< 以斯拉記 1 >
1 波斯王居魯士元年,為應驗上主藉耶肋米亞的口所說的話,上主感動波斯王居魯士的心,叫他出一道號令,並向全國頒發上諭說:
A shekara ta farko ta mulkin sarkin Farisa, wato, sarki Sairus, domin a cika maganar Ubangiji da aka yi ta bakin Irmiya, sai Ubangiji ya taɓa zuciyar Sairus sarkin Farisa ya yi shela a duk fāɗin ƙasarsa, ya kuma rubuta cewa,
2 「波斯王居魯士這樣說:上天的神「雅威」將地上萬國交給了我,囑咐我在猶大的耶路撒冷,為衪建築一座殿宇。
“Ga abin da Sairus sarkin Farisa yake shela, “‘Ubangiji Allah na sama ya ba ni iko in yi mulkin duniya duka, ya kuma zaɓe ni in gina masa haikali a Urushalima cikin Yahuda.
3 你們中間凡作衪子民的,願他的神與他同在,上赫特4的耶路撒冷,建築以色列的神「雅威」的──是在耶路撒冷的神。
Duk wanda yake nasa a cikinku bari Allahnsa yă kasance tare da shi, bari yă tafi Urushalima cikin Yahuda yă gina haikalin Ubangiji, Allah na Isra’ila, Allah wanda yake a Urushalima.
4 所有的遺民,無論僑居在地方,那地方的人都應捐獻金銀、貨財、牲畜,以及自願的獻儀,為那在耶路撒冷的神修建殿宇」。
Duk inda akwai mutumin Yahuda da ya rage, sai mutanen da suke zama kusa da shi, su taimake shi da azurfa, da zinariya, da kaya, da kuma dabbobi, tare da kyautai na yardar rai saboda Gidan Allah wanda yake a Urushalima.’”
5 於是,猶大和本雅明的族長、司祭、肋未人,以及那些受天主感動了心的人,就起身上去,要建築耶路撒冷的上主的殿宇;
Sai shugabannin zuriyar Yahuda da na Benyamin, da firistoci da Lawiyawa, duk wanda Allah ya taɓa zuciyarsa, suka shirya don su je su gina haikalin Ubangiji a Urushalima.
6 四鄰八舍都拿出a的金銀、貨財、牲畜和珠實來協助他們,另外還有各種自願的獻儀。
Dukan maƙwabtansu kuwa suka taimake su da gudummawa na kayan azurfa da na zinariya, da kaya, da dabbobi, da kuma kyautai masu daraja bisa bayarwar yardar rai da suka yi.
7 居魯士王也將上主殿內的器皿,即先前拿步高從耶路撒冷掠奪而放在他神殿裏的器皿,
Sai sarki Sairus ya fitar da kayan da suke na haikalin Ubangiji waɗanda Nebukadnezzar ya kwashe daga Urushalima ya sa a haikalin allahnsa.
8 波斯王居魯士司庫官米特達特,將那些東西拿出,點交給猶太人的首領舍士巴匝,
Sairus sarkin Farisa ya sa Mitredat ma’aji ya ƙirga su a gaban Sheshbazzar ɗan sarkin Yahuda.
Ga lissafin kayan. Manyan kwanonin zinariya guda 30 Manyan kwanonin azurfa guda 1,000 Wuƙaƙe guda 29
Waɗansu kwanonin zinariya guda 30 Waɗansu kwanonin azurfa guda 410 da waɗansu kayayyaki guda 1,000
11 一切金銀器皿,共五千四百件。舍市巴匝就帶著這一切與充軍的人,從巴比倫回了耶路撒冷。
Dukan kayayyakin zinariya da na azurfa sun kai 5,400. Sheshbazzar ya kawo kayayyakin nan duka tare da shi lokacin da kamammun suka hauro daga Babilon zuwa Urushalima.