< 創世記 38 >
1 那時猶大離開自己的兄弟,下到一個名叫希辣的阿杜藍人那裏住下了。
A wannan lokaci, Yahuda ya bar’yan’uwansa ya gangara don yă zauna da mutumin Adullam, mai suna Hira.
2 猶大在那裏看見了一個名叫叔亞的客納罕人的女兒,就娶了她,親近了她。
A can Yahuda ya sadu da’yar wani Bakan’ane, mai suna Shuwa. Ya aure ta, ya kuma kwana da ita;
ta yi ciki, ta kuma haifi ɗa, wanda aka kira Er.
Ta sāke yin ciki, ta haifi wani ɗa, ta kira shi Onan.
5 以後她又生了一個兒子,給他起名叫舍拉;生他的時候,猶大正在革齊布。
Ta kuma haifi wani ɗa har yanzu, aka kuwa ba shi suna Shela. A Kezib ne ta haife shi.
Sai Yahuda ya auro wa Er mata, ɗansa na fari, sunanta Tamar.
7 猶大的長子厄爾行了上主所厭惡的事,上主就叫他死了。
Amma Er, ɗan farin Yahuda mugu ne a fuskar Ubangiji, saboda haka Ubangiji ya kashe shi.
8 於是猶大對敖難說:「你去與你哥哥的妻子親近,與她盡你為弟弟的義務,給你哥哥立後。」
Sa’an nan Yahuda ya ce wa Onan, “Ka kwana da matar ɗan’uwanka ka cika wajibinka gare ta a matsayin ɗan’uwan miji, don ka samar wa ɗan’uwanka’ya’ya.”
9 敖難明知後裔不歸自己,所以當他與哥哥的妻子結合時,便將精液遺洩於地,免得給自己的哥哥立後。
Amma Onan ya san cewa’ya’yan ba za su zama nasa ba; saboda haka a duk sa’ad da ya kwana da matar ɗan’uwansa, sai yă zub da maniyyinsa a ƙasa don kada yă samar wa ɗan’uwansa’ya’ya.
Abin nan da ya yi mugunta ce a gaban Ubangiji, saboda haka Ubangiji ya kashe shi, shi ma.
11 猶大於是對兒子塔瑪爾說:「你回到你父親家中去守寡,直到我兒子舍拉長大成人。」因為他心裏想:「恐怕他也如同他哥哥一樣死去。」塔瑪爾就回去,住在自己父親的家裏。
Sai Yahuda ya ce wa surukarsa Tamar, “Ki yi zama kamar gwauruwa a gidan mahaifinki sai ɗana Shela ya yi girma.” Gama ya yi tunani, “Shi ma zai mutu, kamar’yan’uwansa.” Saboda haka Tamar ta je ta zauna a gidan mahaifinta.
12 過了幾年,猶大的妻子叔亞的女兒死了。喪期過後,猶大便同自己的朋友阿杜藍人希辣,上提默納黑去剪羊毛。
Bayan an daɗe sai matar Yahuda,’yar Shuwa ta rasu. Sa’ad da Yahuda ya gama makoki, sai ya haura zuwa Timna, zuwa wurin mutanen da suke askin tumakinsa, abokinsa Hira mutumin Adullam kuwa ya tafi tare da shi.
13 有人告訴塔瑪爾說:「你公公現正上提默納黑去剪羊毛。」
Sa’ad da aka faɗa wa Tamar cewa, “Surukinki yana kan hanyarsa zuwa Timna don askin tumakinsa,”
14 塔瑪爾遂脫去守寡的衣服,蒙上首帕,遮掩自己,坐在通往提默納黑大道去厄納殷的路口上;--原來她見舍拉已經長大,還沒有娶她為妻。--
sai ta tuɓe rigunan gwaurancinta ta rufe kanta da lulluɓi don ta ɓad da kamanninta, sa’an nan ta je ta zauna a ƙofar shigar Enayim, wadda take a hanyar zuwa Timna. Gama ta lura cewa ko da yake Shela yanzu ya yi girma, ba a ba da ita gare shi ta zama matarsa ba.
15 猶大一看見她,以為她是個妓女,因為她遮蓋了自己的臉。
Sa’ad da Yahuda ya gan ta, ya yi tsammani karuwa ce, gama ta lulluɓe fuskarta.
16 猶大便由路上轉到她面前,向她說:「來! 讓我與你親近! 」他並不知她就是自己的兒媳。她答說:「你給我什麼,好與我親近﹖」
Bai san cewa ita surukarsa ce ba, sai ya ratse zuwa wurinta a gefen hanya ya ce, “Zo mana, in kwana da ke.” Sai ta ce, “Me za ka ba ni in na kwana da kai?”
