< 創世記 11 >

1 當時全世界只有一種語言和一樣的話。
To, a lokacin, yaren mutanen duniya ɗaya ne, maganarsu kuma ɗaya ce.
2 當人們由東方遷移的時候,在史納爾地方找到了一塊平原,就在那裏住下了。
Yayinda mutane suke ta yin ƙaura zuwa gabas, sai suka sami fili a Shinar, suka zauna a can.
3 他們彼此說:「來,我們做磚,用火燒透。」他們遂拿磚當石,拿瀝青代灰泥。
Suka ce wa juna, “Ku zo, mu yi tubula, mu gasa su sosai.” Suka yi amfani da tubula a maimakon duwatsu, kwalta kuma a maimakon laka.
4 然後彼此說:「來,讓我們建造一城一塔,塔頂摩天,好給我們作記念,免得我們在全地面上分散了! 」
Sa’an nan suka ce, “Ku zo, mu gina wa kanmu birni da hasumiyar da za tă kai har sammai, domin mu yi wa kanmu suna, don kada mu warwatsu ko’ina a doron ƙasa.”
5 上主遂下來,要看看世人所造的城和塔。
Sai Ubangiji ya sauko don yă ga birni da kuma hasumiyar da mutanen suke gini.
6 上主說:「看,他們都是一個民族,都說一樣的語言。他們如今就開始做這事;以後他們所想做的,就沒有不成功的了。
Ubangiji ya ce, “Ga su, su jama’a ɗaya ce, su duka kuwa harshensu guda ne. Wannan kuwa masomi ne kawai na abin da za su iya yi, babu kuma abin da suka yi shirya yi da ba za su iya yi ba.
7 來,我們下去,混亂他們的語言,使他們彼此語言不通。」
Zo, mu sauka, mu rikitar da harshensu don kada su fahimci juna.”
8 於是上主將他們分散到全地面,他們遂停止建造那城。
Saboda haka Ubangiji ya watsar da su daga wurin zuwa ko’ina a doron ƙasa, suka kuwa daina gina birnin.
9 為此人稱那地為「巴貝耳,」因為上主在那裏混亂了全地的語言,且從那裏將他們分散到全地面。
Shi ya sa aka kira birnin Babel, domin a can ne Ubangiji ya rikitar da harshen dukan duniya. Daga can Ubangiji ya watsar da su ko’ina a doron ƙasa.
10 以下是閃的後裔:洪水後兩年,閃正一百歲,生了阿帕革沙得;
Wannan shi ne labarin Shem. Shekara biyu bayan ambaliya, sa’ad da Shem ya yi shekara 100, sai ya haifi Arfakshad.
11 生阿帕革沙得後,閃還活了五百年,也生了其他的兒女。
Bayan ya haifi Arfakshad, Shem ya yi shekara 500, ya haifi waɗansu’ya’ya maza da mata.
12 阿帕革沙得三十五歲時,生了舍拉;
Sa’ad da Arfakshad ya yi shekara 35, sai ya haifi Shela.
13 生舍拉後,阿帕革沙得還活了四百零三年,也生了其他的兒女。
Bayan ya haifi Shela kuwa, Arfakshad ya yi shekara 403, ya kuma haifi waɗansu’ya’ya maza da mata.
14 舍拉三十歲時,生了厄貝爾;
Sa’ad da Shela ya yi shekaru 30, sai ya haifi Eber.
15 生厄貝爾後,舍拉還活了四百零三年,也生了其他的兒女。
Bayan ya haifi Eber, Shela ya yi shekara 403, ya kuma haifi waɗansu’ya’ya maza da mata.
16 厄貝爾三十四歲時生了培肋格;
Sa’ad da Eber ya yi shekaru 34, sai ya haifi Feleg.
17 生培肋格後,厄貝爾還活了四百三十年,也生了其他的兒女。
Bayan ya haifi Feleg, Eber ya yi shekara 430, ya kuma haifi waɗansu’ya’ya maza da mata.
18 培肋格三十歲時,生了勒伍;
Sa’ad da Feleg ya yi shekaru 30, sai ya haifi Reyu.
19 生勒伍後,培肋格還活了二百零九年,也生了其他的兒女。
Bayan ya haifi Reyu, Feleg ya yi shekara 209, ya kuma haifi waɗansu’ya’ya maza da mata.
20 勒伍三十二歲時,生了色魯格;
Sa’ad da Reyu ya yi shekaru 32, sai ya haifi Serug.
21 生色魯格後,勒伍還活了二百零七年,也生了其他的兒女。
Bayan ya haifi Serug, Reyu ya yi shekara 207, ya kuma haifi waɗansu’ya’ya maza da mata.
22 色魯格三十歲時,生了納曷爾;
Sa’ad da Serug ya yi shekaru 30, sai ya haifi Nahor.
23 生納曷爾後,色魯格還活了二百年,也生了其他的兒女。
Bayan ya haifi Nahor, Serug ya yi shekara 200, ya kuma haifi waɗansu’ya’ya maza da mata.
24 納曷爾活到二十九歲時,生特辣黑;
Sa’ad da Nahor ya yi shekaru 29, sai ya haifi Tera.
25 生特辣黑後,納曷爾還活了一百一十九年,也生了其他的兒女。
Bayan ya haifi Tera, Nahor ya yi shekara 119, ya kuma haifi waɗansu’ya’ya maza da mata.
26 特辣黑七十歲時,生了亞巴郎、納曷爾和哈郎。
Bayan Tera ya yi shekaru 70, sai ya haifi Abram, Nahor da Haran.
27 以下是特辣黑的後裔:特辣黑生了亞巴郎、納曷爾和哈郎;哈郎生了羅特。
Wannan ita ce zuriyar Tera. Tera ya haifi Abram, Nahor da Haran. Haran kuma ya haifi Lot.
28 哈郎在他的出生地,加色丁人的烏爾,死在他父親特辣黑面前。
Yayinda mahaifinsa Tera yana da rai, Haran ya rasu a Ur ta Kaldiyawa, a ƙasar haihuwarsa.
29 亞巴郎和納曷爾都娶了妻子:亞巴郎的妻子名叫撒辣依;納曷爾的妻子名叫米耳加,她是哈郎的女兒;哈郎是米耳加和依色加的父親。
Abram da Nahor suka yi aure. Sunan matar Abram, Saira ne, sunan matar Nahor kuwa Milka; ita’yar Haran ce, mahaifin Milka da Iska.
30 撒辣依不生育,沒有子女。
Saira kuwa bakararriya ce, ba ta da yara.
31 特辣黑帶了自己的兒子亞巴郎和孫子,即哈郎的兒子羅特,並兒媳,即亞巴郎的妻子撒辣依,一同由加色丁的烏爾出發,往客納罕地去;他們到了哈蘭,就在那裏住下了。
Tera ya ɗauki ɗansa Abraham, jikansa Lot ɗan Haran, da surukarsa Saira, matar Abram, tare kuwa suka bar Ur ta Kaldiyawa, don su tafi Kan’ana. Amma sa’ad da suka zo Haran sai suka zauna a can.
32 特辣黑死於哈蘭,享壽二百零五歲。
Tera yi shekaru 205, ya kuma mutu a Haran.

< 創世記 11 >