< 創世記 39 >

1 若瑟被人帶到埃及,有個埃及人普提法爾,是法郎的內臣兼衛隊長,從帶若瑟來的依市瑪耳人手裏買了他。
To, aka kai Yusuf Masar, Fotifar wani mutumin Masar wanda yake ɗaya daga cikin hafsoshin Fir’auna, shugaban masu tsaro, ya saye shi daga mutanen Ishmayel waɗanda suka kai shi can.
2 上主與若瑟同在,他便事事順利,住在他埃及主人家裏。
Ubangiji kuwa yana tare da Yusuf, Yusuf kuwa yi nasara, ya zauna a gidan mutumin Masar maigidansa.
3 他主人見上主與若瑟同在,又見上主使他手中所做的事,無不順利;
Sa’ad da maigidansa ya ga cewa Ubangiji yana tare da Yusuf, kuma cewa Ubangiji ya ba shi nasara a kome da ya yi,
4 為此若瑟在他主人眼中得了寵,令他服事自己,託他管理自己的家務,將所有的一切,都交在他手中。
sai Yusuf ya sami tagomashi a idanunsa, ya kuma zama mai hidimarsa. Fotifar ya sa shi yă zama shugaba a gidansa, ya kuma danƙa masa kome da yake da shi.
5 自從主人託他管理家務和所有一切以來,上主為若瑟的原故,祝福了這埃及人的家庭,他家內和田間所有的一切,都蒙受了上主的祝福。
Daga lokacin da ya sa shi shugaban gidansa da kuma a kan dukan abin da yake da shi, sai Ubangiji ya albarkaci gidan mutumin Masar saboda Yusuf. Albarkar Ubangiji tana a kan kome da Fotifar yake da shi a gida da kuma a jeji.
6 普提法爾將自己所有的一切,都交在若瑟的手裏;只要有他在,除自己所吃的食物外,其餘一概不管。若瑟生來體態秀雅,容貌俊美。
Saboda haka sai ya bar kome a ƙarƙashin kulawar Yusuf, bai dame kansa a wani abu ba sai dai abincin da yake ci. To, fa, Yusuf ƙaƙƙarfa ne, kyakkyawa kuma,
7 這些事以後,有一回,主人的妻子向若瑟以目傳情,並且說:「你與我同睡罷! 」
bayan an ɗan jima sai matar maigidansa ta fara sha’awar Yusuf, sai ta ce, “Zo ka kwana da ni!”
8 他立即拒絕,對主人的妻子說:「你看,有我在,家中的事,我主人什麼都不管;凡他所有的一切,都交在我手中。
Amma ya ƙi. Ya ce mata, “Ga shi kome yana a ƙarƙashina, don haka ne ma maigidana bai dami kansa da wani abu a cikin gidan nan ba; kome da ya mallaka, ya danƙa ga kulawata.
9 在這一家內,他並不比我更有權勢,因為他沒有留下一樣不交給我;只有你除外,因為你是他的妻子。我怎能做這極惡的事,得罪天主呢﹖」
Babu wani da ya fi ni a wannan gida. Maigidana bai hana ni kome ba sai ke, saboda ke matarsa ce. Yaya fa, zan yi irin wannan mugun abu, in yi zunubi wa Allah?”
10 她雖然天天這樣對若瑟說,若瑟總不聽從與她同睡,與她結合。
Ko da yake ta yi ta yin wa Yusuf maganar kowace rana, amma ya ƙi yă kwana da ita, ko ma yă zauna da ita.
11 有這麼一天,若瑟走進屋內辦事,家人都沒有在屋裏,
Wata rana, ya shiga cikin gida don yă yi ayyukansa, ba wani daga cikin bayin gidan da yake ciki.
12 她便抓住若瑟的衣服說:「與我同睡罷! 」若瑟把自己的外衣,捨在她手中,就跑到外面去了。
Sai ta cafke shi a riga, ta ce, “Zo ka kwana da ni!” Amma ya bar rigarsa a hannunta, ya gudu ya fita daga gidan.
13 她一見若瑟把自己的外衣捨在她手中,跑到外面去了。
Sa’ad da ta ga ya bar rigarsa a hannunta ya gudu ya fita daga gidan,
14 就召喚她的家人來,對他們說:「你們看! 他給我們帶來的希伯來人竟敢調戲我啊! 他來到我這裏,要與我同睡,我就大聲呼喊。
sai ta kira bayin gidan ta ce musu, “Duba, an kawo mana wannan mutumin Ibraniyawa don yă ci mutuncinmu! Ya zo nan don yă kwana da ni, amma na yi ihu.
15 他一聽見我高聲呼喊,把他的衣服捨在我身邊,就跑到外面去了。」
Sa’ad da ya ji na yi ihu neman taimako, sai ya bar rigarsa kusa da ni, ya gudu ya fita daga gida.”
16 她便將若瑟的衣服留在身邊,等他的主人回家,
Ta ajiye rigar kusa da ita sai da maigidansa ya dawo gida.
17 她又用同樣的話給他講述說:「你給我們帶來的那個希伯來僕人,竟到這裏來調戲我。
Sa’an nan ta faɗa masa wannan labari, “Mutumin Ibraniyawan, bawan da ka kawo mana, ya zo wurina don yă ci mutuncina.
18 我一高聲呼喊,他就把他的衣服捨在我身邊,跑到外面去了。」
Amma da zarar na yi ihu neman taimako, sai ya bar rigarsa kusa da ni, ya gudu ya fita daga gida.”
19 主人一聽見他妻子對他所說:「你的僕人如此如此對待我的話,」便大發憤怒。
Sa’ad da maigidansa ya ji labarin da matarsa ta faɗa masa cewa, “Ga yadda bawanka ya yi da ni,” sai ya husata.
20 若瑟的主人遂捉住若瑟放在監裏,即囚禁君王囚犯人的地方。他雖在那裏坐監,
Maigidan Yusuf ya ɗauke shi ya sa a kurkuku, wurin da ake tsare’yan kurkukun sarki. Amma yayinda Yusuf yake can a cikin kurkuku,
21 上主仍與他同在,對他施恩,使他在獄長眼中得寵;
Ubangiji ya kasance tare da shi; ya nuna masa alheri, ya kuma sa ya sami tagomashi a idanun mai gadin kurkukun.
22 因此獄長將監中所有的囚犯都交在若瑟手中;凡獄中應辦的事,都由他辦理。
Saboda haka mai gadin ya sa Yusuf ya zama shugaban dukan waɗanda aka tsare a kurkukun, Yusuf ne kuma yake lura da dukan abin da ake yi a can.
23 凡交在若瑟手中的事,獄長一概不聞不問,因為上主與他同在,凡他所做的,上主無不使之順遂。
Mai gadin ba ya sa kansa game da kome da yake ƙarƙashin kulawar Yusuf, gama Ubangiji yana tare da Yusuf, ya kuma ba shi nasara a cikin dukan abin da ya yi.

< 創世記 39 >