17 猶大答說:「由羊群中取一隻小公山羊送給你。」塔瑪爾說:「你未送來以前,你應給個抵押。」
Ya ce, “Zan aika miki da ɗan akuya daga garkena.” Sai ta ce, “Za ka ba ni wani abu jingina, kafin ka aika da shi?”
18 猶大問說:「我該給你什麼作抵押﹖」她答說:「你的印章,你的繫印帶和你的棍杖。」猶大便交給了她,與她親近了;她於是由他懷了孕。
Ya ce, “Wace jingina zan ba ki?” Sai ta amsa, “Hatiminka da ka rataye a wuya da kuma sandan da yake a hannunka.” Ya ba da su gare ta, ya kuma kwana da ita, sai ta yi ciki.
19 事後,她起來回家,除掉首帕,再穿上她守寡的衣服。
Bayan ta tafi, sai ta tuɓe lulluɓin, ta sāke sa tufafin gwaurancinta.
20 猶大託自己的朋友阿杜藍人送了一隻小公山羊去,好由那女人手中取回抵押;他卻找不到她,
Ana cikin haka sai Yahuda ya aika da ɗan akuya ta hannun abokinsa mutumin Adullam don yă karɓo masa jinginar daga wurin macen, amma bai same ta a can ba.
21 便問當地人說:「那在厄納殷路旁的廟妓在那裏﹖」人答說:「這裏從來沒有廟妓。」
Ya tambayi mutanen da suke zama a can ya ce, “Ina karuwar haikalin da take a bakin hanya a Enayim?” Sai suka ce, “Ba a taɓa kasance da karuwar haikali a nan ba.”
22 他回來對猶大說:「我找不著她,並且當地的人都說:這裏從來沒有廟妓。」
Saboda haka sai ya koma zuwa wurin Yahuda ya ce, “Ban same ta ba. Ban da haka ma, mutanen da suke zama a can, sun ce, ‘Ba a taɓa kasance da wata karuwar haikali a nan ba.’”
23 猶大遂說:「讓她留著罷! 免得我們被人嗤笑。我將小公山羊送了去,可是你沒有找著她。」
Sa’an nan Yahuda ya ce, “Bari tă riƙe kayan kiɗa garin nema mu zama abin dariya. Ni kam, na aika da tunkiyar amma ba a same ta ba.”
24 大約過了三個月,有人告訴猶大說:「你的兒媳塔瑪爾與人通姦,而且因通姦有了身孕。猶大說:「把她拉出來燒死! 」
Bayan misalin wata uku sai aka faɗa wa Yahuda cewa, “Tamar, surukarka ta yi laifin karuwanci, a sakamakon haka yanzu ta yi ciki.” Yahuda ya ce, “A fid da ita, a ƙone!”
25 當她被拉出來時,她派人到她公公那裏說:「這些東西是誰的,我就是由誰懷了孕。」並且說:「請你仔細看看這些東西:印章、印帶和棍杖是誰的﹖」
Yayinda ake fitar da ita, sai ta aika saƙo zuwa wurin surukinta, ta ce, “Mutumin da yake da waɗannan kayan ne ya yi mini ciki.” Ta kuma ƙara da cewa, “Duba ko za ka gane da hatimin nan, da abin ɗamaran nan, da kuma sandan nan, ko na wane ne?”
26 猶大仔細一看,就說:「她比我更有理,因為我尚沒有將她嫁給我的兒子舍拉。」他從此以後,再沒有認識她。
Yahuda ya gane su, sai ya ce, “Ai, ta fi ni gaskiya, da yake ban ba da ita ga ɗana Shela ba.” Bai kuwa ƙara kwana da ita ba.
Sa’ad da lokaci ya yi da za tă haihu, ashe, tagwaye’yan maza ne suke cikinta.
28 她正生產時,一個胎兒伸出一手來,收生婆就拿了一根朱紅線繫在他手上說:「這個是先出生的。」
Yayinda take haihuwa, ɗaya daga cikinsu ya fid da hannunsa; sai ungonzomar ta ɗauki jan zare ta ɗaura a hannun, ta ce, “Wannan ne ya fito da farko.”
29 但是他一收回手去,他的兄弟就出生了;收生婆說:「你為自己開了個怎樣的裂口! 」遂給他起名叫培勒茲。
Amma sa’ad da ya janye hannunsa, sai ɗan’uwansa ya fito, sai ta ce, “Wato, haka ne ka keta ka fito!” Sai aka ba shi suna Ferez.
30 以後,那手上繫有朱紅線的兄弟也出生了,遂給他起名叫則辣黑。
Sa’an nan ɗan’uwansa wanda yake da jan zare a hannunsa ya fito, aka kuma ba shi suna Zera.