< 加拉太書 4 >
1 再說:承繼人幾時還是孩童,雖然他是一切家業的主人,卻與奴隸沒有分別,
Abin da nake nufi shi ne, muddin magāji yana ɗan yaro ne tukuna, babu bambanci tsakaninsa da bawa, ko da yake shi ne da mallakar kome.
2 仍屬於監護人和代理人的權下,直到父親預定的期限。
Yana ƙarƙashin iyayen goyonsa da masu riƙon amana har yă zuwa cikar lokacin da mahaifinsa ya sa.
3 同樣,當我們以前還作孩童的時候,我們是隸屬今世的蒙學權下;
Haka yake, sa’ad da muke’yan yara, mun kasance cikin bauta a ƙarƙashin ƙa’idodin duniya.
4 但時期一滿,天主就派遣了自己的兒子來,生於女人,生於法律之下,
Amma da lokacin da aka tsara ya yi sosai, sai Allah ya aiki Ɗansa, haifaffe daga mace, haifaffe a ƙarƙashin Doka,
5 為把在法律之下的人贖出來,使我們獲得義子的地位。
domin yă fanshi waɗanda suke a ƙarƙashin doka, saboda mu sami cikakken matsayin zaman’ya’ya.
6 為證實你們確實的天主的子女,天主派遣了自己兒子的聖神,到我們內心喊說:「阿爸,父啊! 」
Da yake ku’ya’ya ne, sai Allah ya aiko da Ruhun Ɗansa a cikin zukatanmu, Ruhun da yake kira, “Abba, Uba.”
7 所以你已不再是奴隸,而是兒子了;如果是兒子,賴天主的恩寵,也成了承繼人。
Saboda haka kai ba bawa ba ne kuma, kai ɗa ne; da yake kuwa kai ɗa ne, Allah ya mai da kai magāji.
8 當你們還不認識天主的時候,服事了一些本來不是神的神;
Dā da ba ku san Allah ba, ku bayi ne ga waɗanda a ainihi ba alloli ba ne.
9 但如今你們認識了天主,更好說為天主所認識;那麼,你們怎麼又再回到那無能無用的蒙學裏去,情願再作他們的奴隸呢﹖
Amma yanzu da kuka san Allah, ko kuma a ce Allah ya san ku, yaya kuke sāke komawa ga ƙa’idodin duniya marasa ƙarfi, abin tausayi kuma? Kuna so ku sāke komawa ga bautarsu ne?
Kuna kiyaye ranaku da watanni da lokuta da shekaru na musamman!
Kai, kun ba ni tsoro, don ya zama kamar duk wahalar da na yi a kanku banza ne!
12 弟兄們! 我懇求你們要像我一樣,因為我曾一度也像你們一樣。你們一點也沒有虧負過我。
Ina roƙonku’yan’uwa, ku zama kamar ni, gama na zama kamar ku. Ba ku yi mini wani laifi ba.
13 你們知道:當我初次給你們宣講福音時,正當我身患重病,
Kun san rashin lafiyar da na yi, shi ne ya yi mini hanyar da na kawo muku bishara da farko.
14 雖然我的病勢為你們是個試探,你們卻沒有輕看我,也沒有厭棄我,反接待我有如一位天主的天使,有如基督耶穌。
Ko da yake ciwona gwaji ne gare ku, ba ku yi mini reni ko ƙyama ba. A maimakon haka, kuka karɓe ni sai ka ce mala’ikan Allah, kuma sai ka ce Kiristi Yesu kansa.
15 那麼,你們當日所慶幸的在那裡呢﹖我敢為你們作證:如若可能,你們那時也會把你們的眼睛挖出來給我。
Me ya faru da dukan farin cikinku? Na tabbata, a lokacin, da mai yiwuwa ne da kun ciccire idanunku kun ba ni.
16 那麼,只因我給你們說實話,就成了你們的仇人嗎﹖
Yanzu na zama abokin gābanku don na faɗa muku gaskiya ke nan?
17 那些人對你們表示關心,並不懷好好意; 他們只是願意使你們與我隔絕,好叫你們也關心他們。
Waɗancan mutane suna neman su rinjaye ku da ƙwazo, amma ba da kyakkyawar aniya ba. Abin da suke so shi ne su raba ku da mu, saboda ƙwazonku yă koma gare su.
18 受人關心固然是好的,但應懷好意,且該常常如此,並不單是我在你們中間的時候。
Yana da kyau ku kasance da irin wannan niyya idan da nufi mai kyau ne, ku kuma kasance a haka koyaushe ba sai ina tare da ku ba.
19 我的孩子們! 我願為你們再受產痛,直到基督在你們內形成為止。
Ya ku’ya’yana ƙaunatattu, ina sāke shan wahalar naƙudarku, har sai Kiristi ya kahu a cikinku.
20 恨不得我現今就在你們跟前,改變我的聲調,因為我對你們實在放心不下。
Da ma a ce ina tare da ku yanzu in canja muryata mana! Gama na damu ƙwarai saboda ku!
21 你們願意屬於法律的,請告訴我:你們沒有聽見法律說什麼嗎﹖
Ku gaya mini, ku da kuke so ku zauna a ƙarƙashin Doka, ba ku san abin da Doka ta ce ba ne?
22 法律曾記載說:亞巴郎有兩個兒子:一個生於婢女,一個生於自由的婦人。
Gama a rubuce yake cewa Ibrahim yana da’ya’ya biyu maza, ɗaya ta wurin mace’yar aikin gidansa, ɗaya kuma ta wurin ainihin matarsa.
23 那生於婢女的,是按常例而生的;但那生於自由婦人的,卻是因恩許而生的。
Ɗansa na wajen mace’yar aikin gidansa ya zo bisa ga ƙa’idar jiki ne; amma ɗansa na wajen ainihin matarsa ya zo a sakamakon alkawarin ne.
24 這都含有寓意:那兩個婦人是代表兩個盟約:一是出於西乃山,生子為奴,那即是哈加爾──
Za a iya ɗaukan waɗannan al’amura a matsayin misali, domin matan nan suna misalta alkawura biyu ne. Alkawari ɗaya daga Dutsen Sinai ne yana kuma haihuwar’ya’yan da za su zama bayi. Hagar ke nan.
25 西乃山是在阿剌伯──這哈加爾相當於現在的耶路撒冷,因為耶路撒冷與她的子女同為奴隸。
Hagar tana a matsayin Dutsen Sinai a Arabiya tana kuma kwatancin birnin Urushalima na yanzu, gama ita baiwa ce tare da’ya’yanta.
26 然而那屬於天上的耶路撒冷卻是自由的,她就是我們的母親:
Amma Urushalimar da take sama’yantacciya ce, ita ce kuma mahaifiyarmu.
27 誠如經上記載說:『不生育的石女,喜樂罷! 未經產痛的女人,歡呼高唱罷! 因為被棄者的子女比有夫者的子女還多。』
Gama a rubuce yake cewa, “Ki yi farin ciki, ya ke bakararriya, wadda ba ta haihuwa ki ɓarke da murna, ki kuma tā da murya, ke da ba kya naƙuda; domin da yawa ne’ya’yan macen da aka yashe, fiye da na mai miji.”
To, ku’yan’uwa, ku’ya’yan alkawari ne kamar Ishaku.
29 但是,先前那按常例而生的怎樣迫害了那按神恩而生的,如今還是這樣。
A wancan lokaci, wannan ɗa wanda aka haifa ta wurin ƙa’idar jiki ya tsananta wa wanda aka haifa ta ikon Ruhu. Haka ma yake har yanzu.
30 然而經上說了什麼﹖『你將婢女和她的兒子趕走,因為婢女的兒子不能與自由婦人的兒子,一同承受家業。』
Amma me Nassi ya ce? Nassi ya ce, “Kori macen nan’yar aikin gida da ɗanta don ɗan mace’yar aikin gida ba zai taɓa raba gādo tare da ɗa na ainihin matarka ba.”
31 所以,弟兄們,我們不是婢女的子女,而是自由婦人的子女。
Saboda haka,’yan’uwa, mu ba’ya’yan mace’yar aikin gida ba ne, amma na ainihin matan gidan ne.