Isra’ila ya miƙa hannun damansa ya sa shi a kan Efraim, ko da yake shi ne ƙaramin, ta wurin harɗewa hannuwansa, ya sa hannun hagunsa a kan Manasse, ko da yake Manasse ne ɗan farinsa.
15 遂祝福若瑟說:「願我的祖先亞巴郎和依撒格一生與之往來的天主,自我出生直到今日牧育我的天主,
Sa’an nan ya albarkaci Yusuf ya ce, “Bari Allah a gaban wanda kakannina Ibrahim da Ishaku suka yi tafiya, Allahn da ya zama makiyayina dukan raina zuwa wannan rana,
16 救我脫離一切禍患的使者,祝福這兩個孩童! 願我的名及我祖先亞巴郎和依撒格的名,賴他們流傳! 願他們在地上生育繁昌! 」
Mala’ikan da ya cece ni daga dukan cuta bari yă albarkaci samarin nan. Bari a kira su da sunana da sunayen kakannina Ibrahim da Ishaku bari kuma su ƙaru ƙwarai a bisa duniya.”
17 若瑟見他父親將右手放在厄弗辣因頭上,認為不對,便拿起父親的右手,由厄弗辣因頭上,移到默納協頭上,
Sa’ad da Yusuf ya ga mahaifinsa yana sa hannun damansa a kan Efraim bai ji daɗi ba; saboda haka ya ɗauke hannun mahaifinsa ya cire shi daga kan Efraim zuwa kan Manasse.
18 對父親說:「阿爸! 錯了;這個原是長子,應將你的右手放在他頭上。」
Yusuf ya ce masa, “A’a, mahaifina, wannan shi ne ɗan farin; ka sa hannunka na dama a kansa.”
19 他的父親卻拒絕說:「我知道,我兒! 我知道,他也要成為一個民族,他也要昌盛;但他的弟弟卻比他更要昌盛,他的後裔要成為一大民族。」
Amma mahaifinsa ya ƙi ya ce, “Na sani, ɗana, na sani. Shi ma zai zama mutane, zai kuma zama mai girma. Duk da haka ɗan’uwansa zai zama mai girma fiye da shi, kuma zuriyarsa za tă zama ƙungiyar al’ummai.”
20 那一天他又這樣祝福他們說:「以色列將以你們祝福人說:願天主使你如厄弗辣因和默納協!」他又將厄弗辣因放在默納協前面。
Ya albarkace su a wannan rana ya ce, “A cikin sunanku Isra’ila zai sa wannan albarka ‘Bari Allah yă sa ku zama kamar Efraim da Manasse.’” Saboda haka ya sa Efraim gaban Manasse.
21 然後以色列對若瑟說:「看,我快要死;但天主必與你們同在,必領你們回到你們祖先的地方去。
Sa’an nan Isra’ila ya ce wa Yusuf, “Ina gab da mutuwa, amma Allah zai kasance tare da ku
22 現在我將由阿摩黎人手中,以我的刀劍弓矢奪得的那塊山地賜給你,使你比眾兄弟多得一分。」
Kuma gare ka, a matsayi wanda yake kan’yan’uwanka, na ba da gonar da na karɓe daga Amoriyawa da takobi da kuma bakana.